Kamar de yanda kuka sani yawanci masu amfani da wayar android sun Riga da sunsan android tana da yawan tara folders haka kawai zakaga folder...
Kamar de yanda kuka sani yawanci masu amfani da wayar android sun Riga da sunsan android tana da yawan tara folders haka kawai zakaga folders suna taruwa a wayarka ta android, kuma yawancin folders zakaga babu komi acikinsu, wani lokacinma mutum ya dinga bi yana gogesu daya bayan daya musamman idan bayason yawan ganinsu,
.
Sabo da haka daga yanzu insha Allah kun dena takura kanku wajen bi kuna goggoge empty folder, domin ga wani app wanda ake kira da Empty Folder Cleaner shi wannan app din zai taimaka muku wajen goge dukkan wata empty folder, sabi da haka yanzu ku danna nan domin saukar da wannan app din Download Empty folder Cleaner.apk
.
Bayan kunyi download na wannan app din sai kuyi install dinsa sannan ku budeshi ku duba daga gefe zakuga inda aka Rubuta clear saika danna nan atake zakaga ya fara goge dukkan wata empty folder, saika jira har saiya gama da zarar ya kammala zakaga ya nunama adadin empty folders din daya goge, shikkenan saika fita kaje file manager ka ka duba, insha Allah zakaga babu sauran wata empty folder.
.
Allah ya bada sa,a
COMMENTS