Blog Archive

Powered by Blogger.

Wata Matar ta kashe kanta da 'ya'yanta saboda mutuwar karen mijinta

Wani mutum wanda matarsa ta kashe kanta tare da 'ya'yanta bayan da aka yi zargin cewa ya kitsa mutuwarsa da gangan saboda a biya shi...


Wani mutum wanda matarsa ta kashe kanta tare da 'ya'yanta bayan da aka yi zargin cewa ya kitsa mutuwarsa da gangan saboda a biya shi kudin inshora, ya mika kansa ga 'yan sanda a kasar China. An zaci mutumin mai shekara 34 ya mutu ne bayan da aka gano motarsa a kogi, duk da cewa dai ba a ga gawarsa ba. Bai gaya wa matarsa shirinsa na mutuwar karyar ba, don haka ta yi amanna cewa ya mutu. Daga bisani sai ta fada cikin kududdufi tare da 'ya'yanta bayan da ta wallafa sakon cewa za ta kashe kanta a intanet. Mutumin, wanda 'yan sanda suka ce sunansa He, ya mika kansa ga 'yan sandan ne a gundumar Xinhua a makon da ya gabata. A wata sanarwa da 'yan sanda Xinhua suka fitar a kafar WeChat sun ce an tsare shi kan tuhumar zambar inshora da kuma lalata dukiya ta kasa da kasa. A farkon watan Satumba ne Mista He ya sayi tsarin inshora kan kudi dala 145,000 ba tare da sanin matarsa ba, a cewar 'yan sanda. A cewar wani rahoto da gidan rediyon gwamnatin China ya fitar, sunan matarsa ya sa a matsayin wacce za ta ci gajiyar inshorar. 'Yan sanda sun ce a ranar 19 ga watan Satumba, Mista He ya yi amfani da wata mota da ya ara don shirya yadda mutuwar karyar tasa za ta kasance. An gano cewa ana bin sa bashin kudin kasar yuan 100,000. A ranar 11 ga watan Oktoba ne kuma aka gano gawar matar tasa mai shekara 31 da dansu mai shekara hudu da kuma 'yarsu mai shekara uku a wani kududdufi kusa da gidansu, a cewar gidan rediyon Muryar China. A wani sako da ta wallafa a WeChat, ta rubuta cewa ga ta nan za ta bi bayan mijinta, inda ta kara da cewa "yanzu na kara jin ina so mu kasance tare a matsayin iyalai mu hudu har abada." A washe garin ranar ne Mista He ya mika kansa ga 'yan sanda. Tun da fari dai ya wallafa a shafinsa na bidiyo, wanda daga baya aka yi ta yadawa, inda yake kuka yana cewa ya ranci kudi don ya biya kudin maganin 'yarsa, wacce ke fama da farfadiya. An yi ta yayata zancen a kafafen sada zumunta na China a makon da ya gabata, inda ya jawo ce-ce- ku-ce kan yadda iyalai ke fama da matsalar rashin kudi da nauyin iyali. An yi ta amfani da maudu'in #ManFakesDeathLeadingtoWifesDeath sau kusan miliyan 29 a kafar intanet ta Weibo.

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Wata Matar ta kashe kanta da 'ya'yanta saboda mutuwar karen mijinta
Wata Matar ta kashe kanta da 'ya'yanta saboda mutuwar karen mijinta
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjCnWZl4Ew6tNGwSSWHS-Y2BthEWV-UgfUlNWJGbauzXz628OrKhuSr9dikLUZWKPG6fUE4lOfrpkBnzvh0NNUOx861o0_HymOH3V3kkZ0-DDE_bVunNE1w51WaIvklnI9JyvPTu7UzHDgk/s320/_103897151_blurredweibopic.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjCnWZl4Ew6tNGwSSWHS-Y2BthEWV-UgfUlNWJGbauzXz628OrKhuSr9dikLUZWKPG6fUE4lOfrpkBnzvh0NNUOx861o0_HymOH3V3kkZ0-DDE_bVunNE1w51WaIvklnI9JyvPTu7UzHDgk/s72-c/_103897151_blurredweibopic.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/wata-matar-ta-kashe-kanta-da-saboda.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/wata-matar-ta-kashe-kanta-da-saboda.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy