Blog Archive

Powered by Blogger.

Tambuwal Ne yafi cancanta da Shugabancin Nijeriya - inji Hon. Bashire

HON. ABUBAKAR ZAKI BASHIRE shi ne Sakataren Jam’iyyar APC na Jihar Sakkwato kafin Gwamna Tambuwal ya canza sheka zuwa PDP a watan Agusta. Ts...


HON. ABUBAKAR ZAKI BASHIRE shi ne Sakataren Jam’iyyar APC na Jihar Sakkwato kafin Gwamna Tambuwal ya canza sheka zuwa PDP a watan Agusta. Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Tambuwal kuma fitaccen dan siyasa, babban jigo ne a gidan siyasar Tambuwal wanda ke fadi tashin samun nasarar Mutawallen na Sakkwato a matsayin Shugaban Tarayyar Nijeriya a zaben da ke tafe. A wannan tattaunawar da ya yi da LEADERSHIP A Yau; Bashire ya bayyana Gwamnan na Sakkwato a matsayin wanda ke kan hanyar lashe zaben fitar da gwani kuma mafi cancantar Shugabancin Al’ummar Nijeriya sama da milyan 180 kamar yadda ya bayyanawa wakilinmu SHARFADDEEN SIDI UMAR DOGON-DAJI . Honarabul a matsayin ka na babban jigo a jam’iyyar PDP mene ne kake gani a matsayin kashin bayan Gwamna Tambuwal na neman kujerar Shugabancin Kasa a zaben 2019? A bayyane yake cewar duk wanda ya kwana ya tashi a kasar nan ya san cewar al’amurra ba su tafiya yadda ya kamata domin jiya da yau ta lalace har ta na kokarin shayar da gobe. Idan ka dauki sha’anin tsaro da bangaren tattalin arziki a matsayin misali za ka ga al’amurran sun fita hayyacin su haka ma fannonin ilimi, samarwa matasa ayyukan yi da koma baya a aikin gona duka muhimman abubuwa ne da suka yi bahaguwar tabarbarewar da ake neman agajin gaggawa. Shi kansa Mai Girma Gwamna a mabambantan jawabansa ka na jin yadda yake bayyana kasawar Gwamnatin Tarayya wajen sauke nauyin da al’umma suka dora mata ta yadda al’ummar kasa kullum kuka suke yi suna kara kokawa da karuwar yunwa da fatara da talauci da dimbin tarin matsalolin da suka hadu suka yi wa kasar nan dabaibayi suka hana mata ci-gaba ciki kuwa har da zaman hanyoyin kasar nan a matsayin tarkon mutuwa, koma baya a harkar kasuwanci, kauracewa masu shigowa domin su zuba jari saboda kalubalen tsaro da rashin wadatacciyar wutar lantarki, durkushewar masana’antu, ko- oho da tarin ma’adinan da muke da su, rashin martaba aikin Gwamnati da aiwatar da shugabanci iri na ‘yan Mowa da ‘yan Bora da dai sauran matsalolin da suka zarce shurin masaki wadanda a kan wannan ya hanga ya hango dacewar fitowa domin bayar da tashi gudunmuwa wajen bunkasa Nijeriya tare da dawowa da ita a saman turba mai kyau. Amma akwai mutane da dama da ke da ra’ayin Tambuwal ya yi sauri wajen fitowa takarar Shugabancin Kasa musamman ganin cewar matashi ne wanda kuma ke a kan wa’adin mulki na farko a matsayin Gwamna? Amintacce kuma gogaggen dan siyasar da ya samu nasarar zama kan kujera mafi daraja ta hudu a kasar nan a tsayin shekaru hudu a 2011 wanda kuma ya zama Gwamna a 2015 ba za a ce ya yi gaggawar neman zama Shugaban Kasa a 2019 ba. Nijeriyar mu a yau ta na bukatar matashin shugaba, jajirtacce mai jini a jika wanda zai jagoranci kasa da ‘yan kasa zuwa ga tudun mun tsira irin ko kamar Mai Girma Gwamna Aminu Waziri Tambuwal. Shugaba ne wanda Nijeriya take a tafin hannun sa don haka ya san matsalolin kasa da na ‘yan kasa ya kuma san hanyoyi da dabarun samar da canji mai ma’ana, hanyoyin kawar da matsalolin al’umma da hanyoyin inganta jin dadin su. Yaya kake ganin zaben fitar da gwani da za a gudanar kwanan nan zai kasance tsakanin Tambuwal da ‘yan takara sama da goma? Daga cikin dukkanin ‘yan takarar PDP Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ne mafi dacewa da cancantar mulkin kasar nan don haka yana da kyau wakilai masu zaben fitar da gwani su yi zabe bisa ga cancanta, kishi da hangen nesa. Kar ka manta Tambuwal dan siyasa ne wanda siyasarsa a jiya da yau ta yi dai-dai da siyasar akida ta son ci-gaba da bukasar al’umma don haka wajibi ne wakilai masu zabe su yi wa kansu karatun ta natsu su zabi dan takarar da jama’a ke so wanda aka tabbatar yana iyawa wanda kuma ake da tabbacin samun nasararsa musamman fitowarsa daga yankin Arewa-Maso- Yamma zai taimaka masa matuka kwarai wajen nunawa Shugaba Muhammadu Buhari kofar fita daga Fadar Mulki. Wata babbar damar da ke ga Tambuwal ita ce matashi ne mai jini a jika, mai kishi, tunani da hangen nesa wanda ya samu nasarar a dukkanin mukaman da ya rike. Don haka muna da tabbacin Nijeriya a tafin hannun sa zai jagoranci kakkabe ayyukan ta’addanci ta hanyar samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, habaka tattalin arzikin kasa da gudanar da muhimman ayyukan raya kasa da ci-gaban al’umma a karkashin shugabancin gaskiya a tafarkin gaskiya. Ra’ayin wasu akai shi ne anya Tambuwal zai iya kuwa musamman ganin Muhammadu Buhari ma ya kasa? Kasawar wani ba za ta taba zama hujjar ganin wani ba zai iya ba domin shugabanci lamari ne da ke bukatar jajircewa, sadaukai da kai, aiki tukuru da bayar da kulawar musamman ga kowace irin matsala ko bukatar al’ummar kasa wanda kuma ga duk wanda ya san shi ya san Tambuwal ya mallaki dukkanin wadannan halayen tare da kasancewa cikakken dan siyasa wanda ke da kwarewa da gogewa a sha’anin siyasa da mulki wanda kuma aka shaida da kyakkyawar hulda da al’umma. Don haka a na iya cewa kasawar Buhari ita ce ma ta zama kwarin guiwar Tambuwal ta neman wannan kujerar domin shi ma zai iya da izinin Allah. Ga Allah yake nema wanda shi ke bada mulki ga wanda ya so kuma a lokaci

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Tambuwal Ne yafi cancanta da Shugabancin Nijeriya - inji Hon. Bashire
Tambuwal Ne yafi cancanta da Shugabancin Nijeriya - inji Hon. Bashire
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEh5X8ClkSQ83FbjA5Cr0AKmGl2BygS4RYzzBxHh55h6TA-yprWzs_Z7AuTVxKKqrcNB7xvJJWqKxemMB3tVMj-tbYbFPxh7SkZu4yEHtKncSj0nN9CTN-fZ7-X86cFIVl_iM6sOgtwMHv90/s320/Page-17-Abubakar-Zaki-Bashire.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEh5X8ClkSQ83FbjA5Cr0AKmGl2BygS4RYzzBxHh55h6TA-yprWzs_Z7AuTVxKKqrcNB7xvJJWqKxemMB3tVMj-tbYbFPxh7SkZu4yEHtKncSj0nN9CTN-fZ7-X86cFIVl_iM6sOgtwMHv90/s72-c/Page-17-Abubakar-Zaki-Bashire.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/tambuwal-ne-yafi-cancanta-da.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/tambuwal-ne-yafi-cancanta-da.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy