A jiya ne mutum 29 wadanda suka hada da dalibai 25 da malaman su uku da direba sun rasa rayukan su a kan hanyar su ta zuwa nazarin ilimin ta...
A jiya ne mutum 29 wadanda suka hada da dalibai 25 da malaman su uku da direba sun rasa
rayukan su a kan hanyar su ta zuwa nazarin
ilimin tarihi a gidan dan Hausa da ke Kano. Dalibai da Malaman da suka rasu sun kasance a
karkashin kungiyar Hausa Fasaha dake
makarantar Jeka ka dawo ta GDSS Misau da ke
Jihar Bauchi. Hatsarin ya auku a kusa da garin Gaya dake Jihar
Kano da misalin karfe Goma na Safiyar jiya inda
motar kirar ‘Toyota Hommer’ wacce aka
cunkushe ta da daliban ta yi taho mu gama da
mota kirar tirela mai tayu goma sha biyu, wacce
ke kan hanyar Kano zuwa Maiduguri, inda su kuma ke kan hanyar su daga Misau zuwa Azare
zuwa Kano don gudanar da wannan nazarin
tarihi. LEADERSHIP A Yau ta gano cewa daliban sun
kasance ‘yan ajin karamar sakandare daga daya
zuwa uku wadanda suka kudiri yin wannan
tafiya tare da malamansu sun gamu da hatsarin
ne a dalilin aikin hanya da ake yi a wannan waje
aka kuma hade ana tafiya kan hannu guda. Lamarin dai ya yi muni sosai har sai da matafiya
da mutanen yankin suka yi ta taimakawa kafin
aka jawo gawarwakin dalibai 22 da malamai uku
da direba yayin da kuma dalibai uku aka kai su
asibiti kafin daga baya suma rai ya yi halin sa. Ya zuwa wannan lokaci lamurra sun tsaya cik a
fannin aikin gwamnati a Jihar ta Bauchi kamar
yadda babban mai ba gwamnan Jihar Bauchi
shawara kan harkar ilmi Kwamared Sabo
Mohammed ya shaida wa wakilin mu. Inda ya
mika sakon gaisuwar ta’aziyya a madadin kwamishinan ilimi na Jihar Bauchi da daukacin
masu ruwa da tsaki kan ilmi da kuma gaisuwar
ta’aziyya ta gwamna Mohammed Abdullahi
Abubkar na Jihar Bauchi game da wannan rashi
na daliban inda ya bayyana cewa wannan
babbar hasarace ga Jihar da ba za a taba mancewa da ita ba kan harkar da ta shafi ilmi. Sabo Mohammed ya kara mika ta’aziyyar
gwamnati da jama’ar Jihar Bauchi ga Mai martaba
Sarkin Misau Alhaji Ahmed Sulaiman game da
wannan babban rashi na yara masu kasancewa
manyan gobe a Jihar Bauchi. Ya ce gwmnati ta kadu sosai lokacin da ta samu
wannan labari, kuma nan take jami’an ma’aikatar
ilmi da sauran jami’an gwamnati suka dunguma
zuwa garin na Misau domin yin jana’izar yaran
wacce ta gudana a yammacin wannan talatar a
garin na Misau. Malam Ya’u Mohammed da Malam Mohammed
Kaka Misau Malamai ne a wannan makaranta, sun
bayyanawa LEADERSHIP A Yau alhininsu kan
wannan rashi da suka ce ya haifar da gibi a
fannin ilmi na makarantar ta jeka ka dawo da ke
garin Misau, inda suka yi fatar Allah ya ba da hakuri ga iyayen yaran da kuma abokan karatun
su da malaman wannan makaranta da sauran
‘yan uwa da dukkan jama’ar wannan kasa, inda
suka ce wannan babban rashi ne da ba za su iya
mance wa da shi ba a tarihin karatun wannan
makaranta. Jagoran ayyukan musamman na hukumar kiyaye
hadurra ta kasa FRSC da ke Bauchi Kwamanda
Paul E. Guar a lokacin da wakilin mu ya ziyarce shi
a ofishinsa da ke Bauchi, ya tabbatar da aukuwar
wannan hatsari, inda ya ce daliban sun tashi daga
garin Misau zuwa Kano sun gamu da ajalin su a kusa da garin Gaya sakamakon taho mu gama da
babbar mota, inda ya bayyana cewa yin sakaci da
dokar tuki ya temaka wajen haifar da hatsarin.
Don haka ya roki jama’a su kasance masu lura da
rayukan jama’ar da suke dauka da kuma nasu
shi ne zai taimaka a samu raguwar hadurra a kasar nan. Haka kuma Paul Guar ya bayyana takaici game da
yadda aka cunkusa wadannan mutane har
kusan 30 a motar da ke daukar mutane 18,
lamarin da ya bayyana a matsayin abu maras
kyau da kuma saba dokar tuki da lodi, saboda
yin hakan na samar da karuwar yawan mutanen da za su iya galabaita ko rasa rayukan su a duk
lokacin da wani tsautsayi ya abko kan matafiya,
musamman ganin cewa wannan hatsari ya auku
ne a wurin da ake gyaran hanya. Daga karshe ya
ce ofishin hukumar da ke Jihohin Kano da Jigawa
sune za su bayar da cikakken bayani game da yadda aikin su ya gudana a wajen wannan
hatsari.
©hausaleadership
COMMENTS