NASIRU UMAR GWALLAGA, shi ne shugaban Matasan jam’yyar APC reshen Jihar Bauchi, wanda ake yi masa inkiya da ‘Nasiru A-Kasa-A-Tsare Na Buhari...
NASIRU UMAR GWALLAGA, shi ne shugaban Matasan jam’yyar APC reshen Jihar Bauchi, wanda
ake yi masa inkiya da ‘Nasiru A-Kasa-A-Tsare Na
Buhari’. A hirasa da LEADERSHIP A Yau Juma’a ya
bayyana cewar Atiku da Obasanjo su ne silar
lalacewar Nijeriya domin sun tafiyar da mulkin
kasar nan ta gurbatattun hanya. Ya ce, batun da Obasanjo da ‘yan tawagarsa suke kokarin yi
wajen kawo wa Buhari cikas a zaben 2019
hakan ba zai kawo wa Buhari cikas din ba.
Wakilinmu, KHALID IDRIS DOYA ne ya tattauna da shi kamar haka: Ya ka ke kallon shawarar da tsohon shugaban kasa Cif Obansajo ya bayar ta ganin cewa Buhari bai maimaita shugabanci a karo na biyu ba? Eh, Ni gaskiya wannan lamarin bai zo min a
matsayin sabon abu ko wani lamarin na ban
mamaki ba; domin shi tsohon shugaban Nijeriya
Cif Olusegun Obasanjo yadda ya zama a kasar
nan tun alfi 1999 bayan da suka dale karagar
mulki suka tabarbara Nijeriya, wadda kowa ya san yadda suka maida Nijeriya. bayan sun gama,
suka sake dasa yaransu, su ma su ka daura daga
inda suka tsaya na ci gaba da tumurmusa
Nijeriya. inda suka gasa wa mutane aya a hanu,
suka karya tattalin arzikin Nijeriya. don haka duk
irin wannan mutumin, don ya zo ya fadi irin wadannan maganganun ai ba abun mamaki
bane. To, amma a ganina, da kuma hangen
dukkanin wani mai hankali shi ne, ya kamata shi
Obasanjo ya fa gane cewar irin wannan siyasar
da suke yi na warwaso da kashe mu raba yanzu
lokacin irin wannan siyasar ta wuce a Nijeriya, ba ta da gurbi a zukatan ‘yan kasa. Ba ka ganin za a yi cewa Obasanjo ya san siyasar Nijeriya sosai, don haka abun da ya hango kan Buhari zai taimaki kasar nan? Ina ganin dukkanin wani mataki da Cif Obasanjo
ya taka a rayuwa ina ganin babu wadda Buhari
bai taka ba; sai dai ma a ce Buhari ya fi shi. Idan
gadararsa ya taba zama Janaral ne na soja, Buhari
ma Janaral ne na soja, idan gadararsa ya yi
shugaban kasa na soja ne Buhari ma ya yi shugaban kasa na soja, sannan idan gadararsa
shugaban kasa na farar hula da ya yi ne, shi ma
Buharin yanzu ga shi yana yi, yana kai. Akwai
kuma abubuwa da dama tun a zamanin sojan ma
wadda Buhari ya yi wadda shi Obasanjo bai yi su
ba. Saboda haka tsohon shugaban kasa Cif Obasanjo ya kwatanta Buhari da cewar wadda ba
zai iya mulki ba, wadda bai san mulki ba; wannan
na fadin son ransa ne kawai, yana kuma fada ne
domin sun ga cewar Buhari yana da kawa da
kawaici a cikin lamarinsa, domin da wani ne
shugaban kasa a halin yanzu a Nijeriya a wannan halin da ake cikin nan da yanzu Obasanjo duk
dukiyar kasar nan da ya sata da ya yi baba-kere
da su da ya amayar, kuma da ya jima da
kasancewa a gidan kurkuku, saboda duk irin cin
kasa da suka yi wa Nijeriya, shi bai ga abun da
suka yi wa Nijeriya na hardasa fitinu na yankuna da na banbancin kabila da na addini da suka
dasa a zukatan mutane. Don haka, irin wadannan
kalaman duk ra’ayinsa ya fada kuma, ina son ya
jira da shi da dukkanin ‘yan tawagarsa masu
mara masa baya su jira su gani, Allah ya kaimu
lokacin zabe a 2019, za su gane cewar yanzu ne ma Dimukuradiyya ta yarda da lamarinsa take
kokarin kara goya masa baya, domin ina mai
tabbatar maka cewar kuri’ar da Buhari zai samu a
zaben 2019 sai ya fi wadda ya samu a zaben da
ya gabata. Shin ba ka ganin ra’ayinsa za su yi tasiri domin ya samu goyon baya daga wasu gwamnoni da sanatoci da masu fada a ji kamar yadda ake cewa wasu suna shirye- shiryen mara masa baya da dama? Ba za ka hana mutum ra’ayinsa ba ai. Idan ka ce
akwai gwamnoni da wasu sanatoci da ma
sauransu da suke kokarin mara wa Obasanjo
baya kan ra’ayinsa nan, wannan ba abun
mamaki bane, ai ko a zaben da aka yi akwai
gwamnoni da sanatocin da PDP suka yi, kuma a yanzu din ma akwai gwamnoni da sanatocin da
suke PDP. To, Malam duk wadda yake PDP ko
yake da ra’ayin PDP ai Obasanjo ubansa ne, kuma
har ya mutu ba zai mance da Obasanjo ba; tun da
Obasanjo ya yi musu shugaban kasa a shekara
takwas, kuma ya yi musu abubuwan da suke so, ya kai jam’iyyar matakin da ba tsammata ba; ka
ga duk wani dan PDP da ya ce maka zai zagi
Obasanjo ko zai raina Obasanjo wannan zai yi ne
kawai saboda rashin kunya irin tasu da suka
gada. To, amma ina mai tabbatar maka da cewa
da sanatoci da gwamnoni nasu da suka ce suna tare da shi a kan ra’ayinsa na kada Buhari ya
maimaita mulki daman suna tare da ra’ayin uban
gidansu Obasanjo tuntuni, suna jikin Buhari ne
kawai na dole, don haka idan yanzu sun je sun yi
tarayya da tsohon shugaban kasan ba wani abu
bane ai, siyasa ake yi kuma lokaci zai nuna. Idan fa muka dubi baya, Obasanjon nan ya dafa wa Buhari ko na ce ya mara masa baya a 2015 har ya kai ga nasara, bayan ya zama shugaban kasa ya ci gaba da ba shi shawarwari da sauransu, yanzu da ya zo ya ce kada ya maimaita ba ku ganin da gaske kurakuran ya hango? Obasanjo bai mara wa Buhari baya ba; Obasanjo
dai ya yaga katin jam’iyyarsa ta PDP, ya kuma yi
rawa a gaban jama’a, ya yaga katin jam’iyyarsa.
Yaga katin jam’iyya da yin rawa a gaban duniya ai
ba goyon baya bane. Batun ya mara wa Buhari
baya fa ba ta taso ba, na sake nanatawa. Lokaci ne dai kawai ta kure masa, ka san idan mutum
ruwa zai ci shi ko takwabi ka mika masa zai
kama, abun da ya faru ya ga zabe ya karato ‘yan
takarkarunsu ba za su kai labari ba, sai shi ma ya
zo ya narke a cikin jama’an Nijeriya domin a ce
masa shi ma ya yi dattako ya mara wa Buhari baya. Amma batun mara wa Buhari baya daga
Obasanjo kam babu shi, wadanda suka mara wa
shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari baya
daga cikin manya kam mun sansu, ko a boye ko
a bayyane dukkaninsu mun sansu. Tabbas muna
zaune a jihar Bauchi amma idanuwanmu suna ko’ina, kunnuwanmu suna ko’ina, mu kan kuma
tashi mu je, wasu akan fada mana, wasu kuma
muna ganinsu da idonmu, masu fada mana din
kuma daga bakunan da basu karya a siyasance
su ne ke fada mana. Idan muka dawo gefe guda, Jihar Bauchi tana gaba-gaba wajen yin Buhari, shi a zaben 2019 kuna da wani shiri ne a matsayinku na matasa wajen ganin kun mara wa Buhari baya? Tabbas kuwa, wannan ai ko shakka babu, a
bana kam ma duk kuri’ar da za a samu a wannan
zaben ina mai tabbatar maka na matasa ne,
domin matasa sune ke amfanar wannan
gwamnatin fiye da kowa, matasa sun shiga
hayyacinsu, matasa sun samu tallafin karatu a matakai daban-daban wasu sun tafi karatu
kasashen waje a wannan gwamnatin, matasa sun
samu tallafin N-POWER a wannan gwamnatin,
matasa sun tafi aiyuka daban-daban a Nijeriya,
musamman iyayenmu mata wannan tsarin
ciyarwa na ‘yan makaranta wadda gwamnatin tarayya ta bullo da shi ya samar da aiyukan yi
sosai da kuma inganta tattalin arziki, a nan jihar
Bauchi gwamnatin tarayya ta kawo gwamnatin
Bauchi ta sake fadada ta ninka ta kuma kara fiye
da na gwamnatin tarayyar ma domin mutane su
samu abun da za su ke taimaka wa kawukansu. Ina tabbatar maka zaben da za a sake yi a Nijeriya
matasa ne za su yi ta, kuma wallahi ina tabbatar
maka APC za mu sake yi sama da kasa sak, mu
mutanen Buhari ne kuma, ina mai tabbatar maka
duk inda Buhari ya sanya kafarsa tamu tana biye,
wannan shine akidarmu a siyasa kuma babu wadda ya isa ya sauya mana ita. Wani kwarin guiwa kake da shi na cewar Buharin nan zai tsaya ma takara a 2019? Kwarin guiwa na shi ne yadda Buhari ya dauko
hanyar gyara Nijeriya kuma sai ya ida, shi ne
kowa ya san akwai doka a Nijeriya, kowa ya
dauki dukiyarsa ya tafi a jikinsa ya tafi duk inda
yake bukata domin tsaro ya samu a Nijieriya. Mu
‘yan Arewa Maso Gabas mu gode wa Allah domin in muka yi wa Allah butulci zai iya kawo mana
jarabawar da ba za mu iya daukewa ba. ina mai
tabbatar maka cewar idan muka bijeri da abun da
Buhari ya kawo mana a shiyyar Arewa maso
gabas wallahi abun da zai faru bai da dadi, don
haka ina kiran mutane musamman shiyyar Arewa Maso Gabas su yi wa kawukansu karatun ta
nutsu, su guje wa wadanda za su iya ta tarasu
suna ce musu ga wannan kuje ku sayi koko da
safe a gidanku, duk an yi wannan a ba, ka sayi
kunon shansa ya gagareka, a kashe maka mata,
‘ya’ya, ‘yan uwa duk an yi wannan a baya, don haka ina kira a garemu da mu tashi mu zabi
wadda ya dace wato Buhari. Da ka ke maganar Arewa Maso Gabas, yanzu fa su ‘yan shiyyar sun yunkuru sun ce ba wai so suke su mara baya ma wani ba, a’a suna so ne shugaban kasa ya fito daga yankinsu domin su ma su yi shugabancin kasa, ba ka ganin Buhari ba zai samu tulin kuri’u a nan yankin ba? Shi wannan wadda suke maganar za su tsaida shi
daga Arewa Maso Gabas din ai ga fili ga mai doki
sai mu gani, mune ‘yan Arewa Maso Gabashin
Nijeriyan, ni dan jihar Bauchi ne, kuma Bauchi
itace tushen Arewa Maso Gabas ga filin mu gani,
su dauko shi a kowace jam’iyya ne a Nijeriya mu kara da su mu gani, za su gane cewar siyasa ta
haramta wa shi wadda suke maganan a Nijeriya.
Mutanen da sun rike mukamai basu yi komai ba;
wai har magobayan shi wadda kake maganan
suna bude maki suna cewa ai yin kwalta ba aikin
mataimakin shugaban kasa bane, bai da wani hurumi wajen gudanar da mulki. To a nan jihar ta
Bauchi mace kwamishina ta yi titi (kwalta) mai
tsawon kilomita goma sha a jihar nan. Matar nan
a karamar hukumarta ta Dass ta yi wannan
kwaltan, ta shimfida ya wuce har garinta ya je
wajen wani bakin kogi a nan kwaltan da ta yi ya tsaya, kwamishina fa kenan kuma mace. Balle ka
zo kana ce min wadda ya rike mataimakin
shugaban kasa bai iya samar da ko titi wa
jama’an yankinsa ba, amma wai yana maganar
neman shugabancin kasa tir. Mu dai a Arewa
Maso Gabas muna nan sai Buhari, ba mu ce bamu saon shugaban kasa daga yankinmu ba, a tsaya
Buhari ya kammala dukkanin wa’adinsa. Daga
nan sai mu duba mu ga wani irin zubi da za a yi,
alabashi mu zo mu zauna mu ga waye ya dace
daga arewan maso gabas din mu zabo wadda ya
yi wa jama’ansa aiki, bawai mutum na nan daga shi sai ‘ya’yansa ba ya zo yace zai mulkie.
Dukkaninsu wadanda suke kokarin yakar
Buharin za ka samu za ka ga barayi ne. Bayan wannan da kake ta nuniyar a kansa shi daya, ai akwai wasu daga wannan shiyyar ko su su dace su kara da Buhari? Ai ni ban san da wasu suna neman wannan
kujerar ba, ai duk wadda ake maganar
tsayawarsa takarar shugaban kasa mutum daya
ne a shiyyar Arewa Maso Gabas kuma kowa ya
sani shi ne Atiku Abubakar, abun da ya sa na
kama maka suna shine don a san da wa nake yi kai tsaye. Me jiya ta yi balle yau?. Kasar nan ta
Nijeriya Atiku da Obasanjo su ne suka kasheta,
Billahillazi wallahi da badin Buhari Allah ya sa
masa wani irin ruhi na kaunar al’umma da son a
zauna lafiya ba, da tuni wadanan ba a san wani
irin kurkuku ma za a sanya su ba; duk wani irin cin kasa da aka yi wa Nijeriya Obasanjo da Atiku
su ne suka yi wannan, su suka lalata Nijeriya. don
haka mu babu ruwan da wai maganar dole sai
‘yan Arewa Maso Gabas ya yi shugaban kasa, ai in
ma haka ne akwai mutanen kwarai da su ne za
mu tsayar, don haka mu bamu so, ba ma so! Ba ma so!!. Ba yanzu ba, sai lokacin da masu neman
suka gyara kansu suka taimaka wa jama’ansu na
shiyyar Arewan daga nan sai mu ga mene ne ya
dace da mu. Bar na ba ka misali, a shiryyar Kudu
Maso Kudu da Kudu Maso Yamma, Da Kudu Maso
Gabas akwia mutanen da in suka tsaya suka ce wane za a yi, wallahi duk shi za a yi, meye sa?
Saboda sun taimaka wa mutanensu tuntuntuni,
ba yanzu kawai mutum ya zo yace zai so mulki
ba. muna nan da kai, jam’iyyar da yake son su
tsaida shi, idan suka hanasa zai sake komawa
wata jam’iyyar a haka zai kare a siyasa, muna nan za kuma ka ce na fada maka wannan. Don haka mu muna tare da Buhari, Shiyyar Arewa
Maso Gabas gaba daya na Buhari ne, babu wani
mahalukin da zai zo ya nuna kabilanci, in
kabilancin ne lokacin da ka samu dama meye sa
baka kawo wa al’ummanka ci gaba ba; sai
lokacin da ka rasa mafadi, ba mu bukata Buhari muke yi, duk kuma wadda zai ja da Buhari za mu
kara da shi Allah ya kaimu ran zaben.
.
©hausaleadership
COMMENTS