Blog Archive

Powered by Blogger.

Nigeria ce Kasa ta 4 a yawan kashe Al'umma

Kasashen Najeriya da Syria da Afghanistan, da Iraqi da kuma Yemen su ne a sahun gaba a jerin kasashen da aka fi samun kashe-kashen al'um...


Kasashen Najeriya da Syria da Afghanistan, da Iraqi da kuma Yemen su ne a sahun gaba a jerin kasashen da aka fi samun kashe-kashen al'umma sanadiyyar rikice-rikice a cikin shekara biyar da suka gabata. Hakan dai na kunshe ne a cikin wani rahoto na cibiyar bincike ta Brookings institute da ke Amurka. Rahoton ya sanya Najeriya a matsayi na hudu, da yawan mutane wadanda aka kashe da suka kai Dubu ashirin da hudu da casa'in da bakwai (20,497). A baya-bayan nan dai Najeriya ta fuskanci karin hare-hare da ake zargin kungiyar Boko Haram da kai wa, da fadan da ake bayyanawa a matsayin na manoma da makiyaya. Barista Audu Bulama Bukarti, malami ne a jami'ar Bayero da ke Kano, kuma manazarci a gidauniyar Tony Blair foundation da ke birnin Landan ya ce rahoton ya na yi wa Majalisar Dinkin Duniya hannun ka mai sanda ne. Kan kasashen da ya kamata su maida hankali a kai dan ceto al'umarsu, maimakon wasu kasashen na daban da suke gudanar da aiki. Bukarti ya kara da cewa, ita kan ta gwamnatin Najeriya babban tashin hankali ne a gare ta a ce cikin shekara biyar an kashe sama da mutane 20,000 a kasar, inda nan ma ya kamata ta zage damtse dan ganin ta bai wa 'yan kasar kariyar da ta dace. Rikicin Boko Haram, da na barayin shanu, na daga cikin matsalolin da Najeriya ke fama da su a dan tsakanin nan wanda kuma ke janyo mutuwar fararen hula da asarar dukiya.

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Nigeria ce Kasa ta 4 a yawan kashe Al'umma
Nigeria ce Kasa ta 4 a yawan kashe Al'umma
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEg5V_ghtoxj_GP4qdVtsXKeucvrdlfTUTBaYNBFJKoHtaqOVoDTCItTmQ45vYqp6i6Y3S8f3y03joXeUjrtvwjDzojkspAb6BSXAE-dDU7tNXmZx_zoMjXXpg8n73oOvz71CO-nlsR2eCO8/s320/Soldiers-33-1.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEg5V_ghtoxj_GP4qdVtsXKeucvrdlfTUTBaYNBFJKoHtaqOVoDTCItTmQ45vYqp6i6Y3S8f3y03joXeUjrtvwjDzojkspAb6BSXAE-dDU7tNXmZx_zoMjXXpg8n73oOvz71CO-nlsR2eCO8/s72-c/Soldiers-33-1.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/09/nigeria-ce-kasa-ta-4-yawan-kashe-al.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/09/nigeria-ce-kasa-ta-4-yawan-kashe-al.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy