Blog Archive

Powered by Blogger.

Yadda Zaki Mallake Zuciyar Mijinki

1. Ki riqa yi masa halin mata, wato irinsu kisisina, shagwaba dss, don namiji baya son mai halin maza ta zama matarsa. 2. Ki zamo mai iya kw...


1. Ki riqa yi masa halin mata, wato irinsu kisisina, shagwaba dss, don namiji baya son mai halin maza ta zama matarsa. 2. Ki zamo mai iya kwalliya. Idan kin kasance mai zaman gida ce to kici ado ko da kuwa baza ki fita ko zuwa ko ina ba. 3. Kada ki fara lissafowa mijinki matsalolinki ko na gida a lokacin da ya shigo, ki barshi ya huta tukuna ya samu nutsuwa. 4. Ki zamo mai kirki, ladabi da biyayya ga Mahaifiyar mijinki kamar yadda zaki so shima ya zamo kamar haka ga mahaifiyarki. 5. Ki dinga qarawa mijinki qarfin gwiwa akan abinda kika ga alamar yana nema ya karaya, hakan zai sa ya gwarzo a cikin maza. 6. Ki dinga fadawa mijinki cewa kina sonshi sau dayawa, dayawa dayawa, Aisha ﺭﺿﺎﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ tace Annabin tsira SAW ya kasance yana tambayarta qarfin soyayyarta gareshi, sai tace mishi kamar ‘zarge’ (wato dauri ko kulli wanta bazai kwance ba), sai ya sake tambayarta ‘yaya zargen yake’? Kuma ya kasance yana cewa da ita Allah ya saka miki da alkhairi Aisha, ina farin ciki da jin dadi dake fiye da yadda kike farin ciki dani! 7. Ki dinga yawan sada zumunci ga mutanen gidansu (kamar ziyartarsu, kiransu a waya dss). 8. Ki dinga bashi wani dan qaramin aiki a gida; kuma idan yayi aikin sai ki gode masa. Hakan zai sa ya qara dagewa. 9. Ki dinga qarfafa masa zuciya wajen yin aikin alheri 10. Idan yana cikin damuwa ki dan bashi lokaci, da yardar Allah sai kiga ya dawo dai dai. 11. Ki dinga yi masa godiya akan sama miki abinci da muhalli da yake yi, abune mai girma! 12. Ki tuna cewa mijinki ma yana da damuwa da farin ciki, saboda haka ki dinga tunawa dashi wajen yanke hukunci. 13. Idan mijinki ya nuna damuwa akan dan qaramin abu da kika yi masa to sai ki bashi haquri kuma ki dena. 14. Kiyi dukkan abubuwan da aka lissafo saboda Allah, sai kiga Allah ya sa miki albarka a cikin duk abinda kike yi. Allah ya kawo mana albarka da yalwar arziqi da ta ‘ya’ya a cikin Rayuwar Aure

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Yadda Zaki Mallake Zuciyar Mijinki
Yadda Zaki Mallake Zuciyar Mijinki
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhbQrLs07bsq62P8naI6I1cbMyKorAF84o0JhYUPYoiYGjpFc53PMuTWiMRhT6vYFtLWVIkSA-roS7dkV2h5L309_VoB_WU2CiLI7taljPxRJqNCc_tMwHQgbyFWiZ46EyPcKyGNs3bjRc9/s320/islamic-marriage.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhbQrLs07bsq62P8naI6I1cbMyKorAF84o0JhYUPYoiYGjpFc53PMuTWiMRhT6vYFtLWVIkSA-roS7dkV2h5L309_VoB_WU2CiLI7taljPxRJqNCc_tMwHQgbyFWiZ46EyPcKyGNs3bjRc9/s72-c/islamic-marriage.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/09/yadda-zaki-mallake-zuciyar-mijinki.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/09/yadda-zaki-mallake-zuciyar-mijinki.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy