Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya yi kira ga Gamayyar Kungiyar Hadin Kan Ci Gaban Najeriya, Coalition for Nageria Movement da su yi...
Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya yi kira ga Gamayyar Kungiyar Hadin Kan Ci Gaban Najeriya, Coalition for Nageria
Movement da su yi shirin fafata yakin kwace mulki daga hannun Buhari. Obasanjo ya ce yakin farko shi ne mallakar katin rajista yin zabe. Ya yi wannan bayani ne
a da wurin kaddamar da kungiyar reshen jihar Oyo. A wuri kaddamarwar a garin Ibadan, ya na
mai kara yin kira da cewa su sani fa nan gaba
za su fuskanci barazana, saboda matsayin da
suka dauka na jajircewa ceto Najeriya. Ya ce kowa zai yi tananin kamar ba abu ne
mai yiwuwa ba, amma da karfin Allah da addu’a da kuma jajircewa, hakar su za ta
cimma ruwa. Daga nan sai ya kara maimaita musu cewa su
dauki batun katin jefa kuri’a da gaske. Obasanjo ya kafa wannan kungiya ce bayan
ya rubuta wa Buhari budaddiyar wasika inda
ya nemi ya hakura haka nan, bai cancanci
sake tsayawa takarar zabe a 2018 ba. Obansanjo dai ya ce a matsayin sa bai kamata
ya ji tsoron gaya wa kowa gaskiya ba, kuma bai kamata wani yi wa Najeriya tukin-
ganganci ba shi kuma ya zuba masa ido ya na kallon sa.
COMMENTS