Wani magidanci mai kimanin shekara 45 ya tsallake rijiya da baya, bayan ɗage hukuncin zaman kurkukun shekara biyar da wani alƙalin Afirka ta...
Wani magidanci mai kimanin shekara 45 ya
tsallake rijiya da baya, bayan ɗage hukuncin
zaman kurkukun shekara biyar da wani alƙalin
Afirka ta yamma ya yanke masa, sakamakon
kama shi da laifin yin jima’i da karyar
maƙwabcinsa. Asirin Fanroi Mochachi, wanda ke da ‘ya’ya shida
ya tonu lokacin da karyar maƙwancinsa ke ta
haushin da ba a saba jin tana yi ba, a cikin wani
lambu, wanda ya sa mai karyar da babanta suka
zo domin su duba ko me ke faru wa. Zuwansu ke
da wuya, sai suka kama Mochachi na lalata da karyarsu. Bayan sun kama shi, sai ya fara bayanin cewa,
kafin ya zo wannan guri ya gamu da wasu
karnukan guda biyu, inda idonsa ya rufe ya fara
rungumar karen, wanda ya kubce masa, sai
kuma ya dawo kan karyar wadda ya yi jima’i da
ita. Alƙalin Majistiren Syta Prinsloo, ya bayyana abin
da magidancin ya yi da cewa dabbanci ne da
kuma jahilci. “Babban abin baƙin ciki shi ne, a matsayinsa na
magidanci wanda ya kamata a yi koyi da shi,
amma sai gashi ya jefa kansa cikin wannan
mummunan hali, wanda zai jawo wa ‘ya’yansa
gori”. “A matsayinsa na maigida in yana da buƙata
kamata ta yi ya kusanci iyalinsa, yanzu me zai ce
da iyalin nasa?” Mochachi ya tsallake rijiya da baya, yayin da aka
ɗage hukuncin da aka yanke masa na tsawon
shekara biyar a gidan kurkuku bayan ya amsa
laifinsa a gaban alƙali. Ɗage hukuncin ya kawo taƙaddamar da ta sa ake
ganinsa a matsayin rashin kare haƙƙin dabbobi
da mata da kuma yara ƙanana. Ma fi yawan ƙungiyoyi sun nuna damuwarsu, kan
ɗage hukuncin ganin yadda Mochachi ke ci gaba
da hulɗarsa a cikin gari. Saboda haka sai suka yi kira da bbabr murya kan
a hukunta duk wanda aka samu da irin wannan
laifi na yin lalata da dabbobi ko kananan yara,
saboda ba su da karfi.
.
©hausaleadership
COMMENTS