Blog Archive

Powered by Blogger.

Shin kunsan Kalubalen da ke gaban Buhari da Atiku Wajen cin zabe

Zabukan fitar da gwanin 'yan takarar shugaban kasa a Najeriya na nuna cewa takarar yanzu ta koma tsakanin shugaba mai ci, Muhammadu Buha...


Zabukan fitar da gwanin 'yan takarar shugaban kasa a Najeriya na nuna cewa takarar yanzu ta koma tsakanin shugaba mai ci, Muhammadu Buhari na Jam'iyyar APC da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP. Kowannensu yana da karfi irin nasa. Shugaba Buhari mutum ne wanda kimarsa ta zama jarinsa a siyasar Najeriya kamar yadda shi kuma Alhaji Atiku Abuakar ke daukar wayewarsa a matsayin wani jari da zai kai shi ga ci. Ya rage wa 'yan Najeriya su zabi daya daga cikin wadannan mutane biyu da zai zama shugaban kasar idan har an yi zaben gaskiya da adalci. Ko shakka babu, Shugaba Buhari ya nuna shi mutum ne mai kyawun hali, wanda ba ya karbar cin hanci, kuma ba ya bayarwa, ba ya goyon bayan a karba, ko a bayar, kuma yana nisantar aikata abin kunya. Ya tabbatar wa 'yan kasar cewa shi mutum ne da zai iya rike amanarsu, al'amarin da ya kawo masa rashin jituwa tsakaninsa da wasu abokansa da 'yan uwa da masoya. Ina Buhari yake da rauni? Amma masu nazarin harkokin siyasar kasar suna ganin yana da wani rauni a matsayinsa na shugaba. Ana zarginsa da yin saka-saka da harkokin mulki, da rashin daukar mataki kan mukarraban gwamnatinsa da ke saba wa umurninsa. An ce ya sakar wa wasu 'yan barandarsa ragamar mulkin kasar wanda ya janyo wasu manyan kura- kurai da bai kamata su faru ba. Haka kuma, wasu na ganin cewa tsarin tattalin arzikin da gwamnatinsa ta kawo yana barazana ga rayuwar ma'aikata masu matsakaicin albashi, da jefa talakawa cikin mummunan talauci. Ana yi wa shugaban kallon mutumin da ya zo don gyara barnar da ya ce jam'iyyar PDP ta yi a cikin shekaru 16 da ta yi tana mulkin kasar. Ya kudiri niyyar gina abubawan more rayuwa kamar su tinutan mota da titunan jirgin kasa da filayen jiragen sama da makarantu da asibitoci da samar da wutar lantarki don dawo wa kasar da martabarta da tattalin arzikinta da ya rushe. Kwarewar Atiku Shi kuwa Atiku Abubakar, mutum ne da ke da wayewa kan harkokin kasuwanci a kasashen Amurka da yankin Turai da Asiya da Gabas Mai Nisa. Ana yi masa ganin mutum ne da ya yi fice wajen tsamo mutane masu basira a fannoni daban- daban, duk da cewa shi ba irin su ba ne. Kuma mutum ne da ya fahimci harkokin mulki da shugabanci, domin haka ne ya zagaye kansa da mutane masana al'amuran ci gaba a duniya baki daya. Mai yiwu ne Atiku Abubakar ya kasance irin shuganan da Najeriaya ke bukata a wannan yanayi da kasar ke ciki saboda kasancewarsa shugaba mai son kawo sauyin da zai tafi da zamani. Kalubalen da Atiku zai fuskanta Sai dai kuma wani babban kalubale da zai fuskanta shi ne kallon da ake yi masa a matsayin mutumin da ba ya kyamar cin hanci da rashawa, kuma zai iya amfani da matsayinsa na shugaban Kasa don azurta kansa. Tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo wanda Atikun ya yi wa mataimaki, ya bayyana shi a matsayin mutum mai son tara dukiya ta kowace hanya, kuma zai iya sayar da kasarsa don biyan bukatarsa. Masu nazarin harkokin siyasar Atiku Abubakar sun furta cewa wadandan zarge-zarge ne da ba su da tushe ko makama domin ba wata kotu ko hukumar bincike da ta same shi da wadannan laifuka da ake jibantawa da shi. 'Yan Najeriya masu kada kuri'a suna cikin wani hali na rudu kan wanda za su zaba a zaben shekara mai zuwa tsakanin wadannan mutane biyu da kowanensu ke da irin halayensa da nasarorinsa da kuma manufofinsa a kan kasar. Babban kalubalen da ke gaban Atiku Abubakar shi ne gabatarwa 'yan Najeriya da wani sabon tsari da ya sha bambam da wanda gwamnatocin PDP da suka wuce suka yi alkawari. Kalubalen da Buhari zai fuskanta a 2019 Shi kansa Shugaba Buharin yana da kalubalensa da zai iya hana shi cin zaben na shekarar badi. Daya daga cikinsu shi ne kyamar da yake nuna wa maganar gyaran tsarin kasar, wanda mutanen kudancin kasar da ma wasu da dama a arewacin su ke ganin babban al'amari ne. Akwai kuma batun yadda gwamnatinsa ta kasa shawo kan matsalolin tsaro, musamman kashe- kashen mutane da ake zargin kabilarsa ta Fulani da aikatawa, da garkuwa da mutane da ake yi a arewacin kasar inda nan ne mazabarsa. Duk da cewa gwamnatinsa ta samu wasu nasarori kan yaki da cin hanci da rashawa, akwai korafe-korafe masu tushe da ake yi kan wadansu mukarraban gwamnatinsa da ke da hannu tsamo- tsamo a batun cin-hanci da rashawa amma an ki a hukuntasu, al'amarin da ya sa mutane suka fara shakku kan yaki da cin hancin da gwsmnatin ta ce tana yi. Babban aikin da ke gaban gwamnatin Muhammadu Buhari shi ne sauya wannan tunanin na mutane ta hanyar daukar matakan da suka dace ba maganganun baka ba. Akwai alamun da ke nuna cewa shugaban ba zai dawo da wasu daga cikin mukarraban gwamnatinsa ba idan ya ci zaben, cikinsu har da shugaban ma'aikatan fadarsa wato Abba Kyari, wanda ya yi kaurin suna wajen katsalandan kan harkokin mulkin Shugaba Buharin. Kuma akwai zargin karbar cin hanci da ake yi masa wanda fadar gwamnatin ba ta musanta ba kuma ba ta bincika ba. Wadansu daga cikin ministocinsa su ma ana sa ran zai yi gaba da su saboda sun zame masa kadangaren bakin tulu. Ki-ki-ka-ka Jami'yyar APC wadda ke mulkin kasar tana ganin nasarar da Alhaji Atiku Abubakar ya samu a zaben fidda gwani na Jamiyyar PDP a matsayin wani jari da zai kawo masu nasara a zaben kasar mai zuwa. A cewarsu, ai ya yi an gani a zaben shekarar 2007 inda ya tsaya takara a karkashin tutar jam'iyyar ACN, amma kuri'un da ya samu ba su yi tasiri kan na marigayi Umaru Musa 'Yar Adua ba. Sannan kuma a zaben shekarar 2015 ya yi takarar zaben fidda gwani a karkashin jam'iyyar APC tare da Shugaba Muhamamdu Buhari amma bai kamo ko kafar Rabiu Musa Kwankaso ba wanda ya zo na biyu a takarar. 'Yan jam'iyyar ta APC suna ganin rinjayen da jam'iyyar ke da shi a Arewaci da Kudu-Maso- Yamma kawai ya isa ya ba Shugaba Buhari kuri'un da yake bukata ya cinye zaben na shugaban kasa. Amma magoya bayan Jamiyyar PDP ba su yarda da wannan hasashe ba, don a ganinsu ko a arewa masu jefa kuri'a da dama sun dawo rakiyar jam'iyyar ta APC saboda yadda ta gabatar da zabukan fitar da gwanaye na kwana-kwanan nan inda shugaban jam'iyyar ta kasa, Kwamred Adams Oshiomhole ya dinga ba wasu 'yan takara tikitin jeka-na-yi-ka ba tare da la'akari da tantancewar da aka yi tun farko

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Shin kunsan Kalubalen da ke gaban Buhari da Atiku Wajen cin zabe
Shin kunsan Kalubalen da ke gaban Buhari da Atiku Wajen cin zabe
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEiDIVOHBiovyMPxqoy28cow0c9Frp4uUZpMHbbTVfp2SKPBjsMOO5O6lx22e3cB90TeuWqoFHxKKxLnuOBAyYhX6gHxxELfXfOc49aQoOt-6gR9Qs0mxdKMdrzK9_H5iCgO4lktjmgB5lBg/s320/atiku-buhari2-702x336.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEiDIVOHBiovyMPxqoy28cow0c9Frp4uUZpMHbbTVfp2SKPBjsMOO5O6lx22e3cB90TeuWqoFHxKKxLnuOBAyYhX6gHxxELfXfOc49aQoOt-6gR9Qs0mxdKMdrzK9_H5iCgO4lktjmgB5lBg/s72-c/atiku-buhari2-702x336.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/shin-kunsan-kalubalen-da-ke-gaban.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/shin-kunsan-kalubalen-da-ke-gaban.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy