Wani matashi Nuhu Bulus dan shekaru 17 a duniya da ke zaune a karamar hukumar Toro a cikin garin Bauchi ya kashe mahaifinsa mai suna Bulus A...
Wani matashi Nuhu Bulus dan shekaru 17 a
duniya da ke zaune a karamar hukumar Toro a
cikin garin Bauchi ya kashe mahaifinsa mai suna
Bulus Azi mai shekarun haihuwa 65 a duniya
biyo bayan fizge abun da yake shan tabar wiwi
da shi. Lamarin ya auku ne a yankin Boloji da ke cikin
Toro a ranar 17 ga watan Junairun nan na 2018
inda yaron ya kashe Babansa a bisa wannan
dalilin na ya gan shi na shan sigari. Matashin wadda rundunar ‘yan sandan Jihar
Bauchi ta baje wa manema labaru shi, da sauran
masu laifuka daban-daban a ranar Alhamis din
nan da ta gabata, matashin ya bayyana cewar
babu wani takamaimai laifi wadda mahaifinsa ya
yi ma ssa, ya kuma ce ba su da wata matsala a tsakaninsu amma dai kawai ya kashe shi ba
tare da wani dalili ba. Da yake amsa tambayoyoyin LEADERSHIP A YAU a
lokacin da aka fito mana da masu laifin, matashin
da ya kashe mahaifin nasa ya ce “Ni sunana Nuhu
Bulus shekaru 17 a duniya. Abun da ya faru na
zo nan shi ne a ranan ne dai muka samu matsala
da ni da mahaifina sai na kwada masa Randa (abun anada ruwa) a tsakiyar kansa”. A ta
bakinsa. Ya ci gaba da yi mana bayani da cewa “Gaskiyar
magana har ga Allah ni babu wani takamaimai
abu da zan ce ga shi Babana ya min, abun dai da
ya faru a ranar din ma ni dai kawai na bude idona
ne na ganni a ofishin ‘yan sanda kawai”. A ta
bakinsa. Kana shaye-shaye ne? sai ya amsa da cewa “eh
tabbas ni ina shaye-shaye, ina yawan shan
kwayar Ikzon ne kawai”. Ka ce mana ai kun samu matsala ne da mahifinka
wacce matsace wannan? sai ya amsa da cewa
“Sigari ne ya ke sha sai na fisge daga hanunsa.
Amma ni ba a kan wannan sigarin ne na kashe
shi ba, kawai dai ni na kashe shi ne”, a cewar
Musa Bulus. Ya kuma shaida da bakinsa cewar “Shi baban
nawa na same sa ne yana shan sigari ‘LOFE’,
amma ni babu wani abun da babana ya min”. Matashin yaron dai ya nuna kaduwarsa kan
laifinsa da ya aikata inda ya yi nuni da cewar
hakan na daga cikin sharrin shaye-shaye ne
kawai, ya dai nanata ya kuma sake nanata wa
manema labaru cewar shi fa mahaifinsa bai yi
masa laifin asi ba. Da yake yi mana bayanin yadda suka kama
wannan yaron, Kakakin ‘yan sandan Jihar Bauchi
DSP Kamal Datti Abubakar ya yi mana karin
hasken yadda suka yi nasarar kamo yaron, ya ce,
‘ya’yan marigayin ne suka kawo rahoton
aukuwar lamarin ga ‘yan sanda “A ranar 17/01/2018 wani mai suna Samaila Bulus da dan
uwansa Musa Bulus dukkaninsu mazauna Boloji
a karamar hukumar Toro, Bauchi suka kawo
rahoto wa ofishinmu da ke Toro a kan cewar
wani kaninsu mai suna Nuhu Bulus dan shekaru
17 ya kashe mahaifinsu mai suna Bulus Azi mai shekaru 65 a duniya”. Da yake bayyana yadda yaron ya kashe
mahaifisa ya ce, “Dan ya yi ta kwada wa
mahaifinsa randa (Abun adana ruwa) babu iyaka
wadda har ta kai ya ji masa munanan raunuka
sosai”. Ya ce, baya ga randan da yaron ya yi amfani da
ita, ya kuma kwada wa mahaifinsa katakwaye
babu iyaka. DSP ya ce, nan take an hanzarta da marigayinn
zuwa asibiti domin ceto rayuwarsa biyo bayan
wannan farmakin da dansa ya kai masa amma
hakai bai samu ba domin kuwa rai yayi halin sa,
inda likita ya tabbatar da mutuwarsa a babban
asibiti da ke Toro. DSP Datti ya ce daga cikin abubuwan da suka iya
kamo yaron da su, sun hada da sassan randan da
ya kwakkwada wa mahaifinsa da kuma
kwatakwayen da ya yi amfani da su wajen dukan
mahaifin nasa. Sai ya yi bayanin cewar za su gurfanar da yaron a
gaban kuliya domin fuskantar shari’a daidai da
laifinsa na kisan kai. Rundunar dai ta baje jerin masu laifukan ne da
suka hada da masu garkuwa, ‘yan fashi, ‘yan
damfara ‘yan sara-suka da dai sauransu.
COMMENTS