Blog Archive

Powered by Blogger.

Majalissa Za Ta Tursasawa Shugaba Buhari Don Ya Sa Hannu Kan Dokar Fetur Ta PIGB

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya ce, Majalisar za ta ci gaba da matsawa Shugaban kasa domin samun sa hannun shi a kan dokar sash...


Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya ce, Majalisar za ta ci gaba da matsawa Shugaban kasa domin samun sa hannun shi a kan dokar sashen man fetur. Saraki ya yi wannan kalamin ne a wajen liyafar cin abincin dare wanda aka shirya a matsayin wani sashe na taro na 24 kan tattalin arzikin Nijeriya a Abuja ranar Litinin. Liyafar wacce ta kare a can cikin dare, masana a harkar kasuwanci, ma’aikatu, kananan ‘yan kasuwa da masana a sashen kudi da sauran manyan mutane ne suka halarce ta. A cewar Saraki, shawarar da ‘yan majalisar suka yanke ta yin matsin lamba ga Shugaban kasa domin ya sanya hannu a kan dokar ya zama tilas ne, domin samun habaka sashen na mai da iskar gas a Nijeriya. Shugaba Buhari ya ki sa hannu a kan dokar ta PIGB ne bayan da majalisar ta zartar da ita. Shugaban ya bayar da dalilai na kin sanya hannun na shi ne a bisa dalilai na tsarin mulki da shari’a. Shugaban majalisar ya ce, “Wannan dokar a lokacin da muka fara tattaunawa a kanta, mutane da yawa sun dauka ba za mu iya ba, amma sai muka nu na karfin ikon da muke da shi a Majalisa wajen kafa ta. “Mun kafa dokar, yanzun tana hannun Shugaban kasa ne. “Amma abin takaici, watannin masu yawa da mika dokar sai ga shi yanzun an dawo mana da ita ana tuhumar wasu kananan abubuwan da ba su wuce a magance su ba a cikin yini guda. “Manufarmu ita ce, mu koma mu zauna tare da sashen Shugaban kasa domin amfanar ‘yan Nijeriya. “Wannan kyakkyawar doka ce, kamar yanda masana da ma’aikata a sashen suka yaba mata. Ya ce, matsalolin da aka hanga a cikin dokar ba su kai ga a ce an ki sanya hannu a a kan dokar ba, saboda matukar mahimmancin da dokar ke da shi a fannin zuba jari. “Saboda kamar yanda ku ka sani ne, ba wani mahimmin jarin da ake zubawa a sashen na man fetur da iskar gas, domin mutane ba su da tabbacin ribar da za su samu.

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Majalissa Za Ta Tursasawa Shugaba Buhari Don Ya Sa Hannu Kan Dokar Fetur Ta PIGB
Majalissa Za Ta Tursasawa Shugaba Buhari Don Ya Sa Hannu Kan Dokar Fetur Ta PIGB
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhcVDyekVnEjsO6VlBAip9PP36MsZgmesZY7Q_175EIFYY1g_gaCN70DP4zpm5N8_dXDIoemq8j8YjXMowN9qwa_4tLRSXFS-RQIWdQ_nXpOdm9YogPwVGVG2nZEMnGEFB34BeK9ls00QA0/s320/Page-5-first-story-Buhari.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhcVDyekVnEjsO6VlBAip9PP36MsZgmesZY7Q_175EIFYY1g_gaCN70DP4zpm5N8_dXDIoemq8j8YjXMowN9qwa_4tLRSXFS-RQIWdQ_nXpOdm9YogPwVGVG2nZEMnGEFB34BeK9ls00QA0/s72-c/Page-5-first-story-Buhari.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/majalissa-za-ta-tursasawa-shugaba.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/majalissa-za-ta-tursasawa-shugaba.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy