Barkanku da wannan lokaci kamar yanda kuka sani zaku iya video Record na abubuwan da kukeyi a wayar android, misali idan kana wani abun a wa...
Barkanku da wannan lokaci kamar yanda kuka sani zaku iya video Record na abubuwan da kukeyi a wayar android, misali idan kana wani abun a wayarka ta android to zaka iya hada video Record dinsa wanda idan ka gama zaka iya ganin abin dakayi, misali kana wani wasa ko game a wayarka to zaka iyayi kana wasan sannan kuma kana Record na wasan da kakeyi, kokuma kanaso ka koyar da yanda ake wani abun a wayar android to zaka iya hada video Record kana aikata abun kuma kana Record, wato kamar de yanda kuke gani a computer misali idan kason kaga yanda ake wani abun to da zarar kayi search a youtube zakaga suna amfani da video record din gashi sunayin abun kuma suna video, wannan shi ake kira Screen Record, wato wata hanyace da zaka dauko video na abubuwan da kakeyi a wayarka ta Android, shine de na baku misali nace kamar kana wani game ko amfani da wani app to zaka iya Record din abun da kakeyi wanda daga baya zaka iya kallon wannan video dakayi kuma zaka iya turawa wasuma su kallah, sannan kuma zaka iya hada video na bayanin yanda ake magance wata matsalar a android din kokuma yanda akeyin wasu abubuwan idan ka hada saika tura duk wanda keson koya daya kalli videos sai ya gyara matsalar cikin sauki,
domin yin screen record ga yanda zakuyi da farko ku shiga nan ku dauko application mai suna Screen Record
.
Download Screen Recorder.apk
.
Bayan kunyi download dinsa saiku budeshi ku duba daga sama zakuga start kokuma daga tsakiya saiku danna, da zarar kun danna to shikkenan ya fara saiku fito kuyi abubuwan da zakuyi idan kun gama saiku koma cikin app din kuyi stop sannan kuyi save dinsa sai kuyi play kuga abin da kukayi, sannan kafin kuyi zaku iya duba option kudanyi wasu sete seten misali format na video ko size din da kukeso ya kasance da sauransu
.
Allah ya bada sa,a
.
Pls dan Allah kuyi share dinsa domin wasu su amfana
COMMENTS