Shahararen jarumin nan na fina-finan Hausa, Tijanni Asase ya hadu da iftila’in gobara inda wuta ta cinye gidansa kurmus. Bincikenmu ya nunar...
Shahararen jarumin nan na fina-finan Hausa,
Tijanni Asase ya hadu da iftila’in gobara inda
wuta ta cinye gidansa kurmus. Bincikenmu ya nunar da cewa babu abin da
maigidan da iyalansa suka tsira da shi, komai ya
kone kurmus! amma Allah ya sa iyalinsa sun tsira
da ransu, wato matarsa da ya’yansa uku. Shafin Taurarin Nishadi ya tuntubi Jarumin don jin
abin da ya haddasa gobarar, ga kuma abin da ya
fada: “Ranar Asabar da misalin karfe 2 na dare, matata
tana kwance suna barci sai aka kawo wuta, sai
gun canjin wuta ya kama sai dakinta ya fara
kamawa da wuta, daga nan dakin yara shi ma ya
kama da wuta duk suna barci. Sai da dakina ya
kama ta saman silin zafi ya farka da matar gidan, sai ta rude ta tashi yara ta bude kofar waje ta
dakina suna budewa talabijin ta fashe suka firgita
suka yi waje ba kaya ajikinsu sai a makota aka
basu”. Jarumi Asase, ya cigaba da cewa a lokacin da
gobarar ta tashi ba ya nan, ya kuma bayyana
wurin da yake, inda ya ce “ni kuma muna gun
aiki sai da safe aka gaya min na zo. Amma har na
zo wutar ba ta gama ci ba, babu abin da muka mora
a gidan da ni da matata da yarana guda uku,
Fatima Zainab da Hafsatu”, a ta bakinsa. Domin nuna alhini da kuma jaje ga jarumin, a
ranar Talatar da ta gabata ‘yan fim mata a
karkashin Kungiyar Jarumai Mata na Arewa
(Northern Nigeria Female Actresses) sun ziyarci
gidan da al’amarin ya faru inda suka jajanta masa
da kan wanan abin alhini da ya sameshi. Cikin wadanda suka sami halarta har da
mataimakiyar shugabar kungiyar, Halisa
Muhammad, da sakatariyar tsare-tsare, Mansurah
Isah, da sakatariyar kudi, Sadiya Gyale. Sauran
sun hada da sakatariyar kungiyar Sakna Gadaz,
da sauran wasu da ba sa garin Kano, irin su shugabar kungiyar, Wasila Ismail da
mataimakiyarta ta biyu, wato Rahma Hassan duk
sun yi masu jaje da addu’ar Allah yak are nagaba,
ya mayar da fiye da abin da aka rasa. Har ila yau, mambobi da dama na kungiyar da
dama, su ma ba a bar su a baya ba inda suka taru
suka yi masa addu’a a gidan da ya konen inda
suka roki Allah ya mayar masa da dubunsu. Jarumin ya nuna jindadinsa tare da godiya ga
‘ya’yan kungiyar jaruman ta hanyar fadin, “Na
gode sosai, Allah ya bar zumunci”. Jarumai da dama maza da mata abokan sana’arsa
na cigaba da yi masa jaje ta fuskoki daban-
daban, wasu a gida, wasu ta waya, wasu kuma ta
hanyoyin sadarwa.
.
©hausaleadership
COMMENTS