Blog Archive

Powered by Blogger.

Har yanzu Mutane Basusan waye Shugaba Buhariba -inji Bashir Abdullahi El-bash

Hakika, duk mai nazari da bibiyar al'amura tare da tsinkayen salon tafikar da mulki na Shugaba Muhammadu Buhari a jiya (cikin kakin soja...


Hakika, duk mai nazari da bibiyar al'amura tare da tsinkayen salon tafikar da mulki na Shugaba Muhammadu Buhari a jiya (cikin kakin soja) da kuma yau (cikin farar tagiya), yake kuma nazartar ra'ayoyin mutane da zarge-zarge ko kushe- kushen 'yan adawa, zai tabbatar da cewa mutane da dama har yau ba su san waye Muhammadu Buhari ba. Kuma babbar matsala kenan da ta sanya wasu daga cikin 'yan 'kasar suke shan wahala da 'bata yawun bakinsu da guna-guni kan musayar kalmomi kan sha'anin gudanar da mulkinsa. Babban abin da mafi yawan 'yan 'kasa suka sani shi ne gaskiya da cancantar Buhari kan shugabanci da jagorancin al'umma, (kowa ya yarda ya kuma gamsu Buhari mai gaskiya ne, mai amana ne, ya cancanci shugabancin Nageria, amma ba su san waye shi ta fuskar salo da tsarin tafikar da mulkin ba. Dalili faruwar hakan shi ne: lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi mulkin Nageria cikin kakin Soja, yana da cikakkiyar damar gudanarwa da zartar da duk abin da yake so a 'kasa 'karkashin ikonsa, ba kuma tare da shakka ko fargabar komai ba, kasancewarsa shugaban 'kasa na mulkin soja kuma mai jini a jika. Kuma hakan ne sababin da ya haifar masa samun nasarori da dama masu tarin yawa. Irin nasarorin da 'yan 'kasa suke fatan gani yanzu cikin mulkinsa na farar hula har ma suke ganin ya za ayi gwamnati irin ta shugaba Muhamnadu Buhari ta zartar da wani al'amari daga bisani kuma ta ce ta soke shi, kamar yadda ya faru a yanzu kan hukumar kula da jigila da zirga-zirgar jiragen sama ta 'kasa, (Nigaerian Airways). Tayadda kuma hakan ya haifar da rudu da rudani cikin 'kasa. To, akan wannan gaba, ya kamata mutanan da ba su san waye Shugaba Muhammadu Buhari ba kan sha'anin tafikar da mulkin farar hula su sani, Shugaba Muhammadu Buhari, mutum ne Dattijo mai kuma juriya da hangen nesa, yana yarda a aiwatar da duk wani al'amari da ya shafi cigaban 'kasa, amma a duk lokacin da ya sake nazari kan wannan abu kuma ya fahimci rushe shi ko tsaida shi, ko sake shi ko dakatar da shi, zai zamto shi ne mafi alkhairi ko yafi dacewa da halin da ake ciki, to, ba ko wata-wata zai sake matsayar da ya 'daukwa a baya. Kuma hakan shi ne cikar kalama da dattako gami da hangen nesa, wato a duk lokacin da Shugaba ya hango wani abu mai cike da alkhairi ko wata masalaha ba ruwansa da zarge- zarge ko maganganun mutane zai aiwatar ne kawai, kuma sannu a hankali duk wanda bai gane ba zai gane. Dan haka, mu fahimci yadda al'amuran suke, shugaba Buhari ya dakatar da ayyukan wancan kamfani, kuma 'kasa da kwanaki biyu da hakan, sai aka ruwaito muhimmin labarin da ke bayyana cewa ministar kudin Nageria, Hajiya Zainab Ahmed tana bayyana cewa, Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a fidda zunzurutun makudan kudade har kimanin naira biliyan (N22.68 billion) domin biyan mutanan da suka yi wa kamfanin jiragen saman aiki hakkokinsu na tsawon shekaru goma sha biyar wanda ba a biya su ba. mu 'kara gane cewa, duk wadancan mutane da aka biya su hakkokinsu, ba 'karamin taimaka musu aka yi ba, domin suna da 'ya'ya da jikoki gami da ahalin da suke 'daukar jigila da 'dawainiyarsu. Sannan a sanadiyyar hakan ba 'karamar damuwa da 'kuncin rayuwa suka shiga ba, amma kwatsam rana guda Shugaba Muhammadu Buhari ya ce a biya su, ai ko shakka babu an taimaka musu, an kuma taimaka bunkasar tattalin arzikin Nageria. Kuma fa ba wai anan kadai Shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya ba, yanzu haka ko tun ma kafin wannan, Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da dama a biya iyalan Sojojin da suka rasa rayukansu a filin daga hakkokinsu, sannan kuma gwamnati tana kula da bukatu da harkar Ilimin 'ya'yansu. Ko shakka babu, wannan babban abin alfahari ne da burgewa ga duk 'dan 'kasa, duba da yadda Shugabansa yake da hangen nesa da kuma duba masalahar al'umma kan sha'anin mulki. Dan haka, ya zama wajibi ga duk 'yan 'kasa su zama masu hangen nesa da fahimtar hakikanin tsarin tafikar da mulki na Shugaba Muhammadu Buhari, domin fahimtar hakan, shi zai taimaka musu wajen saninsa da kuma daina ruduwa da rudun da 'yan Adawa da makiya shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatinsa suke yadawa na 'karerayi da farfaganda domin cimma wata manufa ta Siyasa. -Bashir Abdullahi Elbash Shugaban babbar cibiyar kafar sadarwar zamani ta Shugaba Muhammadu Buhari (BNMC), na Jihar Kano. Talata, 25/9/2018.

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Har yanzu Mutane Basusan waye Shugaba Buhariba -inji Bashir Abdullahi El-bash
Har yanzu Mutane Basusan waye Shugaba Buhariba -inji Bashir Abdullahi El-bash
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEg4rIUZiONdANk2Eg0dRwAes9vC_aVMLCrjjjynLydBpdImCeyFIGcbzDIRm-46x6bWFiKqba9DmRpQMGGWreYILUK2U6Quynpikm8X2WRsuepbDyyPj4WUK0CwjCeSMqTKHwUHZADGjfjf/s320/42290347_1815621428536279_60168626346393600_n.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEg4rIUZiONdANk2Eg0dRwAes9vC_aVMLCrjjjynLydBpdImCeyFIGcbzDIRm-46x6bWFiKqba9DmRpQMGGWreYILUK2U6Quynpikm8X2WRsuepbDyyPj4WUK0CwjCeSMqTKHwUHZADGjfjf/s72-c/42290347_1815621428536279_60168626346393600_n.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/09/har-yanzu-mutane-basusan-waye-shugaba.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/09/har-yanzu-mutane-basusan-waye-shugaba.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy