An kama wani mai suna Segun Durojaiye dan shekara 52 malami a makarantar Ijagba da ke Sotubo a garin Sagamu da laifin yi wa ‘yarsa ‘yar shek...
An kama wani mai suna Segun Durojaiye dan
shekara 52 malami a makarantar Ijagba da ke
Sotubo a garin Sagamu da laifin yi wa ‘yarsa ‘yar
shekara 16 fyade har na tsawon shekara 4, an
kama mutumoin ne da dan uwansa Emmanuel
Durojaiye, yarinyar na zaune da mahaifin nata ne a layin Baba-Benja da ke unguwar Oreyo a
Igbogbo Ikorodu ta jihar Legas. Majiyar ta shaida mana cewa Segun ya karbi
kulawa da yarinyar ne bayan rasuwar mahifiyar
ta in da shi da kishiyar uwar suka ci gaba da
renon yarinyar har zuwa shekarar 2014 lokacin
da kishiyar uwar ta rasu daga nan ne ta koma
Abuja wajen wani danuwansu. Bayan ‘yan watanni ne Segun ya umurci da ta dawo gida in
da ya ci gaba da jima’i da ita yana mai yi mata
barazanar ka da ta gaya wa kowa. Bayani ya nuna cewa, ana cikin wannan hali ne
wata rana ta ziyarci kanin mahaifin ta Emmanuel
dan shekara 42 in da shi ma ya yi mata fyade
daga nan ne su biyu suka ci gaba da jima’i da ita
ba kakkauta wa. Wakilinmu ya gano cewa, wani lokaci a watan
Disamba 2107 yarinyar ta yi karfin halin bayyana
wa wata ‘yaruwarsu in da ita kuma ta yi wa
kakarsu bayanin halin da ake ciki. “Kakar ta yi kokarin boye maganan amma da
wasu makabta suka ji labarin sai suka nemi lauya
ya rubuta takardar koke a madadin yarinyar
zuwa kwamishinan ‘yansanda in da a ka kama
mahaifin nata da kawun ta, “Anu kuma su muka
tura “Case” din sashin bincike na farin kaya da ke Yaba” “Tuni suka amsa laifisu in da suka tabbatar da yin
jima’i da yarinyar sau uku-uku, daya daga cikin
‘ya’yan Segun ya bayar da karin shaidar cewa,
lallai ta gaya masa mahaifinsu na jima’i da ita ya
kuma gargade shi akan lallai ya bari” Majiyar namu ya shaida mana cewar yarinyar ta
gaya wa ‘yan sanda cewa sau biyu mahaifin nata
na yi mata ciki, kawun ta kuma sau daya ya yi
mata, su kan kai ta wani wuri ne a zubar da cikin.
“Ta ce mahaifinta ya fara jima’i da ita ne tun tana
shekara 13 a duniya kuma sau uku ana zubar mata da ciki” Jami’in hurda da jama’a na hukumar ‘yansanda
jihar Legas Chike Oti ya tabbatar da faruwar
lamarin, “Mun samu labarin abin da ya faru ne ta
hanyar takardar koke da wani lauya ya rubuta
mana, tuni kwaminshinan ‘yansanda Edgal
Imohimi ya bayar da umurnin sashin SCIID ya ci gaba da bincike” ‘Kwamishinan ‘yansanda a shiye ya ke domin
hada hannu da hukumomin gwamnati wajen
tabbatar da hakkin yara da kare su daga miyagu
masu bata rayuwarsu, zamu tabbatar da an
hukunta duk wanda muka kama da kaifin yin
lalata da yara kanana” in ji shi. An gurfanar da masu lafin a gaban kotun
majastare da ke Yaba in aka tuhume su da laifi 8
da suka hada da fyade da zubar da ciki. Bayan karanta musu laifuffukansu a karkashi
dokokin jihar Legas sashi na 145(2) sun musanta
aikata laifin, daga nan ne alkali Oluwatoyin Oghre
ya bayar da belinsu a bisa sharadin tsayawar
mutum biyu a kan kudi Naira Miliyan 1, dole masu
tsaya musu su kai matakin albashi 15 a aikin gwamnati ko kuma mai rike da sarautar gargajiya
tare da shaidar cikakken biyan haraji, an dai daga
shari’a zuwa ranar 12 ga watan Maris 2018.
.
©hausaleadership
COMMENTS