Ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da martani ga wani limamin addinin Kirista bisa zargin da ya yi ma...
Ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaban
kasa Muhammadu Buhari ya mayar da martani ga
wani limamin addinin Kirista bisa zargin da ya yi
masa na cewa, yana ji yana gani ya kasa yin
komai a kan kashe-kashen da ake yi a Binuwai
da Adamawa da Taraba da jihar Zamfara, yana zaune a gida sai jin dadinsa yake yi. Kamar yadda bayani ya fito daga bakin mai bai
wa shugaban kasar shawara na musamman a
kan harkokin yada labarai, Mista Femi Adesina,
lokacin da yake karbar wata tawaga daga
babbar cocin Catholic Bishops Conference of
Nigeria, wadanda Archbishop Ignatius Kaigama ya jagoranta zuwa fadar shugaban kasa da ke
Billa, Abuja. Buhari ya ce saboda sanin matsalar da ke tattare
da wannan kashe-kashe ya sa ya mike tsaye
wajen ganin an kawo karshen lamarin ta hanyar
tura dakarun tsaro dukkan yankin da ake yin
wannanan kashe-kashe. Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai
da kashe-kashen da ake yi a sassan kasar nan,
tare kuma da daukar matakin da ya kamata
domin kawo karshen wannan kashe-kashe ta
hanyar tura jami’an tsaro wadannan yankuna. Saboda haka sai ya ce, “Idan aka ce na koma ofis
na zauna ina cikin air condition da gida mai kyau
ba tare da damuwa ba, kan wadannan kashe-
kashe, ba a yi mini adalci ba. “A koyaushe, a kuma duk inda nake ina tunani a
kan wannan matsala. da hanyoyin da za a bi
wajen kawo karshenta, domin na san yadda irin
wannan matsala take tun lokacin ina babba
hafasan soja da ke kula da rundunoni uku cikin
rundana hudun a Barikin sojoji da ke Legas da Ibadan da kuma Jos. Shugaban ya ci gaba da cewa tsarin da
gwamnatin tarayya ta fito da shi na samarwa
Fulani makiyaya muhallin kiwo da kaucewa
rikicin Fulani da manoma, ba yana nufin
mallakewa mutane filayensu ba ne. Ya ce, manufar gwamnati shi ne ta samarwa
Fulani gurin kiwo, yadda shanunsu za su samu
abinci. Shugaban ya nuna rashin jin dadinsa bisa yadda
aka juyar da wannan al’amari ake kokarin
murguda shi, yadda zai kawo wata sabuwar
rashin fahimta tsakanin manoma da Fulani Duk da haka, ya tabbatarwa da limamin cocin na
katolika cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba
kokarin ganin an samu zaman lafiya a wannan
kasa. Haka kuma shugaban ya gaya wa masu ziyarar
cewa ba zai gajiya ba wajen ci gaba da tabbatar
da an samu dawwamammen zaman lafiya a
wannan kasa ba.
.
©hausaleadership
COMMENTS