Blog Archive

Powered by Blogger.

Wani Kafinta Ya Yiwa Surukarsa Ciki A Nasarawa

Wani kafinta dan shekara 45 mai suna John Ulaha, a yanzu haka yana cikin matukar damuwa da bakin cikin da ya jefa kansa sakamakon abin kunya...



Wani kafinta dan shekara 45 mai suna John
Ulaha, a yanzu haka yana cikin matukar damuwa
da bakin cikin da ya jefa kansa sakamakon abin
kunyar da ya tabka. John mazauni a karamar hukumar Awe dake
jihar Nasarawa matarsa Bictoria, tana da shagon a
Lafia cikin Jihar Nasawa,inda take sayar da kayan
masarufi, shi kuma John yana gudanar da
sana’arsa ta kafinta. Don su kara samarwa da kansu kudin shiga sun
kuma tsunduma yin aikin noma a Awe, inda suke
daukar hayar laburori suna yi masu aiki a gona. Sakamakon kaddamar da dokar hana samar da
burtali ga Fulani makiya dake jihar Binewe da
gwamnatin ta yi, sama da kashi tamani da biyar
na ayarin Fulani makiya da suka yi hijira daga
jihar ta Binewi, inda suka yarda zango a Awe,
ganin kuma makiyayan sun fara aukuwa gonakin manoman dake Awe, hakan ya kara haifar zama
barazana ga manoman dake karamar hukumar,
inda suka bazama suna ta kokarin su kawar da
amfanin gonakan su. Hakan ya sanya Bictoria ta Bukaci mahaifiyar ta
Ashetu Igbasue, ‘yar shekara 42 data dawo Awe
don ta taikawa Jonh yin girbin Doya da Dawar da
ya shuka tunda ita Bictoria tana ta fama da kula
da shagonta a Lafia. Surukar ta komo Awe a cikin watan Satum bar
2017,inda take taimakawa surukin nata John
don su kawar da amfanin gonar cikin gaggawa. Abin mamaki bayan wata uku Bictoria ta dimauce
data gano mahifiyar ta tana dauke da juna biyun
da John ya yiwa mahifiyar ta. A cewar Bictoria “na kasance a cikin jin bakin
labari kuma ban san yadda zan ji da wannan abin
takaicin ba.” Ta ce, “na auri mijina shekaru tara da suka wuce
munada ‘ya karama wani lokacin mahifiyata ta
kanzo ta kwan biyu a gunmu ganin cewar
mijinta ya rasu, amma a wannan lokacin nida
kaina nace na roketa tazo donta taimaka mana a
gona.” Bictoria taci gaba da cewa, tun wancan lokacin
tana tare da da mijina a Awe tana taimaka masa a
gona, koda yake sukanzo Lafia akai-akai su
kwashi kaya su koma domin sun sha alawshin
sai sun kawar da amfanin gonar don kada
makiyaya su aukawa gonar. Ta kara da cewa, “akawai wani lokaci da mijina
yazo Lafia don karbar wasu kayan girki, inda na
tambaye shi da fatan dai sunaci suna koshi, sai ya
kada baki ya ce mini harga zuciyar sa cewar
girkin mahaifiya ta yafi nawa dadi, ban sa wani
zargi a zuciya ta ba akan amsar da bayani ba, domin na yarda da miji na kuma koma dai
wacece ake magana akai mahaifiya tace ba
kishiya ba.” Ta ce, “wani zuwan karshe da mahaifiya ta ta yi
garin Lafia daga kauyen mijina a cikin razana ta
gaya min cewar bataga aladarta ba a wata na
farko dana biyu ba, inda tace wannan ya nuna
tana dauke da juna biyu ta kuma ce mijina shine
sanadi. Bictoria tace, mahaifiyar ta tace sai a zubar da
cikin domin abin kunya ne a gareta ace tanada
ciki a shekarun ta bayan mijinta ya baya raye. A cewar Bictoria,“ni na gayyato ta tazo ta taimaka
mini don kawar da amfanin gona don kada
makiyaya su auka wa gonar, amma ban san ashe
mijina yanata soyewa da mahaifiya ta ba kuma
mahaifiya ta amsa cewar mijina shine silar cikin.” Da take kara nuna takaicinta akan halin dan
akuyancin mijin nata Bictoria tace, “yafi min sauki
da ace ya yi min kishiya wadda zata kasance tana
gida koda yaushe ko kuma ya samu wata
budurwar sa ta dinga kula dashi in ni bana nan
da yafi da ya tsunduma cikin soyayya da mahaifiya ta, wannan abin kunya ne babba kuma
abin bakin ciki. Ita kuwa surukar ta bayyana cewar, abin ya fara
kamar da wasa a gonar, inda hakan ya kaiga
suka fara kusantar juna a wata rana da dare
bayan sun dawo gida daga gona. A cewar Surukar“ na amince na bashi kaina
bayan da ya bukaci yana son tarawa dani tunda
dai kawai yana son ya biya bukatarsa ce, amma a
hankali sai abin ya zama jiki a kullum sai mun
sadu, ban taba tunanin cewar zan iya daukar ciki
ba a shekaru na.” Ta ci gaba da cewa,” na gayawa diyata gaskiya
don mu samu mafita amma saboda fishin data yi
ta bari maganar ta bazu, nayi danasin abinda na
aikata kuma duk niyyata in samu a zubar da
cikin.” Surukar tace, “da farko diyar tawa ta ta amince da
a samu wani a zubar da cikin saboda bazan iya
barin cikin ba duk wannan abinda ya auku aikin
zuciya ne kuma nayi danasi matuka akan hakan
na nemi garafa daga gunta.” Shi kuwa John a nashi bangaren shima ya amince
da abin kunyar da ya tabka, inda ya ce lallai ya
sabi ubangiji da kuma cin amanar matarsa har da
zuciyar sa ta raudare shi ya kwana da surukar sa
har kuma ta samu ciki.” John ya ce, dole ne a zubda cikin zai kuma yi iya
kokarin sa ya lallashi matar sa data amince a
zubda cikin, nayi matukar bakincikin akan
abinda ya auku.” John ya ce,”wannan ba halina bane kuma abin
kunya ne a gare ni dana jifa kaina a ciki da matata
da dukkan alummar kauyen mu da kuma
wadanda suka sanni.” A karshe ya ce,“ tunda matata ta fitar da maganar
kowa ya sani, bana iya samun wani sukuni har
abinci ma bana iya ci na roki matata ta yafe mini
domin wannan aikin dana tabka, aikin shedan
ne.
.
©hausaleadership

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Wani Kafinta Ya Yiwa Surukarsa Ciki A Nasarawa
Wani Kafinta Ya Yiwa Surukarsa Ciki A Nasarawa
http://fm.nextwapblog.com/files/6475/kafinta.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/02/wani-kafinta-ya-yiwa-surukarsa-ciki.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/02/wani-kafinta-ya-yiwa-surukarsa-ciki.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy