Jama,a Assalamu Alaikum barkanmu da wannan lokaci, kamar de yanda muka saba kawo muku sabbin abubuwa na harkar kimiya da fasaha da sauran ga...
Jama,a Assalamu Alaikum barkanmu da wannan lokaci, kamar de yanda muka saba kawo muku sabbin abubuwa na harkar kimiya da fasaha da sauran garabasa kala kala to yauma ga HausaTricks tafe da wata sabuwar gara6asa na samun data mai yawa akan farashi mai sauki, itace wannan gara6asar kamar yanda muka fada a farko zaka samu 20gb a N100 ko 4gb a N200 kokuma 10gb a N500. Ita wannan garabasa wani sabuwar barauniyar hanyace da muka gano muku da ita domin samun sauki wajen sayan data, to abinde babu wata wuya sosai idan har kabi yanda zamu koyar to insha Allah zaka more wannan gara6asa,
.
To da farko abin da zakuyi shine port wato kafin ka mori wannan gara6asa dole sai kayi porting na layinka, abin da ake nufi da port a bangaren sim shine kamar chanja wani layi zuwa wani layin misali daga mtn zuwa Airtel to wannan shine port sabo da haka kafin ka samu wannan gara6asa sai kayi porting na sim dinka, yanda zakayi shine:
.
Ka samu layin MTN tsoho ko sabo ka tabbata da kaine kayimar Register, idan kuma bakaine kayiba to zaka iya samun wani mtn din sai kaje ayima Register da details dinka, abin dayasa nace dole sai kaine kayi Reg din sabi da yayin da kaje yin port zasu bukaci sunayen da akayi reg din dashi da sauran abubuwa wanda zai bada shedar kaine mai sim din, yauwa bayan ka nemi Sim kayi masa Register to yanzu sai katafi Offishin Airtel mafi kusa dakai da zarar kaje saika sanar dasu kan cewa kanaso ayima Port na MTN zuwa Airtel, da zarar ka fada musu haka shikkenan sukuma zasu baka Form ka cike idan ka gama cikewa, zasu karbi suyima sannan Aitel zasu turoma sako a layin Mtn bayan sakon ya shigo to yanzu saika kashe wayar taka ka sanya Layin da Airtel suka baka wanda akayi port din bayan kasa saika dan jira nadan wani lokaci zaka samu sako na tabbacin kayi nasara shikkenan saura yanda zaka samu data/mb din
.
Domin Samun 2gb a N100 ko 4gb a N200 ko 10gb a N500 kawai kayi Recharge na Layin Airtel din naka Amma ta hanyar Amfani da Bank Account wato dole saita accont zakayi Recharge din naka idan kayi Recharge na N100 zaka samu 2gb idan kayi na N200 shikuma 4gb haka zalika na N500 10gb, duk lokacin da kayi Recharge inde ta bank ne to zaka more wannan gara6asa, ammafa ku sani karkuyi Recharge ta hanyar sanya kati domin idan kayi tanan bazaka samu wannan gara6asaba, ta bank accout kadai zaka more wannan gara6asa, to da zarar kayi Recharge ta bank din zaka samu sakon samun kyautar domin duba data sai a danna *223# kuma data zaiyi expire 30days wato wata daya, sannan kuma data yana aiki a kowane waya da computer.
.
Allah ya bada sa,a
.
Kuci gaba da kasancewa da hausatricks a kowane lokaci domin more gara6asa kala kala
COMMENTS