Wasu ‘yan bindiga da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari wata makarantar mata na kwana da ke garin Dapchi a jihar Yobe. R...
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin mayakan
kungiyar Boko Haram ne sun kai hari wata
makarantar mata na kwana da ke garin Dapchi a
jihar Yobe. Rahotan ya bayyana cewa, maharan sun afkawa
garin ne a cikin motocin akori kura yayin da su
ka isa makarantar inda suka yi ta harbe-harbe
kuma tare da tayar da abun fashewa a garin. Rahoton ya kara da cewa, daliban da malaman
makarantar sun yi nasarar tsere wa ne daga
hannun maharan bayan da hayaniyar ta basu
alamar cewa wani abu na faruwa.
©hausaleadership
COMMENTS