Blog Archive

Powered by Blogger.

Dalilin da yasa na fita daga PDP- Malam shekarau

Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekaru ya fice daga jam'iyyar PDP. Da asubahin Talatar nan ne Shekarau ya bayyana ficewa daga PDP, a ...


Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekaru ya fice daga jam'iyyar PDP. Da asubahin Talatar nan ne Shekarau ya bayyana ficewa daga PDP, a cewar mai magana da yawunsa Malam Sule Ya'u Sule. Shekarau, wanda yana daya daga masu neman takarar shugabancin Najeriya a jami'iyyar PDP ya ce ya fice ne daga jam'iyyar saboda zargin rashin adalci a bangaren shugabannin jam'iyyar na kasa, wajen rushe shugabancin jam'iyyar na jihar Kano, da yunkurin mikawa Kwankwaso shugabancin. A ranar Litinin ma wasu dubban yan PDP a Kano sun yi wata zanga-zangar nuna adawa da matakin uwar jam'iyyar. Shekarau ya ce gabanin daukar wannan mataki, sai da suka zauna da shugabancin PDP na kasa har sau hudu domin gabatar da korafinsu, da kuma kokari warware matsalar. Har yanzu ba a kai ga bayyana 'yan kwamitin ba, sai dai wasu kafofin yada labaran Najeriya sun ruwaito cewa makusantan Kwankwaso za a nada. A ranar Asabar din da ta gabata ne uwar jam'iyyar PDP ta kasa ta bayar da sanarwar rushe shugabancin jam'iyyar na Kano, sai dai har yanzu ba a ba da dalilan daukar matakin ba. Sanarwar da mai magana da yawun jam'iyyar ya fitar ta ce za a maye gurbin shugabannin da aka rushe da kwamitin rikon kwarya. Har yanzu ba a kai ga bayyana 'yan kwamitin ba, sai dai wasu kafofin watsa labaran Najeriya sun rawaito cewa makusantan Kwankwaso za a nada. Kawo yanzu dai Malam Shekarau bai bayyana jam'iyyar da zai koma ba shi da magoya bayansa. Sai dai wasu bayanai na cewa akwai alama zai koma jam'iyyar APC ne, wacce a baya ya fice bayan shigar Kwankwaso. A shekarar 2015 ne Malam Shekarau ya fice daga APC bayan zargin shugabancin jam'iyyar na lokacin da nuna musu rashin adalci ta hanyar fifita bangaren Kwankwaso a kansu. . Copyright @bbchausa

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Dalilin da yasa na fita daga PDP- Malam shekarau
Dalilin da yasa na fita daga PDP- Malam shekarau
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgZJqYvkJaEcl40FoOvsYuEidqhnufZhldo36HmJ_SD08h9ULu9ndsOSdahyk8uJ3qa8e-rSf9Hzu-bdtjinQKgau7eXlWGBOG8jDfhCxWjaY_NAP2rN7yOMDqdw2Qj1OcflTGWSoDlcKJ2/s320/Ibrahim-Shekarau-.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgZJqYvkJaEcl40FoOvsYuEidqhnufZhldo36HmJ_SD08h9ULu9ndsOSdahyk8uJ3qa8e-rSf9Hzu-bdtjinQKgau7eXlWGBOG8jDfhCxWjaY_NAP2rN7yOMDqdw2Qj1OcflTGWSoDlcKJ2/s72-c/Ibrahim-Shekarau-.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/09/dalilin-da-yasa-na-fita-daga-pdp-malam.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/09/dalilin-da-yasa-na-fita-daga-pdp-malam.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy