Blog Archive

Powered by Blogger.

Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Na Taimakawa Kwakwalwar Jarirai Sosai

Wani sabon binciken da aka yi ya nuna cewar idan ana ba jariran da aka Haifa a wata na bakwai, wadanda ake ce ma Bakwaini, nonon uwa fiye da...


Wani sabon binciken da aka yi ya nuna cewar idan ana ba jariran da aka Haifa a wata na bakwai, wadanda ake ce ma Bakwaini, nonon uwa fiye da duk wani abinda za a basu, hakan zai taimaka masu wajen bunkasar kwakwalwarsu. Binciken da aka yi a jami’ar Edinburg an yi nazarin Magnetic Resonance Images na jarirai kusan 50 wadanda suke Bakwaini, wadanda kuma aka haife su kafin mako 33. An gwada kwakwalwarsu lokacin da suke ku san mako bakwai da haihuwa zuwa makonni 40 bayan da aka haife su. Amma amshi wasu bayanai danagane da yadda ake ciyar da su jariran lokacin dake kulawa dasu, ko dai ana basu madara ko kuma ko kuma nonon uwa ko kuma masu bada taimako. Jariran da suka samu shayarwa da nonon uwa a kalla sau uku na ko wacce rana, da suka yi a asibiti, hakan ya nuna an samu wani ci gaba dangane da kwakwalwarsu, idan aka yi la’akari data wasu. Binciken da masu ilmin kimiyya na kasar Scottish suka wallafa a mujallar Neuroimage, abin an kara da wasu binciken da aka yi, wanda kuma ya nuna cewar, shayar da yara nono, wata ingantttar hanya ce, da take taimakawa, da abin ya hada da ba su jariran da suka fi samun matsala wajen haduwa da ingantacciyar rayuwa. Jariran da aka Haifa kafin mako na 37 ana tsammanin sun fi kowa hanyar koyo da tunani wadda babu kyau, kamar manya saboda wata matsalar da aka samu wajen wani muhimmin wuri na kwakwalwa. Masana ilimin kimiyya sun gano ba jarirai bakwai ne nono yana taimakawa wajen samun matsalar da take samuwa wajen hada kwakwalwa. Farfesa James Boardman wanda shi ya yi bincike da kuma rubuta shi sakamakon, ya bayyana cewar, binciken da suka yi ya nuna, yadda girman kwakwalwa yake kasancewa, bayan dab aka haifi su jariran a matsayin bakwaini, abin ana samun ci gaba, amma fag a su jariran da suka samu shan nonon iyayensu mata. “Shi binciken ya nuna da akwai bukatar a sake yin wasu bincike binciken saboda a gane gudunmawar da saurin ba jariran da aka haifa bakwaini, ya dace a taimaka ma su iyaye mata na jariran da aka Haifa cikin wata na bakwai, yadda zasu samu damar shayar dasu nono, saboda yin hakan zai taimaka ma kwakwalwar su jariran ta kasance babu wata matsala. Kamar dai yadda Farfesa James Boardman ya bayyana. Farfesa Boardman ya bayyana cewar wannan zai ba su jariran dama ta kwakwalwarsu ta kasance cikin lafiya. Rahoton da aka samu wanda bai dade ba ya bayyana wasu bayanai masu gamsarwa dangane da, taimakawa da shayarwa ta nonon uwa take da ita. Koda ma kuwa ace jaririn da ya fi kankanta ne, ya kamata a fara masu da kasancewa cikin rayuwa mai kyau ta hanyar shayar da su nonon uwa. Kamar dai yadda Sarah Brown wadda shugaba ce kuma tana daga cikin amintattun Theirworld, wadanda suka taimaka wajen binciken. Ta kara bayyana wa da kuma mika godiyarta ga iyalan da suka bari jariransu suka kasance cikin shirin,` saboda an gane yadda za a bullo ma irin wannan al’amarin idan an samu irin shi a gaba. Kafin wannan lokacin da ake cikin na samun ita danar, akwai bincike binciken da kuma nazari wanda aka gabatar, wadanda suka nuna shayar da jariri nonon mahaifiyar shi, hakan yana taimaka ma shi, saboda yab kunshi wasu sinadarai da ake kira antibodies wadanda daga mahaifiyar ne suke, suna kuma taimaka ma su kwayoyin halittar jaririn wajen yaki da duk wata cuta ko kuma kwayar cuta sa zata nemi addabar shi jaririn. Da akwain alamun da suke jariran da aka shayar dasu nonon uwa suna samunn hazaka sosai wato ( IKs), zai yi kuma wuya su kamu da cuta mai sa kiba ko kuma babban tumbi ko kuma ciki, saboda ita madarar da take da formula tafi maiko ko kuma nau’in kitse cikinta. Shayar da jariri nonon uwa wannan ma wata hanya ce saboda tana samun hanyar kara shakuwa da abinda ta haifa, ta hakan dankon soyayya ke shiga tsakanin da da uwa.

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Na Taimakawa Kwakwalwar Jarirai Sosai
Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Na Taimakawa Kwakwalwar Jarirai Sosai
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjPHiMN5YWxH8QQoH-5bWxQOp9BMQt8GBR74QUZjkJlNaDTXAnFPCRzQoEKPe952k-LREmGW4PfCuOR7xBmjrx0AFZcAguO9w-jZuq8MvrGULmAqaKz0Zh6Mxf33UJgIms88MN17kYhuqzE/s320/97149712_gettyimages-471593802.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjPHiMN5YWxH8QQoH-5bWxQOp9BMQt8GBR74QUZjkJlNaDTXAnFPCRzQoEKPe952k-LREmGW4PfCuOR7xBmjrx0AFZcAguO9w-jZuq8MvrGULmAqaKz0Zh6Mxf33UJgIms88MN17kYhuqzE/s72-c/97149712_gettyimages-471593802.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/shayar-da-jarirai-nonon-uwa-na.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/shayar-da-jarirai-nonon-uwa-na.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy