Blog Archive

Powered by Blogger.

Shugaba Buhari ya tafi kasar America Domin halartar wani taro

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi birnin New York na Amurka domin halartar taron kwamitin koli na Majalisar DInkin Duniya, MDD, kar...


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi birnin New York na Amurka domin halartar taron kwamitin koli na Majalisar DInkin Duniya, MDD, karo na 72, tare da sauran shugabannin kasashen duniya. Shugaba Buhari ya tashi ne ranar Lahadi da safe. Wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkar yada labarai Femi Adesina ya fitar ranar Juma'a, ta ce babban dalilin halartar taron da shugaban zai yi shi ne gabatar da bayani a kan halin da kasarsa ke ciki. Taken taron muhawarar na bana shi ne: 'Mayar da hankali kan mutane: Kokarin samun zaman lafiya da kuma Rayuwa mai kyau ga kowa da kuma duniya mai cike da nutsuwa.' Shugaba Buhari zai hadu da sauran shugabannin duniya a wajen taron da shugaban MDD Antonio Guterres, zai karbi bakuncinsa. Haka kuma, shugaban zai gana da Shugaba Trump a yayin cin abincin rana, tare da sauran takwarorinsa na sauran kasashen duniya. Daga cikin manyan tarukan da Najeriya za ta halartar a yayin babban taron, har da wanda zai tattauna hanyoyin hana sa mata karuwanci da cin zarafinsu. Zai biya ta London Mr Adesina ya ce Shugaba Buhari zai je London bayan ya kammala taron Majalisar Dinkin Duniya da za a yi a Amurka. Sai dai bai yi karin bayani kan abin da zai sa Shugaba Buhari zuwa London ba. Kuma da BBC ta tuntube shi a kan batun, ya ce shugaban kasar zai ya da zango ne kawai a London, yana mai cewa ba zai ce komai ba bayan hakan. A watan jiya ne shugaban na Najeriya ya koma kasar daga London bayan ya kwashe kwana 103 yana jinyar cutar da ba a bayyana ba.

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Shugaba Buhari ya tafi kasar America Domin halartar wani taro
Shugaba Buhari ya tafi kasar America Domin halartar wani taro
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEiG_KmGzN8i9DlWtDWqPd1UdeXdhlIN8Gbe5lvsY5y7fijAVCEORuKpBuA0v-uHDH9WAAMdIP0AssflI-d8DDMRqtmBzUtpwW4BPS-4G3H1ZFZ633NMDvm0ljzXLHFUqEoRveSRqqRENiDU/s320/42330552_1816051905159898_2937486888610562048_n.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEiG_KmGzN8i9DlWtDWqPd1UdeXdhlIN8Gbe5lvsY5y7fijAVCEORuKpBuA0v-uHDH9WAAMdIP0AssflI-d8DDMRqtmBzUtpwW4BPS-4G3H1ZFZ633NMDvm0ljzXLHFUqEoRveSRqqRENiDU/s72-c/42330552_1816051905159898_2937486888610562048_n.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/09/shugaba-buhari-ya-tafi-kasar-america.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/09/shugaba-buhari-ya-tafi-kasar-america.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy