Blog Archive

Powered by Blogger.

Oby Ezekwesili zata kara da Shugaba Buhari a zaben 2019

An faro shirye-shiryen zaben shugabancin Najeriya ne da tunanin cewa fitattun 'yan siyasa maza ne za su fafata, amma fitowar Oby Ezekwes...


An faro shirye-shiryen zaben shugabancin Najeriya ne da tunanin cewa fitattun 'yan siyasa maza ne za su fafata, amma fitowar Oby Ezekwesili ya sauya wannan tunanin. A baya, mata sun sha tsayawa takara, amma ita ce mafi shahara da ta kalubalanci kujerar shugaban kasar, a cewar wakilin BBC Chris Ewokor. Misis Ezekwesili ta yi suna wajen jagorantar kamfe din nan na ceto 'yan matan Chibok wato #BringBackOurGirls wanda ke fafutukar ganin an ceto 'yan mata 276 daga makarantar 'yan mata ta garin Chibok da ke arewacin Najeriya a shekarar 2014. Ta kuma taba rike mukamin ministar ilimi da kuma mataimakiyar shugaban Babban Bankin Duniya. Sai dai babban kalubalenta a zaben da za a yi a watan Fabrairu shi ne doke shugaba mai ci Muhammadu Buhari mai shekara 75 ko kuma doke dan takara a babbar jam'iyyar adawa, Atiku Abubakar mai shekara 72 wadanda suke da magoya baya sosai. Wa'adin rajistar tsayawa takarar ya cika ne da karfe sha biyu na dare agogon Najeriya ranar Lahadi, kuma a kalla 'yan takara tara ne a ke zaton sun mika takardunsu. A karshen makon da ya gabata, jam'iyyar APC ta tsayar da Shugaba Buhari kuma Atiku Abubakar ya buge mutum 11 a zaben fitar da gwani na jam'iyyar PDP. Jam'iyyun biyu dai sun samar da duka shugabannin Najeriya tun bayan kawo karshen mulkin soja a shekarar 1999. Mene ne sakon Oby Ezekwesili? Ga Misis Ezekwesili, mazan da za ta fuskanta a zabensu na "wani rukuni ne na 'yan siyasa da ke walagigi daga wani rikici zuwa wani", kamar yadda ta bayyana a wani taron jam'iyyar Allied Congress Party of Nigeria (ACPN), inda aka tsayar da ita. Tana shirin fitowa a matsayin 'yar takara mai adawa da masu rike da madafun iko, inda ta kira 'yan siyasar da ke rike da kasar masu dagula al'amurra. Kuma a wani yunkuri irin na tsohon shugaban Amurka Barack Obama, jam'iyyar ACPN na yi mata lakabi da 'yar takara mai cike da "buri". Misis Ezekwesili, mai shekara 55 na kokarin kyautatawa matasan kasar, inda ta ce mutanen da ke rike da madafun iko ba su fahimci sauye- sauyen da ke faruwa ba, musamman a fannin fasaha. Fiye da kashi 50 cikin 100 na 'yan Najeriya ba su kai shekara 30 ba. "Ya za a yi a ce kasar da ke da yalwar miliyoyin matasa, masu jini a jika, da fasaha ta saki jiki?" Ta tambaya. Za ta iya rusa zaben? Sharhi daga Wakilin BBC Chris Ewokor Baya ga tsayawa matsan Najeriya, Misis Ezekwesili ta karbu a wajen mata, kuma shahararta a kasar da girmama ta da ake yi a kasashen waje na iya kara mata tagomashi. Kuma ta fito ne daga kudancin Najeriya, yayin da wadancan mazan da za ta fafata da su 'yan arewa ne, don haka wannan na iya ba ta damar samun kuri'u daga 'yan kudu da ke so 'yarsu ta shugabanci kasar. Misis Ezekwesili na iya samun goyon baya sosai, kuma tana iya tsoratar da jam'iyyun APC da PDP, amma ikon da jam'iyyun suka kafa zai yi wuyar tumbukewa. 'Yan kasar da yawa na rayuwa ne cikin yunwa kuma suna fuskantar matsin tattalin arziki, don haka suna iya harzuka har su mara wa wasu jam'iyyun da za su iya jan hankalinsu da kudi don su zabe su. APC da PDP na da magoya baya a fadin kasar da kuma kudi masu yawan gaske. Don haka ne jam'iyyarta ta bude wani asusu da zai tallafawa yakin neman zabenta, sannan kuma ta gina kanta, amma babu tabbas din hakan zai isa. Me Atiku ke cewa? Ya wallafa a shafinsa na Twitter bayan da ya ci zaben fitar da gwani cewa "Yanzu za a fara aikin gyara Najeriya" Mista Abubakar dai babban dan kasuwa ne kuma mai fada-a-ji a fagen siyasa wanda ya yi yaki kan jiki kan karfi ya doke masu neman kujerar ciki har da Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki, wajen lashe zaben fitar da gwanin. Ya rike mukamin mataimakin shugaban Najeriya daga 1999 zuwa 2007 kuma ya sha yunkurin tsayawa takarar shugaban kasar, amma sau daya ya taba cin zaben fitar da gwani a babbar jami'iyya. Ya tsaya takara a jam'iyyar AC, wacce aka kafa kafin jam'iyyar APC, kuma ya fafata da marigayi Umaru 'Yar'Adua na jam'miyyar PDP da Muhammadu Buhari a 2007. Atiku ya samu kashi 7.5 cikin dari na kuri'un amma ya yi korafin an yi magudi

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Oby Ezekwesili zata kara da Shugaba Buhari a zaben 2019
Oby Ezekwesili zata kara da Shugaba Buhari a zaben 2019
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEi-1qr78McfX2GTF8XqCZR6uM5o1ocx14ORDXbe9gH0LEczpO6HqTnn3LJQS8vuKHrXrtkwwI9QojsgLqrsU2kHsd2pjZ9cODlaubj9xjHQnKhI52H67LlDV4c12kOzx8LRsW8_xY-5Mrz9/s320/20181010_060516-BlendCollage.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEi-1qr78McfX2GTF8XqCZR6uM5o1ocx14ORDXbe9gH0LEczpO6HqTnn3LJQS8vuKHrXrtkwwI9QojsgLqrsU2kHsd2pjZ9cODlaubj9xjHQnKhI52H67LlDV4c12kOzx8LRsW8_xY-5Mrz9/s72-c/20181010_060516-BlendCollage.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/oby-ezekwesili-zata-kara-da-shugaba.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/oby-ezekwesili-zata-kara-da-shugaba.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy