Hukumomi a Kenya sun tuhumi wani mutum bisa zargin yin jima'i da wasu akuyoyi biyu na makwabcinsa. An zargi mutumin, mai shekara 35, da ...
Hukumomi a Kenya sun tuhumi wani mutum
bisa zargin yin jima'i da wasu akuyoyi biyu na
makwabcinsa. An zargi mutumin, mai shekara 35, da laifin
kisan akuyoyin bayan ya gama jima'in da su. Masu shigar da kara sun gabatar da mushen
akuyoyin a gaban kotun Kangundo da ke
gabashin birnin Nairobi a matsayin shaida,abin
da ya girgiza mutanen da ke cikin kotun. shaida wa kotun cewa 'yan sandan da suka
kama shi sun lakada masa duka sannan suka
azabtar da shi. Alkalin kotun ya ba da umarni a kai mutumin
asibit domin a binciki lafiyarsa saboda zargin
dukan da ya ce an yi masa sannan ya ba da
belinsa a kan $1,000ko kuma ya samu mai
tsaya masa a madadin hakan. Za a ci gaba da sauraren karar ranar 29 ga
watan Janairun 2018. Dokokin kasar Kenya sun bukaci a daure
mutum tsawon shekarar 14 idan ya aikata irin
wannan laifi. Ba wannan ne karon farko da aka samu mai
aikata irin wannan laifi ba. A watan Maris din da ya gabata, an daure wani
mutum tsawon shekara 15 bayan an same shi
da laifin yin jima'i da kaza a yammacin kasar,
inda ya ce yana matukar tsoron yin mu'amala
da mata. Category: Kannywood A+ A - Print Email × Referensi Geografis Aure bikin Ba Ba da da Hotels in Mina Jebel Ali
COMMENTS