Blog Archive

Powered by Blogger.

Bom Ya Kashe Mutune 5 Tare da Jikkata mutum 44 A Maiduguri

A kalla mutane biyar 5 ne a ka tabbatar da mutuwarsu ciki kuwa har da wasu mata biyu ‘yan kunar bakin wake, inda kuma mutane sama da arba’in...



A kalla mutane biyar 5 ne a ka tabbatar da
mutuwarsu ciki kuwa har da wasu mata biyu ‘yan
kunar bakin wake, inda kuma mutane sama da
arba’in da hudu 44 suka gamu da munanan
raunuka, biyo bayan fashewar wasu jerin bama-
bamai wadda ‘yan kunar bakin waken suka tayar a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Dalori kusa da
unguwar Dalori da ke cikin Maiduguri babban
jihar Borno a Larabar nan da ta gabata. Kamar yadda shugaban hukumar bayar da agajin
gaggawa reshen jihar Borno wato (SEMA ),
Ahmed Satomi ya bayyana cewar biyu daga cikin
wadanda suka mutun ‘yan kunar bakin wake ne
wadanda sune kuma suka tayar da boma-
boman. inda suka kai hari sassanin ‘yan gudun hijiran a ranar Larabar nan da ta gabata a
sansanin IDP’s da ke Dalori da ke unguwar Dalori. Satomi ya ce, sun garzaya da wadanda suka
gamu da munanan raunukan zuwa asibitoci
daban-daban da suke fadin jihar, inda kuma ya
ce yanzu sun yi kokarin shawo kan wasu lamarin
a wannan sansanin biyo bayan fashewar bam din
tun a cikin daren da lamarin ya auku, inda ya ce yanzu haka sun daidaito da komai bisa daidai. Har-ila-yau, da yake tabbatar da wannan
mummunar hari, Daraktan Shiyya na hukumar
bayar da agajin gaggauwa ta kasa a shiyyar
Arewa Maso Gabas Mr. Bashir Idris Garga ya ce
“Bom din farko da ya tashi a unguwar Dalori ya
tashi ne da misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Laraba, inda shi kuma bom na biyun wadda ya
tashi a sansanin ‘yan gudun hijiran Dalori ya tashi
da misali karfe 9:30 na dare duk a wannan
ranar”. Ya ci gaba da bayyana yadda lamarin ya auku,
inda ya ce matar mai dauke da bom na farko ta yi
kokarin shiga cikin sansanin ‘yan gudun hijiran
don tayar da wannan bom din amma Allah bai
bata ikon hakan ba, inda bom dinta ya fashe da
ita a kofar shiga wannan sansanin inda ta kashe kanta da kanta ita kadan “A yayin da kuma mai
dauke da bom na biyu ta samu shiga cikin
sansanin yadda ta kashe mutane uku 3 da ita
kanta, inda kuma aka samu mutane sama da 44
suka gamu da munanan raunuka a sakamakon
tashin wannan bom na biyun wacce ‘yar kunar bakin waken ta tayar”. In ji Shi. Daraktan sashin Arewa maso gabas a hukumar
bayar da agajin gaggawa ta kasan ya bayyana
cewar tuni aka hanzarta kai wadanda suka gamu
da munanan raunakan zuwa asibitoci daban-
daban a cikin Maiduguri domin nema musu
kulawar likitoci cikin gaggawa.
.
©hausaleadership

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Bom Ya Kashe Mutune 5 Tare da Jikkata mutum 44 A Maiduguri
Bom Ya Kashe Mutune 5 Tare da Jikkata mutum 44 A Maiduguri
http://fm.nextwapblog.com/files/6475/bomber.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/02/bom-ya-kashe-mutune-5-tare-da-jikkata.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/02/bom-ya-kashe-mutune-5-tare-da-jikkata.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy