Blog Archive

Powered by Blogger.

Nifa Sulhunta Atiku da Obasanjo na je yi — inji Sheikh Gumi

Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, daya daga cikin malaman addinan da suka shaida sasantawar tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma dan takarar shu...


Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, daya daga cikin malaman addinan da suka shaida sasantawar tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma dan takarar shugaban kasar a jam'iyyar PDP a zaben 2019 wato Atiku Abubakar da kuma tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo, ya yi karin haske a game da sasantawar da suka halarta. Sheikh Gumi, ya shaida wa BBC cewa, shi dai an gayyace shi ne domin ya zama shaida a sulhun da aka yi tsakanin Atiku Abubakar da kuma Obasanjo. Malamin addinin Islaman, ya ce an zabe su su je sulhun ne saboda ana neman mutanen da ba ruwansu da bangaranci addini kawai suka sanya gaba, shi ya sa yakasance daya daga cikin masu sulhun. Sheikh Gumi ya ce, sun zama shaida a sulhun da aka yi ne, bisa la'akari da cewa duk wani abu da zai kawo sulhu a addinin musulunci, abu ne wanda aka kwadaitar da shi a yi shi. Malamin addinin Islaman, ya kuma yi karin haske a kan zargin da ake cewa ko suna nuna goyon bayansu ne ga takarar Atiku Abubakar, inda ya ce ' Ba a Atiku Abubakar ba, ko wanene koda a misali shugaba Muhammadu Buhari zai fito ya ce zai yi sulhu da kanal sambo Dasuki da aka kulle, a nemi ni a ce na zo nayi sulhi, to zan yi'. Sheikh Gumi ya kuma bayyana irin alfanun da ya ke ganin wannan sulhu na su Atiku da Obasanjo zai yi, inda ya ce abu na farko akwai rikici a kasar nan, yawanci kowa a cikin manyan kasar na ganin an cuce shi,to a irin hakan an bukatar yafiya don shi kasa ke bukata. Malamin addinin ya ce, shi fa a bangarensa ba ya goyon kowa a takarar shugabancin kasa, domin ko iyalansa ma ba zai ce musu ga wanda za su zaba ba, don haka shi ba shi da zabi, kuma kowa na da na sa zabin. Ga masu sha'awa, sai ku latsa alamar lasifika a hoton da ke kasa domin sauraron yadda hirar BBC da Dr Ahmad Gumin ta kasance: Matashiya A ranar Alhamis ne Atiku Abubakar ya bayyana cewa ya gana da tsohon mai gidansa Cif Olusegun Obasanjo kuma sun ci abincin rana tare a garin Abeokuta na jihar Ogun. Atiku Abubakar ne ya yi wa Olusegun Obasanjo mataimaki lokacin da yake shugaban najeriya tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007. Tun bayan nan, dangantakar da ke tsakaninsu ta yi tsami kuma Obasanjo bai taba goyon bayan Atiku Abubakar ba a duk lokutan da ya fito a baya na nuna son yin shugabancin Najeriya. An taba ruwaito Obasanjo yana cewa "zai yi iya bakin kokarinsa don ganin Atiku Abubakar bai shugabanci Najeriya ba." Sai dai a wata hira da BBC ta yi da Atiku Abubakar, ya ce "Obasanjo ba shi ne Allah ba, kuma ba shi ne mutanen Najeriya ba." Olusegun Obasanjo dai na daya daga cikin masu fada a ji a fagen siyasar Najeriya. Kuma ya nuna goyon bayansa ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a lokacin da ya lashe zaben 2015, sai dai a bana ya ce ba ya goyon bayan shugaban ya nemi wa'adi na biyu a zaben shekarar 2019.

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Nifa Sulhunta Atiku da Obasanjo na je yi — inji Sheikh Gumi
Nifa Sulhunta Atiku da Obasanjo na je yi — inji Sheikh Gumi
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEi8kfcRuO4pIslaV5FYs_DJ0pcqEB7OZO45OH2gbIgsAnpuCHd18cUis0tXCAN-MgQmpySqNTApiiX-nnzSvBcvkJnPrBcDFApCWWXQ6iaF12mZh3EEEf982JsYjCQbmwhfLeyrVTW3ZiEr/s320/_103846244_c73adf52-50d7-448c-8d56-fbc0636b97d4.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEi8kfcRuO4pIslaV5FYs_DJ0pcqEB7OZO45OH2gbIgsAnpuCHd18cUis0tXCAN-MgQmpySqNTApiiX-nnzSvBcvkJnPrBcDFApCWWXQ6iaF12mZh3EEEf982JsYjCQbmwhfLeyrVTW3ZiEr/s72-c/_103846244_c73adf52-50d7-448c-8d56-fbc0636b97d4.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/nifa-sulhunta-atiku-da-obasanjo-na-je.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/nifa-sulhunta-atiku-da-obasanjo-na-je.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy