Blog Archive

Powered by Blogger.

Shin da gaskene Obasanjo ya ce a zabi Buhari, kar a zabi Atiku a Zaben 2019?

Tun bayan da babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP ta tsayar da Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben 2019,...


Tun bayan da babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP ta tsayar da Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben 2019, jama'a suke ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu game da dan siyasar musamman a kafofin sada zumunta a kasar. Yayin da wadansu suke ganin tsohon mataimakin shugaban kasar zai iya doke Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC, wasu suna ganin hakan ba mai yiwu ba ne. Wannan batun shi ne abin da ya mamaye shafukan sada zumunta a Najeriya tun bayan da manyan jam'iyyun kasar biyu suka sanar da sunayen wadannan 'yan siyasan. Jama'a sun rika yada labarai musamman game da Alhaji Atiku Abubakar wadanda ba sahihai ba ne, ciki har da wadanda ake ikirarin cewa wai sun fito ne daga kafar yada labarai ta BBC. Da gaske ne Obasanjo ya ce a zabi Buhari, kuma kada a zabi Atiku a 2019? An rika yada labaran karya a kafofin sada zumunta inda ake cewa tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya bukaci 'yan kasar da su zabi Shugaba Buhari a zaben 2019, kuma Atiku ba zai taba yin shugabancin kasar ba. Atiku, wanda ya yi wa Obasanjo mataimakin shugaban kasa tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007, bai taba samun goyon bayansa ba a fafutikar da ya sha yi a baya na neman takarar shugabancin kasar. Kodayake Shugaba Buhari ya samu goyon bayan Mista Obasanjo a lokacin da ya lashe zaben 2015, amma daga bisani a bana, ya bayyana cewa ba ya goyon bayan tazarcen shugaban. BBC ba ta yi wata hira da Mista Obasanjo ba kan zaben 2019, hakazalika babu wani labari mai kama da wannan da kafar yada labaran ta ruwaito. Shin Atiku ya kai ziyara Amurka har ya gana da Trump? At last.... Atiku visits Washington via Social Media Airlines.hahaha Posted by Abubakar Sadiq on Wednesday, 10 October 2018 A wata hira da BBC ta yi da Alhaji Atiku Abubakar game da neman takararsa a zaben 2019 wanda aka yi da shi a ofishinmu na Landan a bana. Editan sashen Hausa Jimeh Saleh ya tambaye shi dalilin da ya hana shi zuwa kasar Amurka, inda Atikun ya ce bai san dalilin da ya sa kasar ta hana shi Biza ba . Shi ma wannan batun ya ba da wata kafa ta yada wasu labaran kanzon kurege a kafofin sada zumunta. An rika wallafa wani hoton boge a shafin sada zumunta inda ake ikirarin nuna dan siyasar yana gaisawa da Shugaba Donald Trump a gaban fadar White House bayan taron manema labarai. Ko jikar Atiku ta ce 'Sai Buhari'? Hakazalika an rika wallafa wani sakon boge wanda aka ce ya fito ne daga shafin Twitter na Alhaji Atiku, inda ake cewa wata jikarsa ta ce masa " Najeriya Sai Buhari" bayan da ya koma gida bayan kammala zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP. Wannan ma labarin kanzon kurege ne don shafin da ya wallafa wannan sako a Twitter ba na dan siyasar ba ne. Atiku ya wallafa wannan sakon: "A karshe na koma gida bayan zaben fidda gwani. Jikata ta yi mun maraba. Kuma yanzu ina kewaya gidan da ita rike da balan-balan (mai dauke da rubutun) Sai Atiku a 2019," in ji shi. Bambancin shafin bogen da sahihin shafin Atiku Abubakar Sunan shafin @The_Atiku, maimakon nasa na aihini mai suna @atiku An bude shi ne a watan Oktobar shekarar 2018, dan siyasar ya bude na shi shafin ne a shekarar 2010 Yana da mabiya 261 ne kawai, maimakon mabiya miliyan daya da rabi da sahihin shafin dan siyasar yake da su. Menene labaran karya? Sun kunshi bayanai na karya da hotuna da na bidiyo da ake kirkira a yada domin a harzuka mutane. Ko kuma yada tsoffin hotuna, ko hotunan da ba ma a kasar aka dauka ba. Irin wadannan labaran karyar da kuma hotunan karyar da ake yadawa, na taimaka wa wajen rura rikici musamman a tsakanin kabilu. A wasu lokuta rashin samun bayanai daga bangaren gwamnati ko mutanen da abin ya shafa, na haifar da yada jita-jita da kuma zaman dar- dar. Obasanjo bai isa ya hana ni komai ba - Atiku Abubakar Yadda labaran karya ke ruruta rikicin makiyaya da manoma Hanyar gane labaran karya da ake yadawa a intanet Irin wadannan labaran karya kan haifar da illoli masu yawa, kamar tayar da fitina, da kulla kiyayya tsakanin al'umma da kuma yada bayanan da ba su da tushe. Binciken da BBC ta yi a kw

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Shin da gaskene Obasanjo ya ce a zabi Buhari, kar a zabi Atiku a Zaben 2019?
Shin da gaskene Obasanjo ya ce a zabi Buhari, kar a zabi Atiku a Zaben 2019?
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjEvVu2E2IgTu2bKG58Bqf7Q66811O6R8Bb9QlrKddiOoNX6v-AfpyqZs72LHxDiD1RICG-vQbHon_ZnLm5k9U8EsLakey2ts6HNqSbwuD61whCkP9E1p_D2zVsNw_8ud97hyphenhyphengMJKEbD7lP/s320/_103764616_aaa-1.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjEvVu2E2IgTu2bKG58Bqf7Q66811O6R8Bb9QlrKddiOoNX6v-AfpyqZs72LHxDiD1RICG-vQbHon_ZnLm5k9U8EsLakey2ts6HNqSbwuD61whCkP9E1p_D2zVsNw_8ud97hyphenhyphengMJKEbD7lP/s72-c/_103764616_aaa-1.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/shin-da-gaskene-obasanjo-ya-ce-zabi.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/shin-da-gaskene-obasanjo-ya-ce-zabi.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy