Blog Archive

Powered by Blogger.

wani Mai Gadi Ya Yi Wa yarinya ‘Yar Shekara 10 Fyade

Babban kotun majistiri da ke garin Minna ta tura wani mai gadi mai suna Michael Itanga dan shekara 55 zuwa gidan kurkuku a bisa zargin ya yi...


Babban kotun majistiri da ke garin Minna ta tura wani mai gadi mai suna Michael Itanga dan shekara 55 zuwa gidan kurkuku a bisa zargin ya yi wa wata yarinya karama ‘yar shekara goma fyade da karfin tsiya. Michael Itang ya kasance a gaban kuliyar ne a sakamakon zargin kamasa da laifin yi wa karamar yarinya fyade sau da yawa. Dan sanda mai shigar da kara, ASP Daniel Ikwoche, ya shaida wa kotun cewar wata mai suna Grace Tanko, da take zama a kusa da babban asibitin garin Suleja ne ta kai musu rahoton aukuwar hakan zuwa caji ofis dinsu da ke `A’ Police Dibision Suleja a ranar 3 ga watan Oktaban nan da muke ciki. ASP Ikwoche ya kara da cewa, mai shigar da korafin ta shaida musu cewar wanda suke zargin mai gadi ne wanda ke gadi a asibitin ‘Christ Rebibal Clinic da ke Suleja, inda take zarginsa da yi wa ‘yarta mai shekaru 10 fyade a cikin dakinsa, ta kuma shaida cewar mai gadin ya maida yarinyarta hawan dalewa, inda ya yi ta mata fyade sau da yawa a cikin dakinsa. Kamar yadda dan sanda ke bayyanawa, ya ce shi ‘wanda suke zargin’ yana baiwa yarinyar naira 20 zuwa naira 100 gabanin ya aikata danyen aikin nasa. Ya ce, wannan laifin ya saba wa doka ta 18 ta jihar Neja da ke kan kare hakkin yara ta ‘Child Rights Law’ na shekarar 2010. A lokacin da aka karanta wa wanda ake zargin laifinsa, ya musanta zargin da ake yi masa. Mai shigar da kara ya nemi kotun ta dage sauraron shari’ar domin su je su kammala gudanar da bincikensu a kan lamarin. Da yake yanke hukuncinsa, Alkalin kotun na majistiri, Nasiru Mu’azu ya aike da wanda ake zargin Itang zuwa gidan jarun domin jiran ranar 25 ga watan Oktoba domin ci gaba da sauraron karar.

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: wani Mai Gadi Ya Yi Wa yarinya ‘Yar Shekara 10 Fyade
wani Mai Gadi Ya Yi Wa yarinya ‘Yar Shekara 10 Fyade
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEh82u-kmd75iazUQtvzc7_ywfOFe-y7kwVnMzK0C8tRljZJJ259wmQNAgmF6jbO9QmRSgG-dTikHows-9wor7-_UOSCfbnyGtB9eisDlp-PyihzkRg8bn6mvxQzIU-W_jNuEt-uma9tK1qv/s320/1515360853661.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEh82u-kmd75iazUQtvzc7_ywfOFe-y7kwVnMzK0C8tRljZJJ259wmQNAgmF6jbO9QmRSgG-dTikHows-9wor7-_UOSCfbnyGtB9eisDlp-PyihzkRg8bn6mvxQzIU-W_jNuEt-uma9tK1qv/s72-c/1515360853661.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/wani-mai-gadi-ya-yi-wa-yarinya-yar.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/10/wani-mai-gadi-ya-yi-wa-yarinya-yar.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy