Blog Archive

Powered by Blogger.

Shin kuna ganin Nijeriya Za Ta Iya Magance Cutar Maleriya Nan Da 2030?

Kamar yadda kwanakin baya duniyar ta gudanar da bukukuwan tunawa da ‘Yaki da cutar cizon sauro ta duniya’- wanda aka yiwa taken: a shirye mu...


Kamar yadda kwanakin baya duniyar ta gudanar da bukukuwan tunawa da ‘Yaki da cutar cizon sauro ta duniya’- wanda aka yiwa taken: a shirye muke wajen ganin bayan cutar maleriya. Furucin da masana ke kallon sa a matsayin wanda zai iya kai gaci idan Nijeriya ta cire siyasa a ciki. A cikin jawabin da ya gabatar, da yawun kamfanin harhada magunguna na ‘Nobartis’, Nana Boakye-Yiadom, kwararren masani ne tare da masaniya kan matakan da ya kamata ace Nijeriya ta bi domin ganin bayan wannan hattsabibiyar cuta, nan da shekarar 2030. ”Akwai shirye-shirye masu armashi da manufofin da aka karfafa su da bayanai, sai dai kash, sun samu tsgaron aiwatar war gwamnatin tsakiya”. Inji masanin. Haka zalika kuma, akwai ‘MalaFA’- cibiya ce mai gudanar da bincike, wadda kamfanin “Nobartis” ya kaddamar, a karkashin kulawar Mista Richard Kamwi, wakili na musamman da ke kula da tsarin yadda za a kawar da cutar a Kenya da jami’ar Odford, ta Burtaniya. Bugu da kari kuma, masu bayar da shawarwari a wannan binciken sun kunshi- shirin nan na “Roll Back Malaria”, “Malaria No More UK” da na “African Leaders Malaria Alliance”, suna daga cikin kwararrun da suke ankarar da cewa, akwai bukatar sake karfafa salon da Nijeriya ke amfani dashi ya yi daidai da wanda ake da bukata a wannan jan aikin. Ya bayar da misali da cewa, bisa ga kididigar rahoton shekarar 2017 wanda hukumar yaki da cutar maleriya ta duniya ta bayar, ya nuna cewa akwai matsalolin cutar maleriya da suka doshi miliyan 216 da aka samu a 2016, wanda ya haura wanda ake dashi a 2015- na miliyan 211. Har wa yau da yawan wadanda cutar maleriya ke kashewa da adadin su ya kai 445,000 a 2016, sabanin mutum 438,000 a 2015. Wanda kaso 90 na mutuwar yake ta’allake da cutar inda kuma ta fi shafar kananan yara yan kasa ga shekara 5 a duniya- a cikin kowadanne mintina biyu, maleriya ta na halaka yaro daya. Ya ce, fiye da shekaru biyar masu zuwa nan gaba, daga cikin shirin da kamfanin harhada magungunan ke yi shi ne zasu zuba jarin dalar Amurika sama da miliyan 100, wajen ayyukan bincike mai zurfi dangane da yadda za a tunkari cutar ga al’umma mai tasowa, tare da lalabo hanyoyin kariya da jure wa cutar cizon sauron. A hannu guda kuma, ya ce suna wannan fadi- tashin ne domin bayar da tasu gudumawa wajen cimma kudurorin kungiyar kula da lafiya ta duniya (WHO) a kokarin ta na dakile yadda take shafar kananan yara da yadda take jawo mutuwar yara- akalla kaso 90 cikin dari, a cikin kasashen Afrika da ke kan rairayin sahara, nan da 2030. “Har yanzu cutar maleriya ita ce kan gaba, a matsayin babbar kalubalen da ke ci ma jama’ar tuwo a kwarya a Nijeriya wanda kimanin kaso 76 cikin dari na yawan jama’ar kasar ke cikin hadarin ta. Ita tafi kowacce cuta lakume rayuka, kuma Nijeriya tana sahun gaba a yawan masu kamuwa da maleriya a fadin duniya- duk da ci gaban da mahukunta ke ikirarin sun samar, a yaki da cutar, amma a cikin kowadanne mintuna biyu maleriya tana halaka yara biyu”. Ya ce, Nijeriya tare da wasu kasashe uku da ke doron rairayin saharar Afrika, kamfanin ‘Nobartis’ ya shirya aiki kafada da kafada da wasu kungiyoyi wajen bayar da gudumawar fadada cibiyoyin bincike tare da fadakar da al’umma wajen lalubo hanyoyin yaki da cutar maleriya domin shawo kan matsalar yawan mace-macen kananan yara ta hanyar massasarar cizon sauro, cutar danshi da kwalara. Sakamakon binciken cibiyar “MalaFa” ya nusar da cewar, mahukunta a Nijeriya suna yiwa lamarin rikon sakainar kashi ta hanyar yin kwauro wajen fitar da kudin da ya dace domin yaki da cutar, inda shirin yaki da cutar maleriyar ya dogara ne kacokaf a kan kafafun tallafin da kungiyoyin bayar da tallafi ke bayar wa. Wanda ala-dole shirin yaki da cutar ke tafiyar hawainiya- a tsakanin ga koshi ga kwanan yunwa. “Sannan idan an yi la’akari da yadda cutar ke bijerewa magungunan da ake dasu yanzu, shima wata babbar barazana ce a ci gaban da ake son a samu a yaki da maleriya- kimanin shekaru 20 da suka wuce. Saboda wannan, ba zai yuwu mu nade hannu wuri guda mu jira ba ne, kuma wannan

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Shin kuna ganin Nijeriya Za Ta Iya Magance Cutar Maleriya Nan Da 2030?
Shin kuna ganin Nijeriya Za Ta Iya Magance Cutar Maleriya Nan Da 2030?
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhSWrcPvZkBK-ZTnrJNPhaFH8m_0-O2VqJkE5rGpoyO_cwE7SLzazSpIkM29UeMFQudVatWE8t6ktkz6OjcrD1dnmcq-MmDlj4rUpHjU-rCOvhOe95eh7Wom7oD9wrG_1_MyHeFoNCNIX7Q/s320/MALERIYA-A-NAJERIYA.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhSWrcPvZkBK-ZTnrJNPhaFH8m_0-O2VqJkE5rGpoyO_cwE7SLzazSpIkM29UeMFQudVatWE8t6ktkz6OjcrD1dnmcq-MmDlj4rUpHjU-rCOvhOe95eh7Wom7oD9wrG_1_MyHeFoNCNIX7Q/s72-c/MALERIYA-A-NAJERIYA.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/shin-kuna-ganin-nijeriya-za-ta-iya.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/shin-kuna-ganin-nijeriya-za-ta-iya.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy