Blog Archive

Powered by Blogger.

Zan mayar da Najeriya aljannar duniya idan na zama Shugaban kasa- inji tsohon gwamnan jihar Filato

Tsohon Gwamnan Jihar Filato Sanata Jonah Dabid Jang ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar PDP, a ranar ...


Tsohon Gwamnan Jihar Filato Sanata Jonah Dabid Jang ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar PDP, a ranar Talatar da ta gabata, a tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana dalilin da yake son zama Shugaban kasa. Yaya za ka kwatanta yadda kake ji a wannan rana da ka bayyana niyyarka ta fitowa takarar Shugaban kasa? Wannan rana ce mai matukar muhimmanci a gare ni, hakan ne ya sa nake so in kafa tarihi. Don haka a madadin ni kaina da iyalina da mutanen mazabata da mutanen Jihar Filato da kuma yankin Tsakiyar Najeriya da ma Najeriya baki daya nake sanar da niyyata ta fitowa takarar Shugaban kasa don in gyara Najeriya. Me ya ja hankalinka ka fito takarar? Na lura da yadda abubuwa suke tafiya a kasar nan, na kuma bi tarihi tun lokacin mulkin mallaka, sannan na duba yadda siyasa take tafiya da irin gwagwarmayar da magabatanmu suka yi wajen gina dimokuradiyya da neman ’yancin kai. Na ga nasarorin da suka samu da matsalolin da suka fuskanta, a gaskiya sun yi namijin kokari, amma duk da haka akwai abubuwan da suka kamata mu cimma da har yanzu ba mu cimma ba, kuma wadannan abubuwa ina ganin idan an ba ni dama zan iya cimma su. Wadanne abubuwa ne haka? A yanzu Najeriya ta rarrabu, hadin kai ya zama abin tarihi, inda muke fuskantar yaduwar kananan makamai, ’yan bindiga suna cin karensu babu babbaka, har ta kai mutane suna gidaje a kwance amma a rika bin su ana kashe su. Ga matsalar rikicin kabilanci da na addini da fashi da makami da sacewa da garkuwa da mutane don neman kudin fansa, ga talauci, tattalin arziki ya tabarbare da sauran matsaloli, kuma gwamnati ta kasa yin komai a kan haka. A yanzu da ka bayyana niyyarka ta fitowa takara wane abu kake da shi sabo? Na zo da zimmar daidaitawa da kuma saita Najeriya ce, ina so in dawo da Najeriya ta da, Najeriya da magabatanmu suka rayu a ciki, ina da burin gina Najeriya ta zama kasa daya dunkulilliya, ina da yakinin za mu iya gina Najeriya ta zama cikin manyan kasashen 10 a duniya nan ba da dadewa ba. Don haka zan samar da shugabanci nagari, shugabancin da zai saita kasar nan. A ganinka kana da abubuwan da suka kamata a ce mutum yana da shi kafin ya mulki kasar nan? Na yanke shawarar fitowa takarar Shugaban kasa ne bayan na fahimci matsalolin da suka shake kasar nan, na san kasar nan tana bukatar jajirtaccen mutum wajen mulkarta. Don haka ina da dukan abubuwan da ake bukata wajen mutumin da zai shugabanci kasar nan. Ina da kwarewa a kan aikin soja da shugabanci da dimokuradiyya da zartarwa da yin dokoki da kuma sauran batutuwa da suka shafi samar da ci gaban kasa, wadannan dalilai suka sanya na fito wannan takara domin na san zan iya cire wa Najeriya kitse a wuta. Wadanne abubuwa za ka fi mayar da hankali idan ka samu nasara? Idan an zama Shugaban kasa zan fi mayar da hankali kan zaman lafiya da kuma harkar tsaro, zan samar da tsaro a kasar nan, zan kare rayukan ’yan kasar nan. Ba za mu rika korafi a kan abin da ya shafi matsalar tsaro ba, za a hukunta duk wani mai lafi ba tare da tunanin kabilarsa ko wurin da ya fito ba. Zan tabbatar da an daina kashe mutane ba gaira babu dalili, zan tabbatar da an zakulo ’yan bindiga, an kama su an kuma hukunta su don ’yan kasar nan suka rika alfahari da kasarsu. A bangaren tattalin arziki fa? Zan bunkasa tattalin arzikin kasar nan, zan tabbatar Najeriya ta fita daga matsayin da take kai na komai shigo da shi kasar nan ake yi, zuwa kasar da za ta rika fitar da kayayyaki waje, zan samar da tattalin arzikin da zai samar da ayyukan yi ga matasa, tattalin arzikin da za mu daina dogara da kudin da ake samu daga man fetur. Kuma zan karfafa yaki da cin hanci da rashawa, zan karfafa hukumomin da suke yaki da cin hanci da rashawa, zan tabbatar wadannan hukumomin sun rika bin doka, zan ba su damar cin gashin kansu ba tare da katsalanda ba. A mulkina za a yi yaki da cin hanci da rashawa ba tare da nuna son kai, ko wariya ko bita da kulli ba, za a yi yaki da cin hanci da rashawa bisa adalci. Wani tsari kake da shi ga bangaren noma da ilimi da kuma lafiya fa? Nan gaba kadan idan na fara kamfen zan bayyana hanyoyin da zan bi wajen inganta harkar noma da kiwo da ilimi da kiwon lafiya da kimiyya da fasaha da harkar sufuri da kuma manyan ayyukan raya kasa. Don haka idan aka zabe ni Shugaban Najeriya zan mayar da Najeriya aljannar duniya. Batun sake fasalin kasa, ko kana da wani mataki a kan haka? Na san ana ta magana kan sake fasalin kasar nan, don haka zan sake fasalin kasar nan, fasalin da zai sanya ’yan Najeriya cikin farin ciki, kada a manta mun shafe shekara 58 a salon mulki bai-daya, don haka zan samar da hanyar sauya fasalin kasar nan ba tare da bata lokaci ba, idan na zama Shugaban kasa. Wane kira kake da shi ga jam’iyyarku ta PDP game da zaben 2019? A yanzu ai jam’iyyarmu ta amince cewa dan takarar da zai yi mata Shugabancin kasa zai fito daga Arewa ne, kuma yankin da na fito yana tsakiyar Arewa, yanki ne da ke kan hanyar shigowa Arewa daga Kudu, kuma yankin ya yi kokari wajen dorewar Arewa da kasa baki daya. Sai dai abin bakin ciki yankin bai taba samar da Shugaban kasa da aka zabe shi a karkashin mulkin dimokuradiyya ba. A kwanaki na ji ana takaddama cewa a ba yankin Arewa mafi yawan kuri’a takarar Shugabanci kasar nan a karkashin jam’iyyarmu ta PDP, wannan ba ra’ayin jam’iyyarmu ba ne, ra’ayin wadansu tsirarun ’yan takara ne. Kada a manta Arewa ta Tsakiya tana da miliyoyin kuri’a, don haka ya zama dole a ba yankinmu takara a wannan lokaci, mun goya wa wasu yankuna baya, yanzu kuma lokacin da sauran yankuna za su goya mana baya ne. Ba wai muna adawa da sauran yankunan da suka samu damar mulkin kasar nan ba ne, a’a, sai dai saboda zaman lafiya d nuna kowane dan Najeriya dan kasa ne mai ’yanci, don haka yankin Midil Belt ya kamata ya mulki kasar nan a 2019. Don haka ne na gabatar da kaina a matsayin zabin yankin, nake kuma neman goyon bayan mutanen Arewa da Najeriya ba daya. . Copyright @aminiya

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Zan mayar da Najeriya aljannar duniya idan na zama Shugaban kasa- inji tsohon gwamnan jihar Filato
Zan mayar da Najeriya aljannar duniya idan na zama Shugaban kasa- inji tsohon gwamnan jihar Filato
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEi6Z2e568QXyXNdbJ472hCJhbBaqj1jL2ixQ2WFZcjmrW23PODjZHmU7MkLlHrmhf0DyLWPUzHiD_8jw-dK3fSSQpe3bjPsYDSjiSWnjSsktyhthhLVJGTeQI9Va7NUWwbq7Ivbxzp9_jt1/s320/2018_8%2524largeimg30_Aug_2018_230317716.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEi6Z2e568QXyXNdbJ472hCJhbBaqj1jL2ixQ2WFZcjmrW23PODjZHmU7MkLlHrmhf0DyLWPUzHiD_8jw-dK3fSSQpe3bjPsYDSjiSWnjSsktyhthhLVJGTeQI9Va7NUWwbq7Ivbxzp9_jt1/s72-c/2018_8%2524largeimg30_Aug_2018_230317716.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/09/zan-mayar-da-najeriya-aljannar-duniya.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/09/zan-mayar-da-najeriya-aljannar-duniya.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy