Ministan sifiri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa, zabar Muhammadu Buhari ya ci gaba da zama shugaban kasa a shekara ta 2019, shi ne kadai za...
Ministan sifiri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa,
zabar Muhammadu Buhari ya ci gaba da zama
shugaban kasa a shekara ta 2019, shi ne kadai
zai magance matsalar ci gaba da cin hanci da
rashawa a Nijeriya, saboda haka, ya zama wajibi
ga dukkan ‘yan Nijeriya da su zabi Muhammadu Buhari karo na biyu, don ba shi damar ci gaba da
yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan. Ministan ya bayyana haka ne a ofishinsa lokacin
da ‘yan jarida suka kai masa ziyara. Saboda haka,
sai ya kara jaddada cewa, yaki da cin hanci da
gwamnatin Buhari ke yi na bukatar ‘yan Nijeriya
su ci gaba da tallafa masa wajen ganin an samu
nasara. Ya ce matukar ‘yan Nijeriya suka yi kuskuren
zabar jam’iyyar PDP, su tabbatar da cewa, kamar
sun ba kura ajiyar nama ne, domin kuwa, sun
shafe shekara hudu suna cikin kishi. Saboda
haka da zarar sun sake samun dama sai su ci
gaba da watanda da dukiyar jama’ar kasa, fife ma da yadda suka yi a baya. Ministan ya kara da cewa,“Shekara hudu da suka
wuce jam’iyyar adawa ta PDP na cikin yunwa, ba
yunwar mulki ba, yunwar kudi, domin da za ka
ba su zabi tsakanin kudi da mulki, za su zabi kudi
ne, su bar mulki, saboda suna tsananin bukatar
kudi a halin yanzu,” kamar yadda ya ce. Ha kuma ya ce, ka da ‘yan Nijeriya su dauki sake
zabar Buhari a matsayin abu mai sauki, domin
akwai, wadanda ke zargin gwamnatinsa da laifin
gazawa, wadanda kuma in ma akwai gazawar su
ne suka haifar da wannan gazawar. Saboda
haka sai an jajirce matuka, wajen ganin Buhari ya ci gaba, domin sake ba shi damar da zai ci gaba
da dora kasar nan a kan kyakkyawar hanya.
.
©hausaleadership
COMMENTS