Fitaccen jarumin wasan kwaikwayon Hausa na Kannywood Adamu Abdullahi wato Adam A Zango ya bayyana cewa daukakar da ya samu ta janyo masa aik...
Fitaccen jarumin wasan kwaikwayon Hausa na
Kannywood Adamu Abdullahi wato Adam A
Zango ya bayyana cewa daukakar da ya samu ta
janyo masa aikata kura-kurai da dama a can baya. Adam A Zango Jarumin ya bayyana hakan ne a shafinsa na
sadarwar zamani na Instagram, inda ya bayyana
nadamar shi na kura-kuren da yayi a can baya
gami da shan alwashin gyara wa tunda lokaci bai
kure masa ba. “Nayi kura-kurai da yawa a sanadiyyar daukaka.
Sai dai lokaci bai kure min ba. Gyara ya zama dole,
Allah ya bamu sa’a. ” Idan baku manta ba akwai lokacin da jarumin
yayi wani furuci da bai yima jama’a da yawa dadi
ba. Inda yayi habaici gami da caccakar masu
degree wanda hakan har jawo martani mai zafi ta
dalilin da har jarumin yayi yunkurin daina harkar
film gaba daya a wannan lokacin. Mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu bisa
wannan nadama da jarumin yayi inda suka yaba
masa kan fahimtar su da yayi.
COMMENTS