Blog Archive

Powered by Blogger.

Na fice daga jam'iyyar APC ne saboda gwamnoni sun fi karfin Buhari - Shehu Sani

Sanata Shehu Sani da ke wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya a jihar Kaduna ta Najeriya ya fice daga jam'iyyar APC mai mulkin jihar da kas...


Sanata Shehu Sani da ke wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya a jihar Kaduna ta Najeriya ya fice daga jam'iyyar APC mai mulkin jihar da kasar, yana mai cewa gwamnonin jam'iyyar sun fi karfin Shugaba Muhammadu Buhari. Sanatan ya gaya wa BBC cewa jam'iyyar wadda talakawa ke so da kauna ta kauce daga ainahin akidojinta ne saboda gwamnonin jihohin da take mulki sun yi mata kamun kazar-kuku, hatta shugaban kasar ma wanda dan jam'iyyar ne sun fi karfinshi a kanta. Sai dai kuma duk da cewa Sanatan bai samu tikitin sake takarar kujerar mazabar tasa ba a karkashin APC, ya tabbatar wa BBC cewa lalle zai yi takarar domin akwai jam'iyyun da suka riga suka tsayar da shi amma bai bayyana su ba, idan lokaci ya yi zai sanar in ji shi. Shehu Sani ya alakanta ficewar tasa da yadda aka gudanar da zabukan fitar da gwani na jam'iyyar a jihohi ta yadda sai abin da gwamnoni suka zaba ba jama'a ba shi ne uwar jam'iyyar ma a tarayya za ta amince da shi. Sanatan ya ce tun a baya ya yi yunkurin ficewa daga jam'iyyar lokacin sauran takwarorinsa 'yan majalisu da sauransu suna ficewa, amma uwar jam'iyyar ta dakatar da shi bisa alkawarin cewa za a daidaita al'amura, amma kuma a yanzu alkawarin ya zama yaudara. Dan majalisar dattawan yana da takaddama da reshen jam'iyyar na jiharsa wanda ke bin bayan gwamnatin jihar a game da tikitinsa na sake yin takarar kujerar a zaben 2019, inda jam'iyyar ta mika sunan mai ba wa gwamnan jihar Mallam Nasir El-Rufa'i shawara kan harkokin siyasa Mallam Uba Sani a matsayin dan takararta. Kafin hakan hedikwatar jam'iyyar da ke Abuja tun a baya ta sanar da cewa Shehu Sani shi kadai ne aka wanke da zai yi takarar kujerar, matakin da gwamnatin jihar da reshen jam'iyyar na jihar suka ki amincewa. Sanata Shehu Sani da gwamna El-Rufa'i daman kusan ba sa ga-maciji da juna tun bayan zabensu a shekara ta 2015, duk da cewa 'yan jam'iyya daya ne, ta yadda ma har sukan yi amfani da kalamai na batanci ga junansu.

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Na fice daga jam'iyyar APC ne saboda gwamnoni sun fi karfin Buhari - Shehu Sani
Na fice daga jam'iyyar APC ne saboda gwamnoni sun fi karfin Buhari - Shehu Sani
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEiLW0SHPpCy148YDBHs0qKk2KL2ewN2c43quONtjeI_9FkISHmxWH0Zl_NUXQWVX3Okcw6tMyyW4fePTjxIhnx7Rpny0BnWix6mrKv5hxquo5sKePEeslbaLJGgO_6t3KAk8qCsJqZjW6nE/s320/Shehu-Sani.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEiLW0SHPpCy148YDBHs0qKk2KL2ewN2c43quONtjeI_9FkISHmxWH0Zl_NUXQWVX3Okcw6tMyyW4fePTjxIhnx7Rpny0BnWix6mrKv5hxquo5sKePEeslbaLJGgO_6t3KAk8qCsJqZjW6nE/s72-c/Shehu-Sani.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/na-fice-daga-jam-apc-ne-saboda-gwamnoni.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/na-fice-daga-jam-apc-ne-saboda-gwamnoni.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy