Wani matashin Magidanci da ke zaune a Karamar Hukumar Ningi a Jihar Bauci, ya ce ya kashe dansa da ya haifa da kansa ne a sakamakon bai da h...
Wani matashin Magidanci da ke zaune a Karamar
Hukumar Ningi a Jihar Bauci, ya ce ya kashe
dansa da ya haifa da kansa ne a sakamakon bai
da halin yi masa hidimar suna da kuma daukan
dawainiyarsa a lokacin bukukuwan suna. Mahaifin mai suna, Habibu Bala, ya ce, rashin
kudin sayen ragon suna ne ya sanya ya yanke
shawarar shayar da dan cikinsa sinadarin ‘Fiya-
Fiya’ domin ya mutu don shi bai da halin daukar
dawainiyarsa a ya yin bikin suna. Matashin wanda ‘Yan Sanda a Bauci suka
gurfanar da shi a gaban ‘Yan Jarida a jiya Alhamis
a shalkwatansu, ya yi bayanin yadda lamarin ya
wakana da bakinsa. Habibu Bala, mai shekarun haihuwa 25 shi ne ya
kashe dansa har lahira a sakamakon ba zai iya
kashe kudin suna ba “Ni suna na Habibu Bala,
shekaru na 25 abin da ya faru shi ne, Allah ya
azurtani da karuwa na haihuwa da namiji, kuma
gaskiya ba na da abubuwan da zan yi masa hidima na suna wannan dalilin ne kawai ya sa na
kasha shi,” in ji Habibu Bala. Matashin ya bayyana cewar, wannan yaron
dansa kenan shi ne kadai ya haifa tun lokacin da
ya yi aure, kuma ba bu abin da yaron ya yi masa
illa dai rashin abubuwan da zai yi masa
bukukuwan zanen suna da kuma radin suna, a
bisa haka ne ya shayar da shi fiya-fiya ya mutu har lahira “Ni ba bu abin da dana ya yi min, kawai
dalilin nan da na fada maku shi ne ba na da
abubuwan da zan yi masa hidimar suna, wannan
dalilin ya sa na kashe shi ta hanyar shayar da shi
fiya-fiya.” Ya ce, shi yana da sana’ar da yake yi na
Leburanci, inda ya ce shi gaskiya bai da wadanda
ma za su taimaka masa da kudin da zai yi sunan
dansa “gaskiya ni ban ga wadanda za su taimaka
min ba, amma ina da ‘yan’uwa a kuma daidai
lokacin ni ban ga wanda zai taimake ni da kayan suna ba. da fiya-fiya na kashe yarona”. Ya kuma kara da cewa, “Na yi matukar damuwa
da na kashe dana na kaina, dan kwanaki biyar a
duniya, na tausaya masa kuma na tausaya wa
kaina”. Matashin dai ya bayyana cewar tabbas ya yi
matukar kaduwa da aikata wannan munnunar
aika-aikar da ya yi wa kansa, yana mai bayanin
cewar ya shiga cikin damuwa fiye da tunanin
dukkanin wani mutum don haka ya bayyana
cewar bai san yadda zai yi ba. Da yake karin bayani ga manema labaru, Kakakin
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauci, DSP Kamal
Datti Abubakar, ya bayyana cewa, dan’uwan
mahaifin jaririn ne ya kawo masu rahoton
aukuwar lamarn, inda su kuma su ka kamo
mahaifin jaririn bisa laifin kisan kai, “A ranar 21 ga watan nan da muke ciki Janairu kenan, 2018
wani Musa Bala wanda Wa ne ga wanda ya yi
kisan ya kawo rahoto a ofishinmu da ke Ningi
cewar kaninsa mai suna Habibu Bala ya yi amfani
da sinadarin fiya-fiya wajen kashe dan cikinsa
mai kwanaki biyar kacal a duniya da haihuwa sakamakon ba zai iya daukan nauyin hidimar
bikin sunansa ba”. in ji Kakakin ‘yan sanda. DSP ya ci gaba da bayani da cewa, “An hanzarta
da jaririn zuwa asibitin Ningi amma rai ya yi
halinsa a wajen likita, inda likitan ya tabbatar da
mutuwar jaririn a sakamakon wannan fiya-fiyar
da Ubansa ya shayar da shi”. DSP Datti ya ce, wanda suke zargi kuma mahaifin
jaririn ya amince da laifinsa da bakinsa don haka
suna nan suna shirye-shiryen gurfanar da shi a
gaban kuliya bisa laifin kisan kai. Baya ga nan kuma DSP ya gurfanar wa manema
labaru wasu jerin masu laifuka daban-daban da
suka yi nasarar kamawa a ‘yan kwanakin nan da
suka aikata laifuka daban-daban, ciki kuwa har
da ‘yan sara-suka, wadanda suka addabi cikin
garin Bauci da ayyukan sara da kuma sukan, “sashinmu na musamman ma su dakile aikace-
aikacen ‘yan garkuwa da mutane, FSARS da kuma
AKU sun yi nasarar kama wasu gaggan ‘yan sara-
suka wadanda muke zargin su da sara-suka a
cikin garin Bauci, wadanna da muka kaman sun
addabi jama’a a bayan gari, Yalwa da kuma Jarmari duk a cikin garin Bauci.” Wadanda suka shiga hannun a bisa laifin sara da
kuma sukan sun hada da, Muhammad Sani mai
shekaru 21, Adamu Inuwa 23, Rabi’u Balarabe
20, Yusuf Danladi. Sauran su ne, Ibrahim Musa, sai
kuma Adamu Hassan, dukkaninsu za a gurfanar
da su a gaban kuliya bisa wannan laifin. Abubuwan da ‘yan sandan suka kamo daga
hanunsu sun hada da adduna masu kaifi guda
10, wuka mai kaifi, kwayoyin Syrup kwalba-
kwalba 12, kwayoyin tiramol sacet-sacet guda
takwas da kuma tabar wiwi wadda ya kai
kilogram biyu.
.
CopyRight: hausaleadership.ng
COMMENTS