Yar shugaban wata ƙungiyar asiri, mai aƙidar auratayya birjik, mai suna Warren Jeffs ta ce, Mahaifin nata yayi ta saduwa da ita tsawon sheka...
Yar shugaban wata ƙungiyar asiri, mai aƙidar
auratayya birjik, mai suna Warren Jeffs ta ce,
Mahaifin nata yayi ta saduwa da ita tsawon
shekaru, tun tana ‘yar ƙaramar Yarinya, har zuwa
lokacin da take girma a cikin ƙungiyar ta asiri. Ta bayyana hakan ne a wata zantawa da ita da
aka yi a ranar Juma’ar da ta gabata, a cikin shirin
‘Megyn Kelly Today’. Rachel Jeffs, wacce a yanzu take da shekarun
haihuwa 33, ta shaidawa Gidan Talabijin na NBC
cewa, Mahaifin nata ya fara yin lalata da ita ne tun
tana da shekaru 8 a Duniya, inda bayan nan ya yi
ta saduwa da ita sau ba adadi, duk da yunƙurin
da mahaifiyarta ta yi na dakatar da hakan, haƙar ta bai kai ga nasara ba sai da ta kai shekarun
haihuwa 16. Wasu Mambobin Cocin ‘Fundamentalist of Jesus
Christ of Later day Saints’ wanda ya ƙunshi har da
Ɗan sa Roy Jeffs, su ma sun zarge shi da yin lalata
da su tun lokacin suna yara. Rachel Jeffs ta rubuta wani Littafi, wanda ta
bayyana irin abubuwan da ta sani, inda ta sanya
wa Littafin suna ‘Samun ‘Yanci: Yadda aka yi na
tsira daga Auratayya, Ƙungiyar asiri ta FLDS da
kuma Mahaifi na Warren Jeffs’. Yanzu haka dai Warren Jeffs yana zaman kaso a
Kurkuku sakamakon hukuncin da aka zartar
masa a kan lalata da yayi ta yi da ƙananan Yara
Mata, wa’yanda yake ɗaukan su a matsayin Matan
sa, ba shi da wani Lauyan da yake kare shi,
sannan ya ƙi tankawa buƙatar Tashar NBC na ji daga bakin sa. Lokacin da Rachel Jeffs take ‘yar shekaru 18 an
sanar da ita cewa za ta kasance Mata ta 3 ga wani
mutum a cikin ƙungiyar tasu, lamarin da yayi
matuƙar bata tsoro, da kuma girgiza ta. Ta bar ƙungiyar nasu ne bayan da Mahaifin ta ya
kore ta daga wurin ‘ya’yanta na tsawon watanni,
bayan ya tuhume ta da aikata laifin da ita kuma
take musanta aikatawa. “Na ji a raina kamar yana yi mini horo ne a kan
laifukan da ya aikata a kai na, na ji kamar yana so
in rasa duk wani ƙwarin guiwa ne, sannan in
ɗauki kaina a matsayin wacce ta fi shi wofinta, ba
zan taɓa mayar da kaina in zama hakan ba, na san cewa yayi ta aikata abubuwan da ba daidai
ba, dan haka ba zan taɓa bari ya mayar da ni in zama marar ƙwarin guiwa ba”.
©hausaleadership
COMMENTS