Blog Archive

Powered by Blogger.

Wata mata ta nemi Mijinta Ya Sake Ta Saboda yanda yake Fifita ta A Kan Mahaifiyarsa

Wata mace mai suna Baha mai kimanin shekara 29, ‘yar kasar Saudiyya ta maka mijinta a kotu inda ta bukaci ya sake ta, saboda yana fifita son...



Wata mace mai suna Baha mai kimanin shekara
29, ‘yar kasar Saudiyya ta maka mijinta a kotu
inda ta bukaci ya sake ta, saboda yana fifita sonta
fiye da mahaifiyarsa. Mijin ya yi matukar mamakin yadda matar ta sa ta
kai shi kotun, saboda a cewarsa yana biya mata
dukkan bukatunta. Ita kanta da ta kai shi kotun, ta tabbatar da cewa
yana biya mata dukkan bukatun da ta nema a
wajensa, sai dai inda gizo ke yin sakar shi ne,
yana nuna ya fi sonta fiye da mahaifiyarsa, ita
kuma ta ce sam ba za ta sabu ba, wai bindiga a
ruwa, in a kan haka ne sai dai kowa ya kama gabansa, don haka ta garzaya kotu. Matar ta ce “Ba zan taba gaskata namijin da zai yi
wa matarsa dukkan abin da take bukata ba,
amma ya ki kulawa da bukatar mahaifiyarsa ba,”
Kamar yadda ta bayyanawa alkali. Mijin wanda yake cike da rudani, ya bayyana wa
kotun cewa, yana son matarsa, ya bi duk
hanyoyin da zai bi domin ya yi bikonta, amma ta
ki yarda da hakan. Matar ta ce mijin nata yana kashe mata kudi sosai
ta hanyar saya mata dukkan abin da take bukata.
yakan dauke ta su tafi wasu kasashe domin
yawon shakatawa, ya kuma kashe mata kudi a
tafiye-tafiyen da suke yi, amma duk da haka ta ce,
ba za ta iya ci gaba da rayuwa da shi ba. “Ba zan iya zama da mutumin da ba ya
kyautatawa mahaifiyarsa ba. Saboda ni ma yana
iya juya min baya a kowane lokaci,” kamar yadda
ta ce. Mijin cike da mamaki ya tambayi matar cewa,
“Ban bar iyalina saboda ke ba?” Ta ce, “Ka bari, daman wannan shi ne dalilin da ya
sa nake so ka sake ni.” Matar ta ce dukkan abin da mijin ya fada a kotun
gaskiya ne, amma ita ta yanke shawar rabuwa da
shi ne kawai, saboda ya watsar da ‘yan uwansa
ya rungume ta, cikin wadanda ya yi watsi da su
din kuma har da mahaifiyarsa. Ta ce ba za ta jira har sai lokacin da ita ma zai yi
watsi da ita kamar yadda ya yi watsi da
mahaifiyarsa ta sa ba. Matar ta mayar da sadakin da mijin nata ya ba ta,
sabaoda haka sai alkalin ya tabbatar mata da
sakin. Wata majiya daga kotun ta yabawa matar bisa
tsayuwar dakan da ta yi a kan neman hakkinta
na neman mijinta ya sake ta saboda nuna fifikon
da yake yi tsakaninta da mahaifiyarsa. Majiyarmu ta nuna cewa, wasu mazajen na da
tunanin cewa, nuna soyayya ga matansu shi ne
zai sa su jawo hankalinsu wajen soyayya. “Wannan ba daidai ba ne. Dole ne mutum ya kula
da ‘yan uwansa, musamman mahaifiyarsa, wadda
take ta fi kowa a rayuwarsa” . Ya ce matarsa tana jin haushi, saboda yana fifitata
fiye da mahaifiyarsa, wadda itace da haifeshi kuma ta Reneshi har zuwa lokacin daya girma.
.
©hausaleadership

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Wata mata ta nemi Mijinta Ya Sake Ta Saboda yanda yake Fifita ta A Kan Mahaifiyarsa
Wata mata ta nemi Mijinta Ya Sake Ta Saboda yanda yake Fifita ta A Kan Mahaifiyarsa
http://fm.nextwapblog.com/files/6475/arab.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/02/wata-mata-ta-nemi-mijinta-ya-sake-ta.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/02/wata-mata-ta-nemi-mijinta-ya-sake-ta.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy