A ranar Litinin 22 ga watan Janairun 2018 ne rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi suka yi nasarar kama wasu kwararrun ‘yan fashi da makami wada...
A ranar Litinin 22 ga watan Janairun 2018 ne
rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi suka yi
nasarar kama wasu kwararrun ‘yan fashi da
makami wadanda suka addabi jama’an Jihar.
Haka nan, wadanda aka kaman an kamasu da
hanu dumu-dumi cikin laifukan daban-daban wadanda suka hada da kashe mutane, fashi da
sauransu. Daga cikin wadda suka kashe har da
matar aure mai dauke da juna biyu, da kuma
wani wadda suka kashe gami da yin awun gaba
da babur dinsa. Rundunar ‘yan sandan ta kawo wa manema
labaru wadanda aka kashe musu ‘yan uwan
domin jin bayani daga garesu, Abubakar
Abdullahi Bidolo da ke kusa da Kangere a cikin
garin Bauchi ya rasa matarsa da kuma yi masa
fashin kudi har naira dubu dari 600,000:00. Ya bayyana yadda lamarin ya auku “yadda
lamarin ya auku shi ne a ranar 24/10/2017 cikin
dare sai ga barayi sun shigo gidanmu suka yi ta
harbi kan mai uwa da wabi. Gabanin nan sun yi
wa yayuna dukan tsiya, suka nufo dakina da
harbi suna kokarin shiga, suna cikin wannan harbe-harben nasu ne sai na ji matata ta ce
Innalillahi… matata tana da juna biyu bai wuce
saura mako guda daya tak ta haihu ba, domin ba
mu ma yi tsammanin za ta kai wannan lokacin ba
ta haihuwa ba”. “Ganin yaddda jininta ya fantsama a cikin dakin
sai na kama kofar na bude sai su ka jawo ni suka
kama dukana, na tsallaka gawar matata” Ya ce, daga nan suka yi masa zindir gami da kaisa
shagonsa don kwashe kudin ciki “Bayan nan
suka kamani suka cire min kaya da ni wana suka
kaimu shagona suka kwashe min kudi. Akalla
kudin cikin shagon zai kai dubu dari shida ko ma
fiye domin kudin nawa canji ne sun kai gari ya yi zafi biyu”. A cewarsa. Ya kara da cewa, “Sun rufe fuskokinsu, amma da
na zo nan sai na gane daya daga cikinsu yana
zuwa shagona sayen kaya ma. Su bakwai ne
suka zo suka yi man wannan ta’adin”. A cewar
mijin wacce aka kashe. Shi kuma wadda aka kashe masa dan uwa bayan
da suka yi masa fashi ya yi bayani da cewa
“Adamu Dawai sunana, dan uwan ya je kawowar
kauye ya dawo, daman shi yana sanar aune-
aune ne, suka zo suka yi masa fashin dubu 30, da
suka raina kudin da suka amsa daga hanunsa kawai suka bude masa wuya, suka kashe shi har
lahira, a zatonsu ya boye kudin ya ba su kadan”.
A cewar dan uwan. Da suke tabbatar da kisan da suka yi da
bakunansu ‘yan fashin sun bayyana yadda aka yi
“Sunana Ibrahim Abdulkarim shekaru 25, ina da
mata biyu, ‘ya’yana uku. Kwana uku da suka
wuce aka kiramu a waya aka ce mana akwai
wani aikin fashi a Abuja, sannan kuma aka ce mana akwai aikin fashi a nan wajen Yuguda sai
muka shiga mota muka je na Yugudan. muna isa
sai muka je wani gida za mu yi fashi, Mutumin sai
ya fito mana da adda, to mun yi tsammanin
bindiga ne kawai sai muka bude masa wuta”. “Lokacin da ya fito da adda, da muka zaci bindiga
ne, ni ina rike da bindiga Oluma yana rike da
bindiga kawai sai muka sake ruwan wuta, muka
kashi shi, bayan mun karbi dubu 30 a wajen shi”. “bayan da muka gama wannan kisan sai muka je
wani gida kuma muka kwashe mashuna guda
biyu”. Ibrahim Abdulkarim ya bayyana cewar shi ya
jima’a yanawannan sana’ar ta fashi da makami
amma ba a jihar Bauchi ba “Ni har ga Allah ina
wannan sana’ar amma ba a jihar nan ba; ina yi ne
a jihar Nasarawa”. Salisu Muhammad shi kuma ya ce “Mun je mun yi
fashi muka kuma yi satan Babura da kudin
wadda ya mutun”. A cewarsa. Direbobi biyu daga cikinsu da aka kama sun
bayyana cewar kwarewarsu a iya mota ne ‘yan
fashin ke daukan hayarsu domin su je su yi
wannan fashi wa jama’a. Wadanda dai aka kama kan wadannan laifukan
su ne Ahmed Mohammed 52 shugaban ‘yan
fashin, Ibrahim Abdullahi 28 shi ma shugabansu
ne,. Shu’aibu Adamu 52 mai baiwa ‘yan fashin
bayanan sirri, Sani Ibrahim 47 kwararren mai
tsara yadda za a yi fashi. Sauran su ne Yakubu Musa 42 mai shirye-shiryen
fashin, Musa Isa 44 mai amsar ababen da aka yi
fashinsu, Zakariya’u Mohammed 24, sai kuma
Salisu Mohammed 25 da na karshensu Bala
Ahmadu 30 wadda ya kasance direban ‘yan
fashin. Ababen da rundunar ta kama daga hanunsu sun
hada da Bindiga One Ak 49 Rifle, mai lamba
10553, bindiga AK47 Rifle, harsasan AK47 biyu,
fistol daya, alburasai masu rai guda 64, kwanson
harsasai masu rai, mota kirar Toyota Carina mai
lamba No. AG 656 FGE. Sauran ababen su ne mota Bectra mai lamba JJN
869 SN, Babura biyu kirar Bajaj KB 351 NNG,
mashin Haujue wacce ba ta da lamba, mabudi na
musamman ‘Master Key’, wayoyin salula guda
bakwai, adduna, wasu budin na daban, da kuma
abun rufe idonuwa. Da yake karin haske kan wannan nasarar da
suka samun, Kakakin Rundunar ‘yan sandan
jihar Bauchi DSP Kamal Datti Abubakar ya ce
wadanan ‘yan fashin da suka kaman sun iya
gano cewar suna daga cikin ‘yan fashin da suka
addabi hanyoyin Abuja, Filato, Gombe, Bauchi, Nasarawa da dai sauransu. Ya ce, nasarar tasu ta biyo bayan kokarin da
sashinsu na dakile aniyar ‘yan fashi wato FSARS
da kuma sashinsu na kwararru AKU. “Daga cikin laifukan da wadannan suka yi akwai
fashin mashina, a Durum-Yuga inda suka illata
wasu matafiya a wannan wajen” Bayan nan kuma ya ce “13/2/2018 kuma suka yi
wa wani mutum fashin motarsa kirar Honda mai
suna Sadik Ahmed Iliya da ke zaune a Isa Yuguda
Kuest House Bauhci, sun yi kokarin harbansa da ji
masa raunuka daga bisani ya samu dauki daga
jami’an tsaro”. DSP Datti ya ce laifukan nasu sun hada da “sun
kuma kashe wani mai suna Munkaila Tanko
bayan sun yi masa fashi a kauyen Yuguda. Bayan
nan duk a wannan kauyen sun yi wa Maigyalla
Muhammad da Jafaru Abdullahi fashi”. “Bayan nan sun kuma yi wa wani mutum
Abubukar Abdullahi fashi naira dubu dari shida,
suka kuma kashe masa matarsa mai suna Furaira
Abdullahi ‘yar shekaru 25. Ba su tsaya haka ba, fa
suka kuma yi wa wani mutum mai suna
Abubakar Adamu fashin mashin dinsa wacce darajarta zai iya kaiwa 141,000 dukka a wannan
gidan da suka kashe matar auren”. DSP Datti ya ce wadanda suka kaman gaggan
‘yan fashi ne don haka za su gurfanar da su a
gaban kuliya nan ba da jimawa ba domin
fuskantar shari’a.
.
©hausaleadership
COMMENTS