Blog Archive

Powered by Blogger.

Hukuncin Iddar Matar Da Ta Auri Mijin Da Ba Ya Iyayin Jima’i Har Suka Rabu

Assalamu Alaikum Malam Wani bawan Allah ne ya Auri kanwata, sai daga baya muka gane ya ha’incemu sakamakon rashin mazantaka da baya da shi, ...


Assalamu Alaikum Malam Wani bawan Allah ne ya Auri kanwata, sai daga baya muka gane ya ha’incemu sakamakon rashin mazantaka da baya da shi, daga baya da asirinsa ya tonu sai ya saketa, shin malam za tayi Idda ne? Don babu wata mu’amalar Aure da ya taba shiga tsakaninsu? Wa’alaikum assalam, Mutukar ba su taba kwanciyar aure ba, ai babu idda akanta, kamar yadda aya ta: 49 a suratul ahzaab take nuni zuwa hakan. Allah ne mafi sani. Ina shirin yin aure, sai tsohon mijina ya ce dama can ya yi min kome, shin yana da hakki a kaina? Malam mijina ya sake ni bayan na kammala idda, saura kwana uku na yi aure sai ya zo ya ce dama ya yi min kome, amma bai sanar da ni ba ne, don Allah malam yana da hakki, ko kuma na kyale shi na yi aurena? saboda gaskiya ina son wancan, amma kuma ba na so na sabawa shari’a? To ‘yar’uwa tabbas miji yana da damar da zai yiwa matarsa kome mutukar tana cikin idda, kamar yadda aya ta: 228, a suratul bakara take nuni zuwa hakan, Amma mutukar bai yi mata kome ba har ta kammala idda to ba shi da dama akan ta, amma zai iya shiga cikin manema. Idan ya yi da’awar cewa ya yi mata kome tun tana idda, amma bai sanar mata ba ne sai bayan ta kammala idda, to ba za’a gaskata shi ba, sai ya kawo shaidu, wadanda za su tabbatar da faruwar hakan. Yana daga cikin ka’idojin sharia toshe duk hanyar da za ta kai zuwa barna, idan aka bar abin a bude, wanda yake kin matarsa, zai iya mata mugunta, ta wannan hanyar, hakan yasa malamai suka ce sai ya kawo shaidu za’a gaskata shi, idan kuma bai kawo ba za ta iya zuwa ta yi auranta. Sai dai wasu malaman suna cewa: idan har matar ta gaskata shi, to ya isa, ko da bai kawo shaidu ba. Duba: Al-mabsud 2\23 da Mawahibul-jalil 5\408. Allah ne mafi sani. Zan iya hulda da mai kudin lukudu? Assalama alaikum. Malam dan Allah. Ina aiki ne akarkashin wani Alhaji Amman a nazargin sa da wai kudinsa bana halal bane wasu suce dan luwadi ne wasu kuma suce kudin lukudu ne, ina so in san ya dace na cigaba da mai aiki ko inbari Allah ya kara lafiya da ilimi da kaifin basira amin. Wa alaikum assalam, Ya wajaba ka tabbatar da hakan kafin ka yanke hukunci. Ba a gina hukunci a musulunci akan shakka ko zato mara rinjaye, saboda wani sashen zaton zunubi ne kamar yadda aya ta (12) a cikin suratul Hujraat ta tabbatar da hakan. Idan wani bangare na kasuwacinsa halal ne wani kuma Haram ne za ka iya hulda da shi, saboda Annabi S.a.w. ya yi mu’amala da yahudawa kuma a cikin dukiyarsu akwai halal akwai kuma haram. Allah ne mafi sani. Idan Saki Ya Fito Daga Baki Ba Ya Komawa! Assalamu alaikum, malam wata baiwar Allah ce suka sami sabani da mijinta sai ya bita inda take aiki yaje yana nemanta sai ta fadama wata agurin taje tacemai batanan sai mijin yace da ‘yar sakon tace ya saketa saki uku kuma itama taji da kunnenta, sai daga baya yace shi be saketa ba, shi ne ta ce a tambaya mata ta saku ko aurensu nanan tunda ba ita ya fada ma ba? Nagode Wa alaikum assalam, Ta saku mana tun da saki ba’a wasa da shi in har ya fito daga baki ko da wasa ne ba ya komawa, tun da ya zartu kamar yadda hadisi ya tabbatar da hakan, musamman kuma wacce aka yiwa sakin ta ji da kunnanta, ai karya ta kare. Inkarinsa ba zai yi amfani ba, tun da an tabbatar ya furta. Don neman karin bayani duba: Zadul-ma’ad 5/204. A mazhabarmu ta Malikiyya ta saku saki uku, amma akwai malaman da suke ganin za’a bar shi a saki daya, tun da saki uku A kalma daya Bidi’a ne, kuma haka ake hukuntawa a zamanin Annabi S.A.W. da zamanin Abubakar RA da wani bangare na zamanin Umar RA, kamar yadda hadisin Ibnu Abbas ya tabbatar da hakan. Allah ne mafi sani. Mene ne hukuncin jinin bari? Assalamu alaikum, malam ina da tambaya, Dan Allah idan mace ta yi barin ciki na wata biyu wannan jinin ya zaka na ciwo ko zata daina azumi sallah? To dan’uwa wannan jini ba zai hana sallah da azumi ba, saboda ba jinin haihuwa ba ne, malamai suna cewa: duk cikin da ya zube kafin halittar mutum ta bayyana, to ba zai hana sallah da azumi ba, halittar mutum tana bayyana ne daga 80-90 daga samuwar ciki, saboda haka duk cikin ya da ya zube kafin haka, to jininsa, ba zai hana sallah ba, ba zai hana azumi ba, amma mutukar an busawa yaro rai ko kuma halittarsa ta fara bayyana, to za’a bar sallah da azumi. Allah ne mafi sani. Mene Ne Hukuncin Fad in ‘Juma’at Mubarak’ Ga ‘Yan’uwa Musulmi? Assalamu Alaikum. Dr. Ko ya halatta Musulmi ya yi wa dan’uwansa murna da zagayowar juma’a ta hanyar sako a wayar sailula kamar a ce ‘Juma’a Kareem’ ko ‘Juma’a Mubarak?’ Allah ya kara sani. Wa’alaikum assalam, Akwai malaman da su ka hana hakan, suna ganin ba shi da asali a addini, Amma abin da yake zahiri hakan ya fi kama da al’ada, wannan yasa haramta shi yake bukatar Nassi, tun da babin al’adu da mu’amaloli a bude yake, sai abin da sharia ta haramta. Duk Wanda yake yi ba tare da ya riya cewa ibada ba ce hana shi ko bidi’antar da aikinsa yana da wuya, kamar yadda Ibnu Uthaimin ya yi nuni zuwa haka a fatawar da aka yi masa. Sai dai duk da haka ya kamata kar Musulmi ya zamar da shi al-adarsa kowace juma’a, don kar wasu su fahimci ibada ne. Allah ne mafi sani.

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Hukuncin Iddar Matar Da Ta Auri Mijin Da Ba Ya Iyayin Jima’i Har Suka Rabu
Hukuncin Iddar Matar Da Ta Auri Mijin Da Ba Ya Iyayin Jima’i Har Suka Rabu
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjvTqig5KcO3zILaEiMXTHmxTFsCUNFJrvSKxL9uSc52hW5TQlk5CWL8t89uTDmEi1QMERqnSEvMnCXpcXHthH8vwdzk1jVmLivvjHjjn810kMdnmHOhLH_iu8oC_gMZLlxGs0jwoWXZ0EB/s320/InstaSave.jpeg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjvTqig5KcO3zILaEiMXTHmxTFsCUNFJrvSKxL9uSc52hW5TQlk5CWL8t89uTDmEi1QMERqnSEvMnCXpcXHthH8vwdzk1jVmLivvjHjjn810kMdnmHOhLH_iu8oC_gMZLlxGs0jwoWXZ0EB/s72-c/InstaSave.jpeg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/09/hukuncin-iddar-matar-da-ta-auri-mijin.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/09/hukuncin-iddar-matar-da-ta-auri-mijin.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy