Blog Archive

Powered by Blogger.

Wai me Obasanjo ke tsoro da gwamnatin Shugaba Buhari ne

Kusan za a iya cewa a yanzu Tsohon Shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo na kan gaba a sahun mutanen da ke adawa da gwamnatin Muhammadu Bu...


Kusan za a iya cewa a yanzu Tsohon Shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo na kan gaba a sahun mutanen da ke adawa da gwamnatin Muhammadu Buhari, kuma suke kokarin ganin bayanta. Sai dai wasu na sanya almar tambaya kan ainahin manufar tsohon shugaban. A 'yan makonnin da suka wuce ne Obasanjo ya kai ziyara ga shugabannin kungiyar Yarbawa ta Afenifere domin duba yadda "za a sauya gwamnatin Shugaba Buhari, wacce ya ce tana neman jefa kasar cikin wani hali na tsaka mai wuya". Sai dai ganin yadda ziyarar ta zo a lokacin da ake ci gaba da takun-saka tsakanin tsohon shugaban da kuma gwamnatin APC, wasu na ganin akwai lauje a cikin nadi. Amma Obasanjo, wanda ya goyi bayan Buhari a zaben 2015, ya nuna ba shi da abin da za a zarge shi da shi, illa dai ziyarar ta neman ceton kasar ce. Kalaman da Buhari ya yi na shagube a kan yadda aka kashe makudan kudade kan wutar lantarki a lokacin mulkin Obasanjo "ba tare da an gani a kasa ba" sun sa wasu na hasashen cewa shugaban na da niyyar daukar mataki kan lamarin. Kwatsam kuma ana cikin haka, sai Obasanjo ya fitar da sanarwa yana zargin cewa gwamnati na shirin amfani da shaidun boge domin kama shi da shafa masa laifi ta karfi da yaji. Sai dai gwamnatin ta hannun ministan sadarwa Lai Mohammed, ta ce mai kashi a gindi ne kawai zai tsorata, kuma shi mara gaskiya ko a ruwa gumi yake yi.Tsohon shugaban ya dade yana takun saka da kungiyar ta Afenifere, kuma daga dukkan alamu akwai babban kalubale a gabansa na ganin ya shawo kanta domin cimma manufarsa. Wani mai sharhi kan al'amuran siyasa kuma mamba a kngiyar wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida min cewa ba za su saki jiki da Mr Obasanjo ba. "Duk da cewa muna da matsalolinmu da gwamnatin Buhari, ba mu san manufar Obasanjo ba kuma ba za mu saki jiki da shi ba tukunna," a cewarsa. Me Obasanjo ke tsoro? Wasu majiyoyi kuma sun yi zargin cewa Obasanjo na kamun kafa ne ga kungiyar domin ta mara masa baya idan har Shugaba Buhari ya yanke shawarar bincikar gwamnatinsa kamar yadda wasu kungiyoyi ke kiran da aka yi. Kuma ba za a iya watsi da masu wannan ra'ayi ba ganin kalaman Obasanjo na baya-bayan nan ka cewa ana shirin kama shi, duk da cewa babu wata hujja mai kwari da ya bayar. Wannan ne ya sa wasu ke zargin cewa Obasanjo na tsoron matakin da Buhari ka iya dauka a kansa ko kuma kan wasu matakai da gwamnatin ta dauka a baya, shi ya sa yake kokarin ganin bayan gwamnatin. Sai dai shi mutum ne da ya yi kaurin suna wurin juyawa gwamnatoci baya kamar yadda ya yi wa marigayi Umaru 'Yar'adua da kuma Goodluck Jonathan. Kuma ya nace cewa yana gwagwarmaya ne domin ganin an ceto kasar, saboda a cewarsa Buhari ya gaza ta fannoni da dama. Sai dai gwamantin ta ce badakalar da Obasanjo da sauran gwamnatocin PDP suka yi ne suke kokarin gyarawa, kuma kawo yanzu an fara samun ci gaba. Kawo yanzu dai 'yan kasar na zuba ido su ga yadda wannan lamari zai kaya. Ko Obasanjo zai yi nasara wurin ganin karshen gwamnatin Buhari, ko kuma jam'iyyar APC za ta yi galaba wurin karya tasirin tsohon shugaban a siyasance. Kuma ko abin da Obasanjo ke tsoro zai faru ganin yadda Buhari ya sha alwashin yakar cin hanci da rashawa, duk da cewa wasu na ganin binciken Obasanjo kamar wani abu ne da shugaban ba zai so ya yi ba?

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Wai me Obasanjo ke tsoro da gwamnatin Shugaba Buhari ne
Wai me Obasanjo ke tsoro da gwamnatin Shugaba Buhari ne
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgYGLGf04KCF3FHPanTwKO1iZU_qwJiwqnsUWArc61jgaRgBcYXB6V_ej-sHjwZDgk7ApyZj6M7gRkVybDR4g0qAGQV0Dgf9TpprTatR9k3ETlF1GCFJl0AAtKFxVjIeyH1VwO_KEKXM_K0/s320/obasanjo-n-buhari.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgYGLGf04KCF3FHPanTwKO1iZU_qwJiwqnsUWArc61jgaRgBcYXB6V_ej-sHjwZDgk7ApyZj6M7gRkVybDR4g0qAGQV0Dgf9TpprTatR9k3ETlF1GCFJl0AAtKFxVjIeyH1VwO_KEKXM_K0/s72-c/obasanjo-n-buhari.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/wai-me-obasanjo-ke-tsoro-da-gwamnatin.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/wai-me-obasanjo-ke-tsoro-da-gwamnatin.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy