Blog Archive

Powered by Blogger.

Yadda Matasa Masu Kirga Buhun Gero Suka Sa Jihar Kebbi A Idanun Duniya

Jihar kebbi dai ta zama wata fitila ga idon kasashen duniya kan wasu matasa na masarautar Yauri da ke a jihar da suka shiga mahawara ta sani...


Jihar kebbi dai ta zama wata fitila ga idon kasashen duniya kan wasu matasa na masarautar Yauri da ke a jihar da suka shiga mahawara ta sanin kwarar gero nawa ne ke cikin buhun gero mai nauyin kilo 100, kan haka ne garin na Yauri ke daukar baki na gida Najeriya da kuma ne kasashen duniya domin ganin irin yadda suke kirga kwarorin buhun geron. Garin na Yauri yana daya daga cikin masarautun gargajiya hudu da ke akwai a jihar ta kebbi, inda ya zama wani gari da ake zuwa yawon bude ido kan wasu gungun matasa da suka aza wata mahawara kan cewa buhun gero ya fi ‘yan kasar Najeriya yawa wasu kuma daga cikin matasan suka cewa ‘yan kasa sun fi buhun geron yawa wanda dukkan matasan na zamane a wata majalisa da suka hada domin hutawa a duk lokacin da suka dawo daga wuraren ayyukkansu da yamma. Bisa ga wannan ne suka shiga kirga buhun gero domin sanin iya addadin kwarorin geron da ke a cikin buhu mai nauyin kilo 100 a majalisar matasan da ke a unguwar Katungu da ke cikin garin Yauri da matasan samarin ke zama kowane yammaci bayan sun dawo daga ayyukkansu na gwamnati da kuma kasuwanci a garin na Yauri da ke a jihar ta kebbi. Bayan sun shiga kirga geron jama’a da dama na gida Najeriya da kuma na wasu kasshen duniya na ganin cewa wadannan matasan na garin Yauri da ke a jihar ta kebbi kamar basu da aikin yi ne yasa suka shiga mahawawar na sanin kwara nawane a cikin buhun gero. Saboda haka bayan sun fara kirga buhun, sai maganganu suka fara zagayawa a duk fadin kasar nan da kuma wasu kasashen duniya baki daya kan muhawawar kirgar buhun gero da matasan garin Yauri suka shiga gudanarwa a majalisar da suke zama a Yauri , wanda ta hakan ne suka sanya jihar kebbi da kuma masarautar Yauri ga idon duniya. Inda mutanen jahohin kasar nan da ma na kasashen waje kamar irin mutanen jamhuriyar Nijar , jamhuriyar Benin, china da kuma Amurka da kuma wasu masu gudanar bincike na tihiri kan wani abu da dan adam zai iya gudanarwa a zaman rayuwarsa da kuma sauran sun nata tattaki zuwa garin na Yauri domin ganewa idonun su abin da matasan garin keyi. Rahotannin da ke fito wa daga garin na Yauri da kuma wanda wakilinmu ya tattaro muna na nuna cewa matasan sun fara kirga buhun geron tun kimanin watanni uku da suka gabata inda a halin yanzu suna batun kammala aikin kirga buhun geron . Domin jin ta bakin matasan da ke kirgar kwarorin gero da a cikin buhu kuma gani da ido Jaridar LEADERSHIP A Yau tayi tattaki zuwa garin na Yauri domin tattanawa da Shugaban majalisar matasan na garin Yauri ya kuma kasance shugaban kwamitin kirgar buhun geron, Ahmad Sarkin Yakin Yauri , ya ce “ A kowane rana daga randa muka fara kirga buhun geron nan, ina amsa kiran wayar ta ta hannu daga mutanen a kullun da zaikai sau ashirin daga nan gida Nijeriya da kuma kasashe kamar jamhuriyar Nijar, Jamhuriyar Benin, China, ingila da kuma Amurka da sauran su”. Kazalika ya ce “ mun fara kirga buhun geron nan kimanin watanni uku da suka gabata”. Saboda haka daya daga cikin alkawalin da muka dauka shine bazamu bayyana sakamakon kirgar ba sai mun kammala bakin . Haka kuma ya kara da cewa jama’ar da ke bugo waya na son susan kwarar gero nawa ne ke cikin buhun mai nauyin kilo dari. Saboda irin yadda maganar kirgar buhun geron yasa mutane daga ko ina a cikin kasashen duniya na tattaki kan shigowa garin na Yauri da kuma domin ganewa idanunsu a cikin satutukkan da suka gabata kai wasu har da bugo waya hannu . Wannan kirgar buhun geron dai garin Yauri a unguwar Katungu da ke a cikin karamar hukumar mulki ta Yauri a jihar kebbi. Haka kuma ya ce “ duk wanda ya bugu waya yana son ji kwara nawa ne a cikin buhun gero sai in gaya musu cewa bamu kammala kirgar buhun ba, saboda haka ku jira idon mun kammala kirgar buhun geron zamu sanarwa mutanen duniya baki daya domin sanin ko kwara nawa ne ki a cikin buhun gero mai nauyin kilo dari. Daga nan ne zamu iya sanin cewa ko kwarar gero da ke ciki buhu mai nauyin kilo dari yafi ‘yan kasa yawa ko ‘yan kasa sun fi yawa. Bugu d

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Yadda Matasa Masu Kirga Buhun Gero Suka Sa Jihar Kebbi A Idanun Duniya
Yadda Matasa Masu Kirga Buhun Gero Suka Sa Jihar Kebbi A Idanun Duniya
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhf_7OVXJu71AQnIqr5bpkkGiNMWlk7ZZ6sZrtz5iM8Qyxu1jDQQln-sXmmaWoWAQIzigRJmlEvCdwTHtEIbERKZF0uT4ZcBjRB0YouNIdrYtCALvhqDwAgRuMP1aeLPzVauhb4oNVQ5gbG/s320/Page-26-a-yayin-da-matasan-ke-qirga-buhun-geron.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhf_7OVXJu71AQnIqr5bpkkGiNMWlk7ZZ6sZrtz5iM8Qyxu1jDQQln-sXmmaWoWAQIzigRJmlEvCdwTHtEIbERKZF0uT4ZcBjRB0YouNIdrYtCALvhqDwAgRuMP1aeLPzVauhb4oNVQ5gbG/s72-c/Page-26-a-yayin-da-matasan-ke-qirga-buhun-geron.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/yadda-matasa-masu-kirga-buhun-gero-suka.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/yadda-matasa-masu-kirga-buhun-gero-suka.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy