Blog Archive

Powered by Blogger.

Yaushe Zainab Indomie za ta dawo harkar fim?

Bayan kusan shekara biyar ba a jin duriyarta a harkar fina-finan Kannywood, Zainab Abdullahi ta yanke shawarar komawa bakin sana'arta. Z...


Bayan kusan shekara biyar ba a jin duriyarta a harkar fina-finan Kannywood, Zainab Abdullahi ta yanke shawarar komawa bakin sana'arta. Zainab Indomie, kamar yadda masoyanta da ma'abota fina-finan Hausa suka fi sanin ta, ta yi fice a masana'antar Kannywood a shekarun baya musamman sakamakon irin rawar da ta taka a wasu manyan fina-finai. Daga cikin fina-finan da suka sanya jarumar ta shahara akwai 'Wali-Jam', da 'Ali' da 'Garinmu Da Zafi' da sauransu. Sai dai tana tsakiyar tashe aka daina jin duriyar jarumar, abin da ya kai ga ana diga ayar tambaya da yada jita-jita a kan dalilan daina ganinta a fina- finai. "A lokacin da jarumar ke kan ganiyarta kusan ana iya cewa ta yi wa sauran matan wannan masana'antar fintinkau", a cewar Kabiru Jammaje, wani mai shirya fina-finai a masana'antar Kannywood. Jammaje ya ce akwai daraktoci da masu shirya fina-finan wadanda yanzu haka suka shirya su yi aiki da Indomie saboda hikima da kuma kwarewarta a harkar fina-finai. Mece ce hakikanin abin da ya boye Indomie? Daina fitowar Indomie a fina-finai ya ja hankalin masoyan fina-finan Hausa, har aka rika danganta hakan da wasu bayanai da halayen da ake ganin su suka tilasta mata daina fitowa a fina-finai. Sai dai Zainab Indomie ba ita ce jarumar Kannywood ta farko da ta daina haskawa a fina- finan ba, akwai da dama irinsu Kubura Dhako da Ummi Nuhu da Saima Muhammad da Ummi Zee-zee da dai sauransu. Ko da yake akwai tsoffin jarumai irinsu Safiya Musa da Fati Ladan da Zainab Raga da aure ne ya boye su. A tattaunawarta da BBC Indomie ta karyata dukkanin rade-radin da ake yi a kanta, ta kuma shaida cewa kawai ta yanke shawarar tafiya hutu ne domin dagawa 'yan baya kafa. "A kowanne lokaci ana son wani ya bai wa wani dama don shi ma ya samu lokacin damawa, don in da ina tsaye a kan karagata da ban bai wa 'yan baya dama ba. "Na dawo bakin sana'a ta wadda In Allah Ya yarda idan aka ga na koma to sai dai idan aure ne", inji Indomie Zainab Indomie ta ce a yanzu takamaimai ba za ta iya cewa ga fim din da za a soma ganinta a cikinsa ba, sai dai ana tuntubar ta kuma a cikin wannan watan ma akwai shirin fim da take aiki a kan shi. Labarin dawowarta fina-finai ya ja hankali a shafukan sada zumunta musamman shafin Instagram bayan da fitattun jarumai irinsu Adam A. Zango da Ali Nuhu suka wallafa hotunanta don taya ta murnar dawowa masana'antar. Kabiru Jammaje, wanda ke shirya fina-finan Turanci a Masana'antar Kannywood, ya ce yanzu haka akwai wani shirin fim na Ingilishi da yake shirin haska Jarumar. Akwai soyayya tsakanin Indomie da Zango? An sha yada jita-jitar soyayya a tsakanin Adam A. Zango da Zainab Indomie; ko a wannan lokacin wasu na ganin cewa shi ya taimaka mata sake dawowa bakin sana'arta. Amma Indomie ta ce: "Ni na dauki Adamu ubangida na ne kuma kamar dan uwa na dauke shi kamar yadda ya dauke ni amma babu komai tsakani na da shi. "Zango ya na taimaka min sosai, musamman don ganin na cimma nasara a wannan sana'a". Indomien dai ta ce ba ta da wani buri da ya wuce samun miji na gari ta yi aure. . Copyright @bbchausa

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Yaushe Zainab Indomie za ta dawo harkar fim?
Yaushe Zainab Indomie za ta dawo harkar fim?
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEh8YKkNlrAWMSs7PZtwSTxBGE3eT2MkNwkIPmKjr3e_5jpdan1hs1MGcHjLbR7IgwMaCdjjTStL8Ch2Dmj5gtLTgno0RQFqtVyNvux-xAqOA_-FBP_q-Qih9SIOPdk05JgeubMXnTQrvoD0/s320/vllkyt1ri89orfbkq8.r320x320.c758e403.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEh8YKkNlrAWMSs7PZtwSTxBGE3eT2MkNwkIPmKjr3e_5jpdan1hs1MGcHjLbR7IgwMaCdjjTStL8Ch2Dmj5gtLTgno0RQFqtVyNvux-xAqOA_-FBP_q-Qih9SIOPdk05JgeubMXnTQrvoD0/s72-c/vllkyt1ri89orfbkq8.r320x320.c758e403.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/09/yaushe-zainab-indomie-za-ta-dawo-harkar.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/09/yaushe-zainab-indomie-za-ta-dawo-harkar.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy