Blog Archive

Powered by Blogger.

[Android] Yadda ake chanja version na android zuwa kowane irin version darasi na (4) yanda zakuyi Backup na stock/custome Rom na wayarku ta android

Barkanmu da wannan lokaci idan baku mantaba Har yanzu muna cikin darasin mu na yanda ake chanja version na wayar android wato yanda zaka cha...



Barkanmu da wannan lokaci idan baku mantaba Har yanzu muna cikin darasin mu na yanda ake chanja version na wayar android wato yanda zaka chanja Tsarin wayarka ta android misali daga version 4 zuwa 5 ko daga version 5 zuwa 6 kuma da zarar ka chanja to tsarin wayar taka zai chanju ya koma wanda ka chanja, idan kuna biye damu abaya munyi darusa guda uku wato darasi na 1,2,3 kuma idan har kuna biye damu mun tsaya a yanda ake sanya Custome Recovery akan wayar android munyi muku bayaninsa mun fadi muhimmancinsa mun fadi amfaninsa, to idan bazaku mantaba munce muku shine ja gaba wajen chanja tsarin android, sabi da haka ina fatan kun fahinci wancan darasin daya gabata sannan ina fatan kowa ya sanya custome Recovery akan wayarsa ta android, idan kuma baka Riski darasinba to saiku duba shafin namu www.hausaclass.ml bangaren android zone zaku samu sauran darusan, sannan kada ku manta ku tabbatar da kunyiwa wayarku Root tun a darasin farko mun kawo yanda zakuyi Root dan haka saiku duba shafin. Yauwa to yanzu zamu dora da darasi na hudu(4) wato yanda zakuyi backup na stock custome Rom din wayarku,
.
Da farko kafin ka chanja tsarin wayarka ta android wato kafin ka chanja version ana Bukatar dakayi backup na ainihin kwakwalwar wayar taka wato stock/custome rom shi backup shine ajiye ainihin wayar taka wato ajiye ainihin Rom din wayar taka akan memory ka sabi da koda ka samu wata matsala yayin chanja version to cikin sauki zaka dawo da ainihin inda wayarka take ada. Abin da inke nufi anan shine misali kana da waya version 4.4.2 kitkat to kaikuma kanaso ka mayar da ita 5.0 lollipop to kasande idan tana verion 4 dinnan da zarar ka mayar da ita v5 tofa tsarin wannan wayar taka version4 zai tashi ya koma irin na version5 komi da komi zai koma irin na wannan version 5 din to shikuma backup shine zai baka damar dawowa da ainihin yanda wayarka take, wato idan ka gaji da tsarin daka chanja saida dawo da naka na ainihi, sannan yin backup yana da muhimmanci domin asalin wayar taka zakayi backup ka ajiyeta akan memory dinka ta yanda da zarar wani matsala ya tashi saika dawo da kayarka yanda take, ina fatan kun fahinci abin da nake nufi,
.
Yanzu ga yanda akeyi da farko ku tabbata kun dora memory akan wayarku sannan memory ya kasance akwai space kamar 1gb sannan kuma wayar akwai charge a wayarka kamar 70% ko fiye da haka domin gudun matsala idan chaji yayi karanci akwai matsala domin idan kanayi wayar ta dauke akwai matsala, sabo da haka ka tabbata akwai charge,
.
Bayan ka tabbatar da charge akan wayarka, sannan kuma ka tabbata ka sanya custome Recovery akan wayar taka idan bakasan yanda zaka sanyaba to ka duba darasin mu na 1,2,3 yauwa bayan ka tabbatar daka sanya Recovery a wayartaka to yanzu saika kashe wayar taka. Sannan yanzu saika kunna idan ka tashi kunna wayar saika danne Madannin kunna wayar tare da wajen Kara Volume na wayar duk ka dannesu a lokaci daya, wato wajen kunna waya da wajen kara volume su zaka danne. Da zarar ka danne bayan wadansu seconds zata kawo sannan zata kawoka cikin Recovery dinnan daka dora to karka damu yayin data kawo zakaga ta nuno Rubutu kamar haka:
.
--reboot system now
--Install Zip From SDcard
--Wipe data/factory Reset
--Wipe cache Partition
--backup and restore
--Mounts & Storage
--Advance
.
Wannan Rubutun data jero sune Recovery din daka dora to yanzu abin da zakayi saika shiga Inda aka Rubuta ==>backup and restore<== idan zaka shiga wajen saikayi amfani da madannin kasa domin yin kasa idan kazo kan inda zaka shiga saika danna madannin kunnawa wata wayar kuma zaka danna wajen kara volume din da zarar ka danna zai shiga idan ya bude zai kawoka wani waje da Rubutu shima saika shiga inda aka Rubuta ==>Backup<== da zarar kun shiga saiku danna wajen kunna wayar shikkenan daga nan zai farayin Backup na Rom din naku zaiyi shine akan memery ku shiyasa nace ku tabbata kun dora memory sannan memory akwai space domin zai iya kasancewa Rom din wayar taka yana da nawi to bayan wani dan lokaci zai gama idan ya gama zai nuna muku funish to saiku shiga Go to back sannan ku shiga Reboot system now shikkenan wayar taku zata kawo to shikkenan ya gama backup zai ajiye muku da Ainihin rom dinku akan memory dinku zai muku folder mai suna Clockworkmod ko makamancin haka to wannan folder karku kuskura ku chanja mata suna sannan karku gogeta domin idan kuka goge to ku sani kun goge wayarku dole ku barta sabi da idan kun tashi dawo da wayarku dashi ne zaku dawo da ita yanda take kokuma idan ansami matsala wajen chanja version din to da wannan zaku dawo da ita idan kuma kuka Riga kuka goge to zan iya ce muku sory domin saide ku kaicha a sa mata file. Wannan itace hanyar da zakuyi backup na stock custome rom dinku ina fatan kun fahinci yanda abin yake . Yanzu kuma sai yanda zaku dawo da Rom din naku wato idan kunyi backup kun ajiye akan memory dinku to yanzu saura yanda zaku dawo da ainihin wayar taku wato Restoring, domin yin Restore na Rom din da kukayi backup wato wanda kuka ajiye akan memory to idan zaku dawo dashi ga yanda zakuyi kubi mataki na farko wato ku sanya wayar taku a Recovery wato ku danne madannin kunna wayar da kuma wajen kara volume da zarar kun danne zai kawo muku Rubutu kamar yanda na fada afarko wato kamar haka: --reboot system now --Install Zip From SDcard --Wipe data/factory Reset --Wipe cache Partition --backup and restore --Mounts & Storage --Advance . To saiku sake shiga ==>Backup & Restore<== da zarar kun shiga zakuga inda aka Rubuta ==>Restore<== saiku shiga da zarar kun shiga zai farayi muku Restoring na ainihin Rom din naku bayan wadansu mintuna zai gama da zarar ya gama zai nunama funish shikkenan ka gama saika dawo ka shiga Reboot system shikkenan ka gama zakaga tsarin ka ya dawo yanda yake, ina fatan kun gane wannan darasin,
.
Idan baku ganeba zaku iya kiranmu a 0816982309
.
Insha Allah darasin gaba shine na yanda zaka dora kowane irin version din tunda yanzu mun kawo muku matakan yanda akeyin komi kafin aje ga chanja version din, kuma insha Allah inde kukabi a nutse kowa zai iya chanjawa tasa wayar, idan baka riski darusan farkoba to ka duna shafin namu www.hausaclass.ml domin karanta sauran darusan.
.
Allah ya bada sa,a
.
Pls here to facebook/whatsapp

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: [Android] Yadda ake chanja version na android zuwa kowane irin version darasi na (4) yanda zakuyi Backup na stock/custome Rom na wayarku ta android
[Android] Yadda ake chanja version na android zuwa kowane irin version darasi na (4) yanda zakuyi Backup na stock/custome Rom na wayarku ta android
http://fm.nextwapblog.com/files/6475/flash-custom-rom-onto-your-samsung-galaxy-note-2-and-enhance-your-android-experience-w1456.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/01/android-yadda-ake-chanja-version-na.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/01/android-yadda-ake-chanja-version-na.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy