Blog Archive

Powered by Blogger.

Wata Uwa Ta Yi Barazanar Rataye Kanta Idan har ’Yan Sanda Suka Gaza Gano Inda Danta Yake

Wata uwargida mai suna Wuche Ajuru, mahifiya ga wani matashi dan shekara ashirin da uku mai suna Happiness Ajuru, wanda ya bace daga hannun ...



Wata uwargida mai suna Wuche Ajuru, mahifiya
ga wani matashi dan shekara ashirin da uku mai
suna Happiness Ajuru, wanda ya bace daga
hannun ‘yansanda a garin Fatakwal a cikin jihar
Ribas, ta yi barazanar kashe kanta tare da mijinta
in har ‘yansanda suka gaza fito mata da danta. Happiness, wanda mazauni ne a garin Ndele
dake cikin karamar hukumar Emohua, ‘yansanda
sun cafke shine a ranar 28 ga watan Satumbar
shekarar 2016. Bayan kwana biyar yana tsare a
ofishin na ‘yansanda dake Rumoji yaron ya bace. Koda yake, babu wani bayani da aka bayar akan
dalilin kamun da aka yiwa yaron,kuma har naira
dubu 49,000 da kuma wayar sa ‘yansanda sun
karbe. Matar a hirar ta da manema labarai a Fatakwal a
ranar Jumar data gabata ta ce, tana cike da tsoro
kuma tana ganin zata iya zama mahaukaciya
domin a kullum tana tunanin cewar ‘yansanda
sun kashe mata dan nata ne. Wuche ‘yar shekara The 38 da haihuwa a cikin
kuka a lokacin da take hirar da manema labarai
ta ce, ita da mijinta zasu rataye kansu, in har
‘yansandan suka ki yi masu bayani akan me ya
samu dan nasu. Ta zargi wani dattijo dake yankin mai suna
Sampson Agbaru akan kin sanya baki a cikin
maganar, sai dai ta ce, tana sane da cewar,
‘yansandan sun cafko mutane hudu a ranar 20
ga watan Janairun shekarar 2018 akan maganar
kuma mutanen da aka cafko sune, Okechukwu Eleonu, wanda ya bayar da naira 60,000 don ayi
belin dan nata wanda tuni aka bayar da belin
nasa. Matar wadda take sana’ar sayar da Garin Rogo ta
zargi ‘yansanda akan yin rufa-rufa akan maganar
don sunga ita talakace kuma bazata iya bin
maganar ba sau da kafa ba. A cewar ta, “na san ni talakace, amma a shirye
nake in rataye kaina, in har ‘yansanda sukaki
gaya mini a ina suka boye dana Happiness”. Taci gaba da cewa,” Agbaru ba dansanda bane
kuma bai kamata ya kasance a tsakiyar maganar
ba, in kuma yaci gaba da kasancewa a cikin
wannan maganar, nida mijina zamu kashe
kanmu a cikin wannan gidan.” Ta kara da cewa, “suna yi mini hakan ne saoda ni
talakace, kuma banda kudi, amma inada Allah
wanda yafi karfin Agbaru da Eleonu da kuma
‘yansanda.” Matar ta ce, “ina son maganar taje gaban Kotu
saboda ban yadda da ‘yansanda ba kuma zanci
gaba yiwa dana yaki har sai naga bana
numfashi.” Tayi tambaya da cewa,”me yasa suka karbi naira
3,000 daga gare ni ? na kuma basu naira 5,000
don su sanya mai a motar su, kuma shin, me ya
faru da naira 60,000 wadda aka karba daga gare
ni wanda ya kamata ace an baiwa ofishin
‘yansanda na gundumar don su sako min dana?” Ta ce, “in har suka ci gaba da tabka mini karya,
zan wuce Kotu, kuma ina son ‘yansandan su
gaya mini ina dana yake, domin dana baida wani
laifi kuma shi ba dan kungiyar asiri bane.” Lauyan matar mai suna Mista Ransome Worgu, ya
yi kira ga shugaban rundunar ‘yansanda ta kasa
Ibrahim Idris da ya duba maganar don a bayyana
maganar ba cewar yaron wadda yake karewa da
ya bace daga hannun ‘yansanda na dake Rumuji,
a cikin karamar hukumar ta Emohua dake jihar ta Ribas. Worgu ya yi zargin cewar Eleonu ya tsallake beli a
shekarar 2013 bayan da ‘yansanda suka cafko
shi akan zargin yin kisa kuma aka bayar da belin
sa da kuma akan ba cewar Happiness daga
hannun ‘yansanda. Lauyan ya kuma zargi ‘yansanda akan yiwa
matar da yake karewa barazana, inda har ta yi
kurarin zata hallaka kanta idan aka kashe mata
danta kuma zata ci gaba da neman danta
Happiness. A cewar sa,“ ban san dalilin da ya sanya
‘yansandan suka gaggauta sako wadanda ake
zargi akan ba cewar yaron daga hannun
‘yansanda ba kuma wadda nake karewar, an
gayyace ta zuwa Abuja, amma bata da kudi don
yin tafiyar. A cewar sa,”zamu ci gaba da yin matsin lamba
akan maganar saboda muna son wannan ya
zama na karshe akan yadda ‘yansanda suke
kashe wadanda basuji basu gani ba a lokacin
suke tsare dasu.” Worgu yace, da aka tuntubi Agbaru, ya karya
sani wata masaniya akan ba cewar Happiness
daga hannun ‘yansanda. Yace ya amince ne kawai da belin Eleonu a
lokacin da aka tsare dashi a wurin ‘yansandan a
wasu lokuta da suka shige. Agbaru, wanda tsohon Sakataren Gwamnatin
Jihar ne, ya zargi matar akan yunkurin hallaka
shi, ya kara da cewa, matar tana son ta bata masa
suna. Yace, “idan ta ce zata hallaka kanta a gidan ta,
zata sha mamaki akan wannan ikirarin nata,
domin nine zan fara mutuwa a gidan ta, domin ni
banda wata masaniya akan maganar yaron da
suke magana akai.” Ya kara da cewa, “ naje kawai nayi belin din Eleon
a lokacin dana samu labari cewar ‘yansanda sun
kama shi, kuma matar da take zargi na, daidai
take da shekarun ‘yar dana haifa, domin a yanzu
na kai shekaru 84 da haihuwa kuma ita ce za’a
zarga in wani abu ya same ni. ” Shi kuwa DPO na ofishin ‘yansandan inda aka
tsare Happiness ya kuma bace, a yanzu haka
anyi masa canjin aiki, inda ya zama kwamanda na
rudunar yaki da ‘yan fashi da makami dake jihar
Edo. Kwamandan mista Idachaba ya karyata karbar
wadannan kudade daga gun mahifiyar
Happiness. Yaci gaba da cewa, wata mata ta tunkare shi
wadda ta yi ikirarin cewar ta turo mini da naira
60,000 ta hanyar wani shugaban matasa don a
saki wanda ake zargi wanda aka zargi da
‘yansanda suka cafke a lokacin da aka kai
samame akan wasu gungun wadanda ake zargin yan kungiyar asiri ne da kuma wasu ‘yan tayar da
kayar baya. A cewar sa,“Ina son in sanar daku cewar a wani
lokaci a cikin watan Yuni na shekarar 2016, anyi
min canjin wurin aiki zuwa ofishin ‘yansanda
dake Rumuji saboda wasu ‘yan kungiyar asiri
tare da wasu ‘yan tayar da kayar baya sun kai
farmaki a ofishin na ‘yansandan, inda har aka cire DPO din daga ofishin aka kawo ni. Kwamandan ya kara da cewa, “ba’a jima ba
bayan naje wurin, nima wadannan gungun suka
kai mani farmaki, amma basu samu damar shiga
ofishin ba, kuma a wannan daren sai muka
sanya aka karo mana dakaru, inda muka samu
muka iya tarwatsa gungun tsagerun da ‘yan kungiyar asirin suka arce zuwa cikin gari muka bisu muka
kashe mutum biyu daga cikinsu da kwato
bindiga daya.” A cewar sa, “uwar yaron tazo guna, inda ta ce
shugaban matsan dake yanki ya karbi kudin da
suna na a matsayin DPO, inda ta ce, mutumin
yace zai zo ya bani kudin don in saki wani da aka
kama da dare, kuma a lokacin da matar ta same
ni, na gaya mata cewar ta koma ta tambayi mutumin.” Yaci gaba da cewa, “matar ta sake dawo wa, inda
ta ce lallai mutumin bai bani kudin ba don in saki
wani na kuma gaya mata bani da bayanin akan
wanda take magana akai a ofishi na.” Kwamandan yace, “da muka gayyaci mutumin da
ta ce ta bashi kudin, mun kira matar cewar ta zo
don ta babbance akan zargin nata, amma batazo
ba.” Idachaba ya kuma karyata sanin wani mai suna
Happiness har zuwa iya tsawon zaman da ya yi a
matsayin DPO a yankin, inda yace, anyi masa
canjin wurin aiki a watan Disamba na shekarar
2016, kuma ba cewar Happiness ta auku ne a
shekarar 2017 wannan wani abune da banda masaniya akai. Sai dai, kakakin rundunar ‘yansandan jihar ta
Ribas Mista Nnamdi Omoni, ya bayyana cewar
ana ci gaba da gudanar da bincike akan
maganar, inda yace, “a lokaci na karshe dana
duba maganar na lura cewar ba cewar Happiness
Ajuru daga hannun ‘yansanda, jami’an mu na sashen bincike na gudanar da bincike akan
maganar
.
©hausaleadership

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Wata Uwa Ta Yi Barazanar Rataye Kanta Idan har ’Yan Sanda Suka Gaza Gano Inda Danta Yake
Wata Uwa Ta Yi Barazanar Rataye Kanta Idan har ’Yan Sanda Suka Gaza Gano Inda Danta Yake
http://fm.nextwapblog.com/files/6475/igiya.jpeg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/02/wata-uwa-ta-yi-barazanar-rataye-kanta.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/02/wata-uwa-ta-yi-barazanar-rataye-kanta.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy