Matar babban likitan kungiyar Boko Haram Rabi Abu-Yasir, ta mika kanta ga jami’an sojoji na rundunar “Operation Lafiya Dole” a ci gaba da ka...
Matar babban likitan kungiyar Boko Haram Rabi
Abu-Yasir, ta mika kanta ga jami’an sojoji na
rundunar “Operation Lafiya Dole” a ci gaba da
kakkabe saura ‘yan ta’adda da rundunar ke yi.
Kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole,
Manjo Janar Rogers Nicholas, ya bayyana haka a lokacin da yake mika mata fiye da 82 da
rundunar ta ceto daga hannun ‘yanta’adda ga
hukumar bayar da agajin gaggawa (SEMA) a
Maiduguri. Rabi ta bayyana cewa, mijinta shi ne babban
likitan Abubakar Shekau, ta ce, an ceto ta ne
ranar Jumma’a yayin da sojoji suka fatattaki ‘yan
ta’addan a wani bangare na dajin Sambisa. Da take bayyana halin da ta shiga lokacin da take
hannunsu, ta ce, lallai an fifita ta a bisa sauran
mata saboda kasancewar ta matar Likitan
Shekau. “Miji na Likita ne yana duba mutane yana kuma
gudanar da “Operation” in an samu mai rashin
lafiyar da ta yi tsanani, abincin da nake ci da
sauran abubuwan amfanin da suke bani daban
yake da na sauran mata da kananan yaran da ke
sansanin ba”. “Mun sha wahala a hannun su, sun kuma
gargademu da cewa sojoji zasu kashe duk
wannan ya mika musu wuya” “Sun yi ta karfafa mana guiwar cewa, mu tsaya
tare da su kada mu mika wuya ga sojoji, amma ga
shi sojoji na kula da mu yadda ya kamata ba
kamar yadda suka gaya mana ba” Rabi ta kuma gode wa sojoji da suka ceto su ta
kuma bukaci wadanda suke cikin daji da su fito
su mika kansu ga rundunar sojoji. Da yake karin bayani, Manjo Janar Nicholas ya
bayyana cewa, Rabi na cikin fafaren hula 84 da
rudunarsu ta ceto, ya ce, 8 daga cikinsu na
karbar magani a asibitin sojojin Sama na
Maiduguri. Ya kuma ce, wadanda suka ceton sun
fuskanci tsananin cin mutunci a hannun ‘yan ta’addan. Ya ce, an ceto mutanen ne bayan da rundunarsa
ta yi kai hari wajen ajiye makamain kungiyar a
cikin dajin Sambisa in da suka samu daman kama
motocin yaki da albarusai tare da ceto daruruwar
fararen hula. Ya kara da cewa, rundunar zata
tsugunar da farfado da ‘yan ta’addan da aka kama kafin a shigar da su cikin alumma su ci
gaba da rayuwarsu, “Ina kira ga wadanda suke
cikin daji da su fito su mika kansu, ba muna
kashe mutane bane, mun zo mu taimaka muku”.
.
©hausaleadership
COMMENTS