Blog Archive

Powered by Blogger.

Shugaba Buhari Zai Sake Lashe Zabe A 2019 – inji Nda-Isaiah

Shugaban rukunin kamfanonin LEADERSHIP, Sam Nda-Isaiah, ya bayyana tabbacin da yake da shi na cewa, Shugaba Muhammadu Buhari, zai sake lashe...


Shugaban rukunin kamfanonin LEADERSHIP, Sam Nda-Isaiah, ya bayyana tabbacin da yake da shi na cewa, Shugaba Muhammadu Buhari, zai sake lashe takarar shugabancin kasar nan a babban zaben 2019. Sam Nda-Isaiah ya ce, kyawawan ayyukan da shugaban ya yi a karkashin gwamnatin Jam’iyyar APC ne za su sake maido da shi a karagar mulkin kasar nan. Sam Nda-Isaiah, ya yi wannan bayanin ne ga manema labarai a Akure, ta Jihar Ondo, jim kadan da nada shi Sarautar, ‘Aare Baroyin’ na dadaddar masautar ta Akure, a karshen makon nan. “Ni dan Jam’iyyar APC ne, zan ci gaba da goyon bayan dan takaranmu na shugabancin kasa, Muhammadu Buhari, a wannan babban zaben na 2019. “Tabbas zai cinye zaben, duk da yake ba za mu yi sakaci da lamurran ba, amma dai muna da tabbacin zai lashe zaben ba tare da wani wahala ba. A cewar sa, kasar nan ta samu canji mai yawa a karkashin gwamnatin ta Jam’iyyar APC, musamman a fannin noma. “Abubuwa sun fara farfadowa, kasarmu ta zama ma fi girman tattalin arziki a Afrika duk da irin kalubalen da muka yi ta fuskanta. “Kar ku manta da irin halin ni-‘ya-sun da tattalin arzikinmu ya shiga, don haka tilas ne abubuwa su canza, yanzun kuma mun fita daga wannan yanayin na tabarbarewar tattalin arzikin. “Kwanan nan, za ku ga kasar nan ta zama mai dogaro da kanta ta fuskacin shinkafar da za mu ci, wanda hakan bai taba faruwa ba a baya. “Ba cewa nake yi mun iya cika duk alkawurran da muka yi ba, amma dai kun san ai muna kan hanyar hakan. “Kowa ya ganin ma idonsa, ai dan adam tara yake bai cika goma ba, ina da tabbacin za mu sake lashe zaben.” Da yake magana a kan zabukan fitar da gwani na Jam’iyyar wadanda suka janyo cece-kuce masu yawa a tsakanin ‘ya’yan Jam’iyyar, Nda-Isaiah, ya bayar da tabbacin duk za a sasanta komai kafin babban zaben na 2019. “Ban ji dadi ba, musamman a kan abin da ya faru a Jihar Zamfara, duk da yake dai mun je kotu, amma dai ban san yanda lamarin zai karke ne ba. “In har muna son ci gaba da mulkin kasar nan, ya zama tilas mu bayar da misalin abin da ya fi kyau a bisa na Jam’iyyar PDP. “Za dai mu yi nasara, amma dai gaskiya an yi abin da bai kamata a ce ya faru a hakan ba a wajen.”

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Shugaba Buhari Zai Sake Lashe Zabe A 2019 – inji Nda-Isaiah
Shugaba Buhari Zai Sake Lashe Zabe A 2019 – inji Nda-Isaiah
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEj1xdjILc33bG3p4ua3vxOmjPH3nZWwEJPFdcZkUU1hpxEq5851WJTAk9UfgYquVsslspP5qOWzCMB0EjqGbitPPqW7u4-tB4nL5RyhAlqAaWyh3RDpYsqNJk9TVEtgKcyKhx-qgLQfwGAQ/s320/David-Mark.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEj1xdjILc33bG3p4ua3vxOmjPH3nZWwEJPFdcZkUU1hpxEq5851WJTAk9UfgYquVsslspP5qOWzCMB0EjqGbitPPqW7u4-tB4nL5RyhAlqAaWyh3RDpYsqNJk9TVEtgKcyKhx-qgLQfwGAQ/s72-c/David-Mark.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/shugaba-buhari-zai-sake-lashe-zabe-2019.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/shugaba-buhari-zai-sake-lashe-zabe-2019.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy