A na kiransa ‘Garcinia kola’ amma a saukake an fi kiransa da Namijin Goro kuma tushensa da tsirransu sun fito ne daga Afirka ta tsakiya. Wan...
A na kiransa ‘Garcinia kola’ amma a saukake an fi
kiransa da Namijin Goro kuma tushensa da
tsirransu sun fito ne daga Afirka ta tsakiya.
Wanda hakan ke nuna irin mahimmancin da
nahiyar ta Afirka ke da shi a fannin tsirrai. Namijin
Goro yana samar mana da ɗimbin hanyoyin warkar da cututtuka na mamaki. Yana daga cikin
dangin tsirrai na Fulawa yana kuma fita da launin
ruwan ƙasa. AMFANIN GA HUHU: Yana magance Huhu da wasu
sassa na jikin mutum suna taimakawa wajen
gudanar manyan ayyuka a cikin jikin mutum.
yana taimaka mana wajen yin numfashi. Cin irin
sa yadda ya dace, yana taimakawa Huhu wajen
gudanar da aiki yadda ya kamata kuma ya bada kariya a cikin jikin mutum. Yana kuma taimakawa hanyoyin Jini haka yana
magance sanyi na zuciya. Saboda haka, ga
mutane masu zuƙar Taba Sigari, namijin goro na
iya zame musu magani. MAGANIN CUTAR CIZON SAURO: Irin Namijin Goro
ana taimakwa wajen warkar da cutar cizon Sauro.
Ba mamaki da masu magungunan gargajiya suka
bada shawara a riƙa yin amfani dashi. Ba a
bayyana wata illa da Namijin Goro keyi wa mutum
a jikin sa ba saboda yin amfani dashi. Amma a wasu lokutan, cin Namijin Goron yana janyo
wasu illoli a jiki. DAIDAITA BUGUN ZUCIYA YADDA YA KAMATA:
Wasu sassan na jikin mutum sukan nuna ƙyama
wajen cinsu ɗin wasu itatuwan, inda cinsu ke
janyowa jikinsu wani irin yanayi. A irin wannan
yanayin yana da kyau mutum ya tuntuɓi Likitansa
ya kuma daina yin amfani dashi. A yanzu mun riga mun san cewar Namijin Goron,
ba wai lallai ɗaci kawai yake dashi ba, yana kuma
da ɓangare na zaƙi wanda kuma yana taimakawa
wajen ƙara lafiyar jiki a gare mu.
.
©hausaleadership
COMMENTS