Blog Archive

Powered by Blogger.

Wane Irin Hanyoyi Za Kibi domin Namiji Ya Aure Ki?

Maza su kan zama a rude yayin da su ka tashi neman mace tagari har su kan shiga shakka kan wace ce macen da ya dace su aura. Amsar da su ke ...



Maza su kan zama a rude yayin da su ka tashi
neman mace tagari har su kan shiga shakka kan
wace ce macen da ya dace su aura. Amsar da su
ke samu ita ce, su yi duk inda za su yi su lalubi
mai kamun kai, domin daga ita ne a ke samun
mace tagari. Ita kuwa mai kamun kai siffofinta a bayyane ya ke, inda namiji in ka kura ido ka
tsanannta nema, to za a dace. Mace tagari ita macen da Bahaushe ke kira mai
kamun kai wadda ta siffantu da kakkyawar
dabi’a da halaye da kamala, wacce kuma kallo
daya za a iya gane tarbiyyarta da kokarin da
iyayenta su ka yi wajen ba ta tarbiyya. Mace ta
kwarai ita ce wadda kowanne namiji mai hankali zai yi fatan a ce ta na gidansa ta zame masa
sanyin idaniya ta zama al-mar’atissaliha da
Annabi Muhammad (SAW) ya ce ta fi duniya da
duk abin da ya ke cikinta. Mace ingantacciya ita ce
dai matar da kowanne namiji zai so ya sami zuriya
da ita. Mata da dama da za ka tattauna da su shi ne
babbar matsalarsu mijin aure, abin haushi da ke
damun su ga masoyan nan kamar jamfa a Jos,
amma auren ya gagara. Mata na ta wahala addu’a
da ’yan dabaru kana su na ta fama, amma abu ya
ki yi wuwa. Tashin hankalin ba ga matan ba zawarawan ba. Mace wadda ba ta da makusa ta
kowanne bangare kyau ko asali ko ilimi, amma
aure ya gagara a na ta laluben dalili an kasa gano
gaskiya abu guda ke zagayawa a kwakwalwarsu
shi ne maza mayaudara ne, amma fa duk
yaudararsu su na neman mace tagari ne, don sa wa a daki. Kamun kai Idan ka tashi neman matar da za ka aura ka dage
ka nemi mai kamun kai. Ya na cikin matakin farko
da mace ya kamata ta fara nunawa a gun duk
wanda ta ke so su kulla mu’amala da ta ke fatan
dorewarta zuwa aure. Hanyoyi da dama za ka
lura da shi in ka na son gane mace mai kamun kai, kada ka jira a ba ka labari; kai da kanka za ka
sa ido ka lura. Mata a yau a tunaninsu yadda su
ke ganin maza na haba-haba da mata ba tare da
nuna wani zabe ba, to su sani iyakarta waje ne. Sutura Sutura ita ce abin da a ke sanyawa a jiki don kare
tsiraici. A sutura a na gane kamalar mutum. Abu
na farko da kan ja hankalin namiji ga mace har ya
gane ajin da zai ajiye tashi ne irin suturar da ta
saka jikinta. Mata a yau su na tunanin bayyana tsiraicinsu shi
ne hanyar da za su iya janyo hankalin namiji gare
su har ya gane kyan wani bangare na jikinsu da
zai kai su ga aure. Wannan kuskure ne, domin
namjin da wannan zai dauki hankalinsa har ya yi
tunanin ku yi sabo, to tabbas sai dai soyayya, wanda a karshe danasani ne zai biyo bayan
haduwar. Ya na da kyau mace ta yarda da cewa
mijinta duk inda ya ke zai tarar da ita, sannan ba
wani dace da za a samu a sabon Allah. Surutu Surutu barkatai alamu ne na rashin kamun kai.
Macen kwarai ba a san ta da daga harshe ba ko
da a cikin ’yan’uwanta mata ne bare kuma maza.
Wata matar ta na tunanin idan ta shiga dandazon
maza ta daga muryarta da zakewa shi ne zai
janyo hankalin namiji kansu. Mace mai surutu rau-rau a kan titi ko cikin maza ba ta cikin irin
matar da ka ke nema ka aura. Mace mai kamewa da karancin magana ko da
kuwa a wajen saurayin ne abar yabo ce da
soyuwa ko da batun auren ne irin su a ke nema a
adana a gida. Kunya Bahaushe ya ce kunya marin da. Ka tabbatar
matar da za ka aura mai kunya ce, don kuwa duk
macen tagari an san ta da kunya da yakana da
kara. Mace ba ta isa mace abin sha’awa idan har
ta zamanto fitsararriya. Akwai hanyoyi da dama
da mace za ta nuna kunya kamar haka: Zance barkatai Yin surutu rau-rau kafin namijin ya yi guda kin yi
goma. In har aka zo batun aure maza ba irin
wannan suke nema ba in har kina neman mijin
aure to anan kin fadi jarrabawar. Ciye-ciye Mata a yau sun zubar da kyakkawar al’adar nan
ta kame kai wajen ciye-ciye a kan hanya ko
gaban samari. Mace mai ciye-ciye da rashin kimtsi
ko ga sa’anninta mata ba ta farin jini bare maza.
Duk matar da ka ganta tana ciye ciye kan turba
bar ta kawai ba ta shirya samun mijin aure ba. Roko Roko shi ma wata hanya ce ta nuna rashin kunya
da mata kan dauka hanya wayewa. Duk matar da
ta fiye roko tana kashe wa kanta wata daraja ne
ga mai sonta kuma in har mace ta fiye roko to fa
tana nunawa wannan da zai aure ta irin zaman da
za su yi. Hali na farko da za su sa a ran su in har suka kai ki gidansu ba za ki iya hakuri da samu
da rashi ba sannan duk randa babu ba za ki iya
rufa wa zamantakewar asiri ba. Roko ga mace
babbar hanya ce ta zubar da mutunci. Don haka
in budurwarka ta ishe ka da ba-ni-ba-ni na ba
gaira ba dalili to fita a guje ba ba matar aure ce ba. Kallo A kallo kadai a na iya bayyana halin mace,
tarbiyyarta da kunyarta da dacewa ka kai ta gida
ko kuma ba za ka kai ta ba. Ka lura da yadda
wadda za ka aura ta ke kafe ka da ido, ba
rusanawa, to ka bi a sannu. Rashin jan aji Mace ta kirki da jan aji da kamewa a ka santa. Ba
wai ta zama mai girman kai ba, amma ka nemi
wanda ta san darajar kanta. Idan har mace za ta
zama arha kowanne namiji ya kira ta ba
tantancewa ta je, kowa yake bukatar jin hira ko
yawo ita za a zo nema a tafi da an ce ana sonta to fa kasuwa ta bude ba sauran edcuse to fa mai irin
wannan halin ta kade ba ta sa dan-ba ba a wajen
neman mijin aure ba. Kai ma me neman matar
kwarai kada ka leka. Zafin soyayya A nan ba sai na yi dogon sharhi ba ku maza ku
ne ku ke lallabawa ku nemi yarinya da bukata ta
biya ba kwa kuma komawa mu a bangarenmu
mata sai mu ce rashin alkawari ne ya janyo haka
amma ku kuka san dalili don haka ni a nan ba ni
da ta cewa. A wannan gabar ya ragewa matan tunda sai me karfin rabo saurayi ke neman mace
a karshe ya aure ta. Na san zai yi wuya ko na ba
ka shawarar idan haka ta afku duk da ba a fata
nace ka aure ta ko na fad aba ji z aka yi ba. Abin nufi dai da wannan rubutu shi ne kwarya
tagari na rataya. Maza irin wannan suke nema su
kai gida. Kalubale ne ga iyaye su sa ido kan
tarbiyyar ‘ya’yansu sannan su ke nusar da su
abubuwan da ya dace na tarbiyya. Allah ya sa mu dace, amin.
.
©hausaleadership

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Wane Irin Hanyoyi Za Kibi domin Namiji Ya Aure Ki?
Wane Irin Hanyoyi Za Kibi domin Namiji Ya Aure Ki?
http://fm.nextwapblog.com/files/6475/aure.png
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/02/wane-irin-hanyoyi-za-kibi-domin-namiji.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/02/wane-irin-hanyoyi-za-kibi-domin-namiji.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy