Blog Archive

Powered by Blogger.

Fina-finan Hausa su Ke Sanya Ma’aurata Na Kashe Rayuka inji Afakallahu

Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano a karkashin jagorancin Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallahu) ta bayyana cewa, yawaitar finafinan...




Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano a karkashin jagorancin Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallahu) ta bayyana cewa, yawaitar finafinan Hausa na fadace-fadace ne ya janyo matasa da ma’aurata ke kashe rayuka ba-ji-ba-gani a tsakankanin al’umma.
Wannan na kunshe ne a cikin wata wasika, wacce hukumar ta aike wa da furodusan fim din Auren Kaddara, Abdul Amart, mai lamba CB/ADM/497/BOL.I mai kwanan wata 17 ga Janairu, 2018.
Ita dai wannan wasika, wacce wakilinmu ya mallaki kwafi, ta na dauke da sa-hannun daraktan kula da sashen shiryawa da bunkasa finafinai na hukumar, Idris Musa Hausawa, ne a madadin Babban Daraktan hukumar, Alhaji Isma’il Afakallahu.
Hukumar ta aike da takardar ne sakamakon zargin sakin tallan wannan fim mai suna Auren Kaddara a kafafen sadarwa na ‘social media’ gabanin hukumar ta amince da ita ko bayar da izinin yin amfani da tallan
.
Don haka hukumar ta yanke shawarar kin duba tallan bakidaya tare da umartar Furodusa Abdul da ya kawo fim din kacokam, domin dubawa.
A saki na biyu na wasikar, Alhaji Afakallahun ya nanata cewa, “wannan ya zama wajibi ne bisa la’akari da yadda babu kakkautawa a ke shirya finafinan Hausa na fadace-fadace da a ke sarrafa makaman inda matasa da ma’aurata ke kwaikwayo ta yadda hakan ke kai wa ga asarar rayuka.”
Daga nan sai hukumar ta ja kunnen furodusan da ya sanar da dukkan masu ruwa da tsaki cewa, “duk wanda ya daddara ya saka wannan talla ba tare da takardar shaida ba, hukumar ba za ta saurari fim din ba kuma ya zargi kansa.”
.
Copyright: hausaleadership

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Fina-finan Hausa su Ke Sanya Ma’aurata Na Kashe Rayuka inji Afakallahu
Fina-finan Hausa su Ke Sanya Ma’aurata Na Kashe Rayuka inji Afakallahu
http://fm.nextwapblog.com/files/6475/afakallahu.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/01/fina-finan-hausa-su-ke-sanya-maaurata.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/01/fina-finan-hausa-su-ke-sanya-maaurata.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy