A Faransa akalla bakin-haure biyar suka jikkata a birnin Calais na kasar, sakamakon arrangamar da aka yi tsakanin bakin hauren kasashen Afgh...
A Faransa akalla bakin-haure biyar suka jikkata a
birnin Calais na kasar, sakamakon arrangamar da
aka yi tsakanin bakin hauren kasashen
Afghanistan da kuma Eritria. Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya
ruwaito cewa yanzu haka, an garzaya da wasu
bakin haure 4 ‘yan kasar Eritria asibiti, domin cire
musu harsasan da aka harbe su da su. Fadan wanda bakin hauren suka shafe kimanin
sa’o’i 2 suna gwabzawa, ya fara ne a lokacin da
bakin hauren ke bin layin karbar abinci. Kimanin bakin-haure ‘yan kasar Eritria 100 da
kuma na Afghanistan 30 rikicin ya rutsa da su.
.
©hausaleadership
COMMENTS